1

8.6K 339 17
                                    


DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN K'AI,WANNAN LITTAFI ME SUNA A SAMA K'IRK'IRARRENE BA FARUWA YAI DAGASKE BA,SUNAYE DA GARURUWAN CIKI DUK NASANE SABODA NISHADANTAR WA,SABODA HAKA A KIYAYE KADA A CANXA MIN LITTAFI KO DAUKAR WANI B'ANGAREN NA CIKINSA DUK WANDA YAI HAKAN............!



Wannan littafi SADAUKARWA ne agareki; cutest mommah😘(Xarah bukhar)
_TUKWICI ne agareku;billyn abdul (Tawan)tareda my ya hajja😘💯


nanahafsat.wordpress.com


Particular thanks gs to you uwar d'akina, daga shafi na d'aya zuwa na biyar duk nakine (Ummi A'isha)😘💞thank you for working on this book in various ways...


Banmantaba dakeba
Dota feedhom😘😘gaisuwa mai tarin yawa agareki,Allah ya albarkaci rayuwarki aduk inda kika shiga😘💞




_1_
OXFORD UNIVERSITY ENGLAND;


"Sugar boo,yanxu haka xaka tafi kabarni?!"
Wata budurwa me kimanin shekara ashirin da biyu Ruwan wankan tarwad'a tanada kyau dede gwargwado Ke fad'in haka yayinda tasauke idanuwanta dake d'auke da fix lashes akan wani kyakkyawan saurayi dake sunkuye yana d'aure mad'aurin takalminsa samfarin designer din zara da alama dashi take magana...
*D'ago dara daran idanuwansa yai wa'enda suke d'aukar zuciyar duk wanda yakalleshi ya d'ora akanta,cikin sanyayyar muryar shi me kamada sanyayyar ruwan sanyi ahankali kuma anutse Kamar ana busa sarewa yace;
"Basma yakike so nayi uhm?! baaba yakira waya yace Lalle nakoma Nigeria yau, Kuma I have no choice" yak'arashe xancen yana mik'ewa tsaye..
Kan Faffad'an k'irjinsa dake tafiya da ita tafad'a tana rusgar kuka tana shak'ar k'amshin turarukan jikinsa dake cakud'e da k'amshin designers tana magana ahankali cikeda shagwab'a..
"To baby se yaushe kenan?! Nikawai bari in shrya inbika kawai inyaso Idan an d'aura auren semu da......"
Bata k'arasa abinda xata fad'a ba yasa hannu yatureta daga jikinsa idonsa yakad'a yai jawur muryarsa har rawa take yafara fad'in;
"Basma for how many times xance maki kibar xancen xaki bini muje gidanmu tare?! nace kidinga kama kanki, wallahi kika kaini k'arshe zan mugun sa..."
Caraf basma tacafe xancen taname had'a hannuwanta guda biyu alamar hakuri..
"Shikenan sugar boo, Allah yakaika lapia , karka manta ka kirani Idan ka isa plss"
"Naji..."shine kawai abinda kyakkyawan saurayin yafad'a
Cikeda azama basma tad'au jakarsa had'e da jan akwatinsa samfarin designer d'in giogio Armani da d'ayan hannunta.. Suka fice waje inda motar daxata kaishi airport ke jira.. Saurin sallama yai da abokansa dake jiransa awajen berkley Nottingham hall yayi sannan ya juya yashiga mota ko kallonta beyiba yashiga maxaunin owners corner yaxauna bayan driver yabud'e masa.. Idonta yaciko taf da hawaye se binsa take da kallon soyayya cikeda fargabar karta rasa sahibin nata da take dakon soyayyarsa kowacce rana..
"Sugar boo"tace hakan muryarta tana rawa ,idanuwanta na fitar da ambaliyar hawaye
Shikwa driver harya saka key xe tashi motar, saurayin yatsaidashi;
"Hold on a second,"
Kyakkyawan saurayin yace hakan yana me juyar da dubansa xuwaga basma
"Yass basma, we r running out of time ?! What is it now uhm?!"
"Yareema haydar... Please take care of my love for you, you know I love you, sugar boo I'm so so afraid that...."
"Ssshh! Basma nothing can separate our love,kece _Son Rai na_"
"But sugar boo..."
Saurin katseta Aliyu Hydar yai don baifiya son magana ba don ma Itace shiysa haryake bata amsa..
"Say no more plsss,I will call u Idan na isa,take care of yourself,read hard and study well..."
Bata Iya bashi amsa ba sema kuka dayaci k'arfinta don gani take Idan yatafi shikenan sun rabu har abada don Ita kanta tasan ita take dakon soyayyar Hydar ,kusan rabin yan matan makarantar sonsa suke ita d'ince de yake kulawa sama sama saboda azababban nacin datake masa,bawa driver umarni yai dayaja sutafi,, suna xuwa airport aka bud'e mashi private jet yashiga ciki ,wanda ko'ina ajikin jirgin anrubuta _H_R_H SB(his royal highness,shehun borno),, mintina k'alilan jirgin yai booting sannan yad'aga xuwa sararin samaniya, shikam yareema Hydar gyara kwanciyarsa yai akan doguwar kujerar dake luntsumewa don laushi yaiwa kansa matashi da pillow ya lumshe idanuwansa yana tunanin neman me baaba yake masa?! Allah de yasa lapia ...cike da tunani barkatai bacci yai awun gaba dashi ciki harda na'cac'can nacin da basma take masa Kamar ba mace ba!!!!
WANENE YAREEMA ALIYU(HYDAR)?!
Aliyu (Hydar) Shehu Bulama Goni saurayi ne d'an shekara talatin,me d'auke da kyawu wanda duk ko yaya ka d'ora idonka akansa seka furta kalmar tubarkAllah,d'a ne ga mai martaba shehu Bulama,sarkin Borno state, mahaifinsa mai martaba yanada mata guda uku hajia gajiram sheriff itace matarsa tafarko se hajia Hajjagana Ali Itace matarsa ta biyu se hajja yakolo bukar Itace amarya tak'arshe,Hajiya gajiram matarsa tafarko tanada y'a y'a uku,mata biyu namiji d'aya; babagana,falmata sekuma ayiya.. While hajia hajjagana tanada y'a y'a hud''u: usman(Ngari) se Aliyu(hydar),Aisha wacce suke kira da (Aysa)sekuma auta affy, amarya hajja yakolo kuma tanada yay'a biyu; fannah da kuma Rukymamah...!
__Mai martaba shehun borno mutum ne me halin dattako da sanin yakamata da darajta al'umma da kula da hakk'ok'insu, shiyasa mutan borno suke sonshi, bakuma ya nuna son wani b'angare akan wani b'angare dukkan yaren garin yana mulki dasu kan zuciya d'aya kama daga kanuri,babur,Fulani da sauransu sosai yake yin mulkinsa na kanem empire bisa yadda yagada daga hannun mahaifinsa marigayi Bulama Goni..
*hajia gajiram sherrif uwargidansa tafarko da amaryarsa hajiya yakolo sune suke xaune a masarautar while hajia Hajjagana mahaifiyar su Aliyu Hydar tana xaune ne acan wani b'angare a jihar maidugurin cikin d'aya daga cikin tanfatsetsen gidan na shehurin(shehun borno palace) a unguwar damboa road dake garin na maiduguri hakan yafaru ne tun wata matsala da tatab'a faruwa lokacin yareema Ngari(usman)ne kawai d'anta aduniya!
**Awanni masu yawa ne suka kai yareema Aliyu hydar gidah Nigeria.. sannan suka d'aga xuwa garin maiduguri,suna xuwa airport motoci a tawaga sukaxo d'aukarsa ,kowacce mota d'auke da tambarin h_r_h SB ajikinta har guda biyar,ajere suke tafiya har shehuri(palace d'in sarkin borno)....!

[4/22, 4:53 PM] My Xoxo: ••SON RAI KO ZAB'IN IYAYE?!••

💜?👨‍👩‍👧

SON RAI KO ZABIN IYAYE?!(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now