39

443 40 8
                                    

🎗⚾⚾🎗⚾⚾🎗⚾⚾🎗

*RAYUWAN NAJWA*

🎗⚾⚾🎗⚾⚾🎗⚾⚾🎗️

*WRITTEN*

*BY*

*AYSHA ISA (Mummy's friend)*

*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*

_____________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*LITTAFAN MARUBUCIYA*

_*1. Na Tsani Maza*_

_*2. Meke Faruwa (labarin Amira)*_

_*3. Ruhin 'Dana*_

_*4. Illar Rik'o ( 'yar rik'o)*_

_*5. Shi nake so ( labarin Fusailah)*_

_*6. Bani da laifi ( bayin kaina bane)*_

*DEDICATED TO:*

_*Zaman Amana Asso.*_

*ALL MOST TRUE LIFE*

*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM*

*Page 39*

Lawyern Isma'il ne ya kirashi ya sanar dashi halin da ake ciki tare da shaida mashi cewa ya janye daga tsaya mashi a kotu. Ba ƙaramin girgiza Isma'il maganar ta yi ba jin wai har kotun ta raba auren, bai taɓa tsammanin Najwa zata iya aikata abinda ta yi ba.

Bayan kwana biyu da faruwan haka, Najwa ta je har gidan da mota suka ɗebo kayanta, a nan Ummin shi ke sanin abinda ya faru, tsabar takaici saida ta zubda hawaye, lallai Isma'il yayi asarar mace tagari wacce samun irinta a wannan zamanin sai an tona, haƙuri sosai Ummi ta bata.

"Lah! Wallahi Ummi babu komai, ni babu abinda kika min" Najwa ta ce ta rungume Ummi.

Haka suka rabu Ummi bata so hakan ba. Su Hajiya Inna da Mama sai tsegumi suke wai ta ƙi zaman aure, tun suna yi abin na damun Najwa har yazo ya daina damunta.

Haka ma unguwa ake ta faɗin ta ƙi zaman aure.

_______________________________________________________________________

Najwa ce zaune tana arranging credentials ɗin ta cikin files, yayin da Ummita ke daga gefenta tana ta razgan kuka zata bi Nusaiba wacce ta tafi islamiyya.

Ummi ce ta shigo ɗakin ta ɗauke ta ta fara lallashinta ta ce " yanzu kina zaune take ta wannan kukan haka?"

"Ummi ni bansan abinda zan yi mata bane, na fa lallasheta har biscuit na bata ta ƙi amsa."

"Sai ki ɗauke ta, ba gashi yanzu ta yi shiru ba. Kudai 'ya'yan zamani baku da haƙuri da 'ya'yanku, ko irin goyon nan baki san yiwa yarinyar nan " Ummi ta ce ta saɓa Ummita a baya, sannan ta fice daga ɗakin.

Binsu ta yi da ido har suka fice daga ɗakin sannan ta juyo ta ci gaba da abinda take.

Tana cikin gyaran ta ji kamar sallamar Rumaisa, leƙowa ta yi dan gasgata zargin ta, a risine ta sameta tana gaida Ummi wacce sallamar Rumaisar ne ya fito da ita daga ɗakin, amsa mata Ummi tayi cikin sakin fuska.

Najwa ce ta ƙaraso falon fuska ɗauke da murmushi ta ce " lah! Ashe ke ce."

"Eh nice, yaushe a gari?" Rumaisa ta ƙarasa zance cike da mamaki, sannan ta miƙe.

RAYUWAN NAJWAWhere stories live. Discover now