36

409 37 2
                                    

🎗⚾⚾🎗⚾⚾🎗⚾⚾🎗

*RAYUWAN NAJWA*

🎗⚾⚾🎗⚾⚾🎗⚾⚾🎗️

*WRITTEN*

*BY*

*AYSHA ISA (Mummy's friend)*

*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*

_____________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

*LITTAFAN MARUBUCIYA*

_*1. Na Tsani Maza*_

_*2. Meke Faruwa (labarin Amira)*_

_*3. Ruhin 'Dana*_

_*4. Illar Rik'o ( 'yar rik'o)*_

_*5. Shi nake so ( labarin Fusailah)*_

_*6. Bani da laifi ( bayin kaina bane)*_

*DEDICATED TO:*

_*Zaman Amana Asso.*_

*ALL MOST TRUE LIFE*

*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM*

*Page 36*

Murmushi Najwa ta yi ba tare da ta ce mata komai ba ta ci gaba da wasa da Mujaheed.

"Ukhtee magana fa nake amma baki ce dani komai ba."

"Toh me kike so nace maki? Eh bani da lafiya, ko me?. Wai ma in tambaye ki wani irin rashin lafiya kike nufi?" Najwa ta jero mata tambayoyi.

"Yanzu kina son ki cemin baki abinda nake nufi ba ko me?" Rumaisa ta ce.

Murmushi Najwa tayi ta ce " eh."

"Ok barin na maki bayanin yadda zaki fahimta, ina nufin yanzu ke baki kin komai irin..." ta kashe mata ido sannan ta ƙarasa da faɗin " kin gane ai."

"Nifa har yanzu ban gane ba" Najwa ta ce tana danna dariyan dake nema ya ci ƙarfinta.

"Bana son iskanci fa, wallahi nasan ki gane abinda nake nufi, don haka ki amsa min tambayata kawai" Rumaisa ta ce a hasale.

"Maida wuƙar mallama, ba mamaki bani da lafiyan ne kinsan fa nayi jinya" Najwa ta ce cikin muryan tausayi.

"Subhanallah! Yanzu kina nufin bakin inji komai kenan? Allah sarki Ukhtee kinga rayuwa" Rumaisa ta ce cikin murya tausayi kamar zata yi kuka.

Dariya Najwa ta fashe dashi "mallama kar ki min kuka, babu abinda ya sameni auren ne dai baya gabana yanzu, wallahi naji duk ya fice min a rai, ni fa ji nake yanzu _*na tsani maza*_"

"Aikuwa wallahi baki isa ba, har nawa kike da zaki ce auren ya fice daga kan ki, kuma ki fara istigrafi da wannan kalman da kika faɗa, daga mutum ɗaya ya maka laifi shine aka taru aka zama ɗaya?. Toh ni ba gashi a bayan ki na yi aure ba, kinga shi wannan ya min haka ne? Ko haka kika ga iyayenmu maza sun yiwa matayensu?"

Sallamar Nusaiba da taji ne yasa tayi shiru, shigowa ɗakin Nusaiba tayi ɗauke da tray ɗin abinci da drink, sai da ta ƙaraso gabanta ta gaisheta sannan ta ajiye, karɓar Mujaheed dake hannun Najwa ta yi suka fice daga ɗakin.

Kallo Rumaisa ta bi ta dashi tana mamakin saurin girma irin na Nusaiba, ta zama cikakkiyar budurwa dudu yanzu haka wuce 13 zuwa huɗu ba, "haka Nusaiba ta zama, Masha Allah. Toh kin ga idan kina wa Allah ki fidda miji kiba wannan yarinyar wuri taci ƴan matancinta, ehee."

RAYUWAN NAJWAWhere stories live. Discover now