11

4.2K 164 0
                                    


****

"Wa'alykm salam.."

Ammi ta amsa sallamar tasa xaune take akan doguwar kujera mecin mutum uku hannunta d'auke da remote tana rage volume na tv..

Gefe yaxauna daga k'asanta kansa a k'asa ahankali cikin muryar girmamawa yace,

"Ammi barka da rana"

"Barkanmu Aliyu..Affy tace maka inason magana dakai ko?!"

"Eh Ammi"

"Yawwa Aliyu magana nakeson muyi dakai kabani hankalinka nan kana jina?!"

"Eh Ammi..."

"Wato Aliyu so nake kafad'amin gaskiar al'amarin dake faruwa tsakaninka da matarka Basma,kanata wasa da hankulan jama'a kace taje England ne wajen malaminsu kan abun graduation dinsu segashi da mukasa aka binciko sam babu wani abu dayai kama da haka,

"To inason kagayamun gaskiar al'amari shin Menene yashiga tsakaninku kake kwana kwana,kuma wani sabon labari yazo mna kan cewar anga Basma a kano which means tana gidan iyayenta kenan..."

Shiru Ammi tai tana d'an girgiza kanta,

"Aliyu bansanka da k'arya ba,bansanka da b'oye b'oye ba Aliyu bakada rufa rufa baka b'oyewa iyayenka duk lamuranka hak'ika wannan abu dakayi ya mugun tayarwa mahaifinka hankali yace mun ya tuttunku b'eka akan maganar Basman kak'i,

"Kagaya masa kome aciki kanata inda-inda,hakan ba k'aramin d'aga masa hankali yai ba ganin baka b'oye masa abinda yashafe ka,shin Aliyu menene ya had'aka da Basma?kuma wane mataki kad'auka akanta..."

Shiru sarki Aliyu Hydar yai shi kansa yasan be kyauta ba na rashin shawartar iyayen nasa...

"Kiyi hak'uri Ammi...wato abinda Basma tayimun nayi nayi na yafemata na kasa kuma ban yanke hukunci bane don natozarta maku a'a sam bahaka bane kawaide nayi mata hakanne don tasan duniya makaranta ce ko tayi hankali.."

Ajiyar zuciya Ammi tasauke d'an duban Aliyun tai kafin tace,

"Shin wane mataki kad'auka akanta har kake neman yafiyarmu,kuma metai maka da har xaka yanke hukunci batare da shawartar nagaba da kaiba?"

Gyara xama sarki Aliyu Hydar yai sannan ya shiga gayawa Ammi duk abinda yafaru ya k'ark'are da,

"Nikuma lokacin i was out of control shi..shine kawai na rubuta mata takardar saki saboda koda na kyaleta baxata ji dad'in xama dani ba..."

Salati Ammi tashiga rafkawa kafin tad'aga hannunta tamai alamar dak'uwa,

"Ungo nan Aliyu nace ungu nan,au yanzu shine kasakar masu y'a bawani bincike babu komai?!katab'a jin ko ganin wanda akace maka yayi saki a shehurin nan tun kaka da kakanni?,

SON RAI KO ZABIN IYAYE?!(COMPLETED✅)Where stories live. Discover now