10

3.4K 151 1
                                    

*D*a sallama Modu yashiga babban parlorn sarki Aliyu Hydar,xaune ya iske sarki Aliyu Hydar kansa asama da alama tunani yake d'an gyaran murya Modu yai se a sannan sarki Aliyu Hydar yadawo daga duniyar tunanin da yake nannauyar ajiyar zuciya yasauke ahankali ya amsa sallamar Modu tareda gyara xaman kishingid'ewar dayai.

Samun guri Modu yai yaxauna daga kujerar nesa dashi,

"Ranka yadad'e yai k'arko my guy,yerwa nayinka fiye da tunanin mutum"

D'an Murmushin k'arfin hali sarki Aliyu hydar yai cikeda nutsuwa yace,

"Godia nake guy,yaya hidima?!"

"Wannan seku mutumina"

Y'ar daria sarki Aliyu hydar yai,

"Guy kaima kabiyo sahu ai"

"Kaide bari kawai"

Shiru sukayi dukkansu na d'an wani lokaci Modu nata tunanin tayaya xe sako maganar Ammi ahankali yace,

"Da fatan kaje kun sasanta da Ammi"

"Ance maka nayi fad'a da itane??"

"No,yaxa'ai kai fad'a da ita kawaide yadda kake ignoring d'inta hakan be kamata ba"

"Plss let me be Modu,idan Kasan abinda kazo fad'a kenan to xantashi nabar maka wajen"

Shiru Modu yai kawai dan it's being ages da sarki Aliyu hydar yaki rashi da Modu har ya manta shiru Modu yai cikin sigar jan hankali yafara magana,

"Wata rana wani sahabin manzo SAW yaje wajen manzon Allah sai yace dashi yarasulullahi wayafi cancanta dana kyautatawa sai annabi SAW yace dashi mahaifiyarka sai mu'awiya d'an haidata yasake cewa dashi sai kuma wa?!sai manzo yace mahaifiyarka sai mu'awiya ya k'ara cewa sai kuma wa?! Sai manzo SAW yace mahaifiyar ka,sai mu'awiya ya k'ara cewa sannan kuma wa?! Sai manzo SAW yace mahaifinka,

"Kaga guy wannan Hadiths d'in yana mana nuni da muhinmmancin uwa kaga seda yakira uwa sau uku kafin yakira uba,Guy kada kabari wasu can suk'ara yin galaba akanka su shiga tsakaninka da mahaifiyarka kada kazo kanayin nadama domin idan kace xaka bijirewa Ammi to wallahi Allah baxe barka ba irin wahalar datasha wurin d'aukar cikinka guy kayi tunani akai"

Dan siririn tsuka sarki Aliyu Hydar yaja tareda kauda kansa gefe daga kallon Modu murmushin dayafi kuka ciwo Modu yai ahankali yace,

"Guy kada kabari Ammi taxubar da hawaye akanka domin yadda kake mata xe iya sanyata hawaye kuma hawayen iyaye musibane guy,kaje kanemi gafarar Ammi kasanyata daria guy please i beg of you baxan mantaba if you can recall a islamiyar mu then akwai wani hadiths da akai mana shi shima wani mutumine yazo wajen manzo SAW seyace dashi ni naxo natafi yak'i tare dakai amma nabar iyayena sunata kukan rashina atare dasu sai manzo SAW yace koma wajen iyayenka kasanyasu dariya kamar yadda kasasu kuka domin kukan iyaye yanasa al'arshin Allah ya raurawa,

SON RAI KO ZABIN IYAYE?!(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now