19

431 39 0
                                    

🎗⚾⚾🎗⚾⚾🎗⚾⚾🎗

*RAYUWAN NAJWA*

🎗⚾⚾🎗⚾⚾🎗⚾⚾🎗️

*WRITTEN*

*BY*

*AYSHA ISA (Mummy's friend)*

*Vote me on wattpad @ AyshaIsah*

*LITTAFAN MARUBUCIYA*

_*1. Na Tsani Maza*_

_*2. Meke Faruwa (labarin Amira)*_

_*3. Ruhin 'Dana*_

_*4. Illar Rik'o ( 'yar rik'o)*_

_*5. Shi nake so ( labarin Fusailah)*_

_*6. Bani da laifi ( bayin kaina bane)*_

*DEDICATED TO:*

_*Zaman Amana Asso.*_

*ALL MOST TRUE LIFE*

_*"Soft nature of a person doesn't mean weakness, Remember : Nothing is softer than water, but its force can break the strongest of rock."*_

*Page 19*

Da asuban fari Usman ya tashi, tada Najwa yayi ba tare ya jira tashinta ba yayi ficewansa daga d'akin, ruwa ya zuba a buta sannan ya fad'a bayi ya tsarkake jinsa. Alwala d'ora ya bayan ya fito daga bayin sannan ya nufi d'akinsa ya gabatar da sallan raka'atanir fijr. D'akin Najwa koma bayan ya iddar da sallan don ganin har yanzu bata fito.

Kwance ya sameta kamar yanda ya barta idanuwanta lumshe tana barci, tashinta ya kuma yi a karona biyu. Da kyar ta bud'e idanuwan wanda suka mata nauyi, da sauri ta maida rufe ganin zaune yana sakar mata murmushi.

Dariya mara sauti yayi yace " 'yan mata a d'aure a tashi ayi sallah. Najwa nagode da wannan kyautan da kika min, Allah ya faranta maki rai kamar yanda nima kika ranta min. Ina kuma rok'on afuwa gareki, ki yafe min don nasan na kasance mai laifi a gareki na aurenki ba tare da amincewar ki ba, Najwa *bani da laifi* duk wannan ya faru ne *a sanadin k'aunar* da nake maki. Najwa ina maki son da bansan ko wace iri bace..." Tada sallah yaji an fara yi ne yayi ya k'atse mata zancesa, mik'ewa yace " dan ki d'aure ki tashi kiyi sallah..." Sannan ya fice da sauri don samun sallah. Sai da ya biya d'akin ta d'akin ya kwansa masu k'ofa sannan ya tafi.

A daddafe Najwa tashi, tana cije lab'e duk da dai bata ji irin zafin da ake fad'i ba, haka dai ta lalab'e taje ta tsaffetace jikin sannan tazo ta d'ora alwala, d'akin ta dawo ta gabatar da sallah. Duk da tana me takaicin faruwan haka amma taji zuciyarta wasai kamar an sauk'e mata wani nauyin da ya rataya a kanta. Tana iddarwa nan tayi kwanciyarta nan da nan barcin yayi awon gaba da ita.

Aunty Aisha ce ta shigo d'akin tare dasu Sadiq jin yau Najwa shiru, kwance suka sameta tana barci. Nasir yaje ya zauna kusa da ita yace "aunty ina kwana"

Cikin barci taji kamar ana magana bud'e ido tayi ta zubasu kan Nasir dake zaune kusa da ita maida ido tayi zata koma barci, taji murya aunty Aisha " k'anwata da fatan kina lafiya dai ko? Naji ki shiru."

Mik'ewa tayi zaune tace cikin muryar barci tana murza ido " wallahi yau ji nayi duk jina nake wani irin..."

"Ayyah! Sannu k'anwata ai jiki da jini watarana sai da haka. Kodai muyi anko ne?" Auntyna Aisha ta k'arasa zance tana murmushi.

"Anko kuma?" Najwa tace tana nema karin bayani.

"Eh mana, Allah yasa kema juna biyun gareki muyi haihuwan mu tare..."

Zaro ido Najwa tayi tace " kai auntyna ni wallahi da komai. Allah dai ya saukeki lafiya."

"Ameen k'anwata. Kema Allah yasa muji labari mai me dad'i cikin wannan kwanakin" cewan Aisha.

RAYUWAN NAJWAWhere stories live. Discover now