12

2.6K 142 1
                                    

*B*ilkisu na zuwa unguwarsu taga baki d'aya yanayin unguwar ya canza daga yadda tasanta,a k'ofar wani had'add'an gida mai matukar kyau jikin shi duk tiles nan taga driver d'in ya tsaya tare da fitowa da sauri ya b'ud'e mata murfin kofar yana cewa,

"Rankishi dad'e gamu munxo Allah ya k'ara miki lafiya."

Jinta tayi wani gingirin ganin yadda yake tayi mata sannan yana nuna mata gidan a matsayin wanda zata shiga,sake kallon driven tayi sannan cikin tsoro tace,

"Dan Allah malam ina ne nan ka kawo ni?!"

"Ranshi shi dad'e ai cewa akayi na kawoki gidan mahaifanki toh kuma gashi munzo Allah ya temakeki."

Ya fad'a cikin gazgata mata abinda ya fad'a,sake kallon gidan tayi sannan ta girgiza kai alamar bata yadda ba ganin tak'i fitowa yasan kuma ba haka takeyi ba yasa shi k'arasawa cikin zauran gidan ya kwad'a sallama,Ummi ce kanwarta ta fito dan ganin wanene tana ganinshi da kayan sarauta ta durkusa har k'asa tana gaidashi ya amsa tare da cewa.

"Yauwa 'yan mata kinga ga yayarki bilkisu tak'i fitowa daga cikin mota ko zaki je idan ta ganki k'ila ta fito?!"

Ai da sauri Ummi tayi waje murfin motar a bud'e yake nan billy ta ganta tayi saurin fitowa da sauri suka rungumi juna cikin murna kafin Ummi taja hannunta suka shiga babu wanda yayi magana a cikin su dan tsabar murna sai da suka shiga cikin gidan.

"Umma ki fito ga Yaya Bilki tazo."

Cewar Ummi cikin d'aga murya suka k'arasa cikin parlor suka zauna yayin da bilkisu keta faman kallon yanayin gidan tana mamakin yadda rana d'aya Allah kan sauya al'amura bata gama mamaki ba Umman su ta shigo parlon tana murmushi tace,

"Ke dai bilkisu bakya son zama duka-duka yaufa kwanaki uku kenan da kuka zo gidan nan amma yauma har kin kuma fitowa."

Sakkowa billy tayi daga kan kujera ta fad'a jikin Ummanta tana kuka nan da nan hankalinta ya tashi ta kalli inda Ummi take tace,

"Tashi kije ki d'akko mata ruwa da abinci."

Ummi ta tashi jiki a sanyaye yayinda billy ta maida hankalinta wajan mahaifiyarta cikin kuka take cewa,

"Umma ya cuceni ya b'atamin rayuwar da kuka dad'e kuna kula min da ita wallahi Umma ba laifina bane saceni yayi ya tafi dani masarautarsu ya aikata zina dani Umma ya b'ata rayuwata dama ace na mutu kar naga rayuwata ta gaba dan nasan sai tafi haka muni da wulakanta...!l

Sai faman surutai takeyi daga gani hankalinta ne ya dawo dan haka Umma ta barta sai da tayi kukan sosai har ya haddasa mata da ciwon kai sannan Umma tace,

"Kiyi shiru Bilkisu kiyiwa Allah godiya daya dawo miki da tunaninki bayan kin kwashi tsawon shekaru sannan kiyi min bayanin shin waye kike maganar yayi miki duk wad'annan abubuwan...?!"

"Umma waye kuka bashi aurena?!"

Tayi maganar hawaye na sake zubowa Umma ta rungumeta cikin sanyi jiki da tunani kala-kala tace mata.

SON RAI KO ZABIN IYAYE?!(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now