29

361 32 2
                                    

🎗⚾⚾🎗⚾⚾🎗⚾⚾🎗

*RAYUWAN NAJWA*

🎗⚾⚾🎗⚾⚾🎗⚾⚾🎗️

*WRITTEN*

*BY*

*AYSHA ISA (Mummy's friend)*

*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*

_____________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*LITTAFAN MARUBUCIYA*

_*1. Na Tsani Maza*_

_*2. Meke Faruwa (labarin Amira)*_

_*3. Ruhin 'Dana*_

_*4. Illar Rik'o ( 'yar rik'o)*_

_*5. Shi nake so ( labarin Fusailah)*_

_*6. Bani da laifi ( bayin kaina bane)*_

*DEDICATED TO:*

_*Zaman Amana Asso.*_

*ALL MOST TRUE LIFE*

*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM*

_*"Life is like a book. Some chapters are sad, some are happy, and some are exciting, but if you never turn the page, you will never know what thenext chapter has in store for you."*_

*Page 29*

Murmushin yak'e Ummi tayi ta ce " nima bansani ba, dan likita bai min bayani ko ba."

Ajiyar zuciya Abba yayi sannan ya ce " ko dalilin da ya ke nema na kenan?"

"Ina ji..." Ummi ta fad'a a takaice.

Mik'ewa Abba yayi wannan ya yi daidai da dawowar Najwa daga bayi, " muje ko " ya ce bayan Najwa ta k'araso inda suke, mik'ewa Ummi tayi suka fice daga d'akin. A tare suka nufi Office d'in Dr. Harun su hud'u har da Mujaheed. Knocking suka yi, sannan suka bud'e k'ofan bayan Dr. ya basu izinin shigowa. Zaune suka sameshi ya duba folders d'in patient, "bismillah" ya ce yana masu nuni da kujera, Abba da Ummi ne suka zauna a kujeran dake facing d'inshi, yayin da su kuma Najwa suka zauna daga bayansu. Gaisawa suka yi sannan Dr. Harun ya fara magana, ya ce" da fari dai zan so ku d'auki komai a matsayin k'addara duk da dai har da sakaci a cikin wannan lamarin, amma idan har ba hakan yake a rubuce ba babu abinda zai faru. Ina fatan kuna zaku k'arb'a wannan k'addarar hannun biyu ba tare da nuna butulcewar ba?"

"InSha Allahu " Abba ya ce.

"Masha Allah. Kuna same da sabon laluran da ya kusanto 'yarku?"

Girgiza kai Abba ya yi. Dr. Harun ne ya ci gaba da magana ya ce " bakomai bane illa yoyon fitsari, wanda aka fi sani a turanci da V.V.F ( Vessico Vaginal Fistula )...."

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un...Yoyon fitsari" su Abba suka fad'a a tare.

Gyad'a masu kai ya yi alamar eh, " calm down. Insha Allah komai zai zo da sauk'i" ya ce yana mai kwantar masu da hankali.

"Wai meke kawo wannan cutar ne? " Muhajeed ya tambayeta.

"Babban abinda yakan haifar da wannan cutar ta yoyon fitsari sune; _*doguwar nakuda, yima mata kaciya, ko k'ari ko yankan gishiri da wanzamai suke yi. Doguwar nakuda takan aku sanadin abu biyu; imma dai kugu uwar matsattse ne, ko kuma kan jaririn kato ne. Idan kugun uwa matsattse ne ko d'an k'arami kuma kan jariri dai yake, to kugun zai rik'e kan jariri ya k'asa fitowa. Haka ma idan kugun uwar daidai yake ( wadatacce ne) amma kan jariri k'ato ne, to kan zai mak'ale ya k'asa wucewa. Idan d'aya daga cikin wa'innan ya faru, maimaikon mace ta yi nakuda cikin 'yan awoyi, sai a wuni a kwana ana yi, wato nakuda ta zama doguwa kenan. To wannan kan sa kan jariri ya rik'a gogan fatar da ta raba matsara da wurin haihuwa ta koke, fitsari ya fara yoyo, kuma a mafi yawan lokutan akan rasa jariri saboda wannan matsin. Ana iya kare aukuwar haka tun daga fara zuwa awon ciki inda za'a iya gane girman jariri har zuwa haihuwa a asibiti.*_" shiru Dr. Harun ya yi na d'an lokaci sannan ya ci gaba " wannan d'aya kenan daga cikin dalilin dake haifar da yoyon fitsari. Dalili na biyu shi ne _*ta yiwa mata kaciya ko yankan gishiri da wasu wanzamai ke yi, inda cikin kuskure aka tab'a mafitsara da aska har ta huje, fitsari ya fara yoyo. Ana iya kare aukuwan haka aukuwan haka idan aka daina yankan gishiri kwata-kwata" nisawa Dr. ya yi sannan ya ci gaba " mace na iya kamuwa da cutar yoyon fitsari da hanyar _*k'arin da ake yiwa mace yayin haihuwa, idan mace bata son haihuwa a asibiti yana da kyau kwararriyar ungozoma wanda aka ba horo na zamani, wacce ya ta san lokacin da nakuda ya kamata ta k'are, ta kuma san lokacin da dole a rankaya asibiti don tiyata a cire jariri kafin ya mutu ko yoyon fitsari ya auku. Har ila yau kamata wannan ungozoman ta san daidai idan akewa mata k'ari ta yadda ba zata yanka mafitsara ba. Shekaru da kuma ciwon daji na mafitsara kan haifar da cutar yoyon fitsari wasu lokutan. Wannan shine takaitaccen bayani akan wannan cutar ta yoyon fitsari.*_"

RAYUWAN NAJWAWhere stories live. Discover now