“Babu komai Zinneera na yafe miki Allah dai yai miki albarka”

“Amin. Ina Ya Nabeel ne?”

“Ina jin yana dakinsa Aleeya ki rashi”

Umma ta fada sai Zinneera ta mike tsaye. Sai Zinneera ta mike tsaye tana fadin

“Ba ri na same shi ciki”

Ko da ta shiga dakin wayarsa na hannunsa yana chatting hasken wayar na haska fuskarsa tana ganin yadda yake mata far'a. Kusa da shi ta zauna tana murmushi.

“Yar gudun Hijira kin dawo?”

Ta yi dariya.

“Kin yi tunanin mai kyau da kika gudu Zinneera, ko da ban so kika je gurin Hajiya Karima ba amman kin yi tunani mai kyau da kika je can ba kije wani gurin daban ba, amman ya akai kikasan inda take?”

A nan ta bashi labarin komai ciki har ta gutsura masa tarihinta na zamansu da Abbah.

“Akwai abubuwa da yawa Nabeel na tabbatar da za ka ji su duka da kaima kanka za kai ma Mama uzuri, kuma fahimce ko tana da laifi kadan ne, duka abunda Abbah ya fada mana ya saka mike ta tsanarta ba gaskiya ba ne, Mama ta sha wahala a zaman da tai a gidan nan kuma abunda ta aikata saboda babu yadda za tai ne”

“Amman Zinneera kina da tabbacin gaskiya ta fada miki?”

“Mi zai sa tai min karya Ya Nabeel, ko da ba haka ba ne ya kamata mu mutunta hakkin uwa ya wuce wasa, daukin ciki kawai ba karamin hakki ba ne, kuma ina ta tabbacin ta yi nadamar abunda ta aikata, tan da wasu iyalin a can amman she's care for us saboda tana son mu, ba kuma wani abun take bukata a garemu sai soyayyarmu”

Tasa hannu a jakarta ta ciro 50k ta mika masa.

“Mijinta ne ya bani wannan ni kuma ban san abunda zan yi da shi ba,so i decided na baka 50k ko za kai wani abun na bawa Umma sauran, tun da Abbah na ga Sadam ya bashi”

Nabeel ya karbi kudin yana murmushin jindadi lallai Zinneera ta yi hankali tun da har ta san ta fada masa wannan maganar kuma ta dauko kudi ta bashi ta ba Umma.

“Thank you so much”

“Thanks too, amman ina son dan Allah ko dan ni ka yafewa Mama kuma ka kirata wani lokacin ku gaisa mu bar komai kamar ba komai ba Nabeel let's be united again, we have two parents yanzu and both suna son mu, sai mu kara na mu iyalin cikin farinciki”

“Zinneera kin yi hankali yanzu kamar ba ke ba, zuwan ki Kaduna Hajiya Karima ta canja ki”

“Bata canja ni ba Ya Nabeel duniya ce ta canja ni, ita ce tai min karatun ta natsu na gane komai a yanzu”

Ya sauke ajiyar zuciya.

“I'm happy”

“I'm happy too nima ina ji mutum a yanzu”

Ta fada tana hawaye. Sannan tai ma dan'uwanta sallama ta fito dakin yana biye da ita a bayan taje gaban Umma ta aje mata ragowar kudin. Umma ta daki kirji ta sake daka sai ta fashe da kuka bata tsammanin Zinneera za ta dauko kudi mai yawa haka ta bata ba, 50k kusan sai tace bata taba rika 50k na kanta ba, a zuciyarta tana ta yawa Sadam a tunaninta shi ya bata kudin domin Zinneera bata fada mata inda ta samu kudin ba, tana ta sausayin Aleeya da yanzu ita ce a wannan dalar ba Zinneera sai dai babu yadda ta iya da hukuncin Allah.

Har bakin mota suka ragota ta shiga suna daga mata hannu Sadam ya kama hanyar gida da ita, da dayan hannunsa yake tuki yayinda dayan yake rike da hannunta yana murzawa a hankali, ita kuma tana ta kallonsa kamar all her life depend on his face ne. They arrived late da gangan ta ki bude motar har sai ta ya zagoyo ya bude mata sannan ta fito ya rufe motar.

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now