“Thank you Mommy you're such a wonderful mother”

Suraiya ta fada tana share hawayenta.

“Zinneera ta yi sa'ar samunki a matsayin suruka, and i know your grandchild zai yi alfahari da ke”

Sadam ya fada idonsa a rufe yaja jin kaunar mahaifiyarsa har cikin ransa.

“In-Sha-Allah, zan zame mata uwa saboda kai, as for my grandchild ba zan iya fadar abunda zan masa a yanzu ba, all what i know is i will be a perfect grandma for him, kaje Daddy ka yana son magana da kai”

Ya saketa da sauri cike da farinciki marar misaltuwa ya nufi part din Daddy ba ki har kunne.

ZINNEERA POV.

“Na auri mahaifinku a lokacin da aure yake da dadi da saukin yin, a lokacin ba Motarsa ce yake ja ba, motar wani mutum ce idan yai direbanci sai ya kawo masa kudinsa ya dauki ribarsa, a lokacin daga sokoto yake dauko fasinjojinsa ya kawo su nan garin Kaduna, ni kuma ina siyar da wake da shimkafa a cikin tashar, a haka muka hadu Allah ya hada jininsu har ta kai mu ga aure, a lokacin da na auri mahaifinku yana ciyarda ni ya shayar da ni, amman babu sutura, shi ma kuma ban taba damuwa ba, saboda na san cewar ba ko wane namiji zai tsare maka duka ba, samun mai yi maka ci da sha da sutura dace ne, wani idan ya baka ci da sha ba zai baka sutura ba, muna zaune cikin farinciki da kaunar junanmu, har na haifi Nabeel, haihuwar fari ce amman kala uku yai min har na goyon jariri, ban taba nuna masa hakan be min ba ina zaune da mijina lafiya kalau, a nan garinmu kaduna na dawo nai wanka gida, bayan na gama na koma muka cigaba da rayuwar mu kamar kullum har na samu cikin ki, a lokacin da na samu cikinki sai komai ya canja, mutumen ya karbe motarsa ya zama ba shi da aikin yi, kuma aka gagara samun wanda zai ba shi wata motar, kayan dakina na siyar da duk wani abu da nasan idan an dake shi zai iya zama kudi, na hada kudi mai yawa na bashi ya kama shago ya zuba kayan masarufi a ciki, mu ka cigaba da rayuwar mu a haka cikin rufin asiri, kina da wata biyu a cikin cikina shagon ya kone komai be fita ba, a cikin gida ya rika min kuka kamar mace ni nake ta bashi hakuri, a lokacin mun shiga cikin mawuyacin halin tsananin na rayuwar abunda za mu ci, daker na iya hada kudin mota na je garinmu kaduna aka siyarda gidan da baban mu ya bar mana aka raba aka bani hakkina na dawo na kawo masa ya siye sabon mashin ya soma yin achaba, amman idan ya samu baya iya bani abunda zai wadatar da ni da Nabeel sai dai mu lasa tun ina hakuri har na kai ga yin magana, sai yace min saboda na siya masa mashin zan masa gori, daga ranar ban sake ce masa komai ba, ashe kudin da yake tarawa aure yake son ya kara har ya fara neman wata bazawara, ban taba sani ba har sai dai cikinki ya kai wata biyar shima ta dalilin hadarin mashin din da yai har ya karye a kafa, sai yace wa abokinsa ya bashi kudin auren da yake tariya ya nemi magani idan ya ji sauki sai ya nemi wasu, matar da yake nema har cikin gidan ta zo dubashi a ranar na ji kamar na mutu bayan fitarta babu kalar fadan da ban yi da shi ba. A ciwon kafar ya cinye kudin auren kamin kafar ta warke mun sha wahala ni da nake jinya da kuma shi da yake ciwon, har mashin din sai da aka siyar muka koma ba mu da komai, kuma baya fita ya nemo wai ala dole sai ranar da wani ya kirashi ya bashi mota ko wani abun sana'a, ko wace sana'a ganin yake ta masa kadan kuma zata iya sakawa a raina shi ko a kalleshi makaskanci, har ta kai mu yuni da yunwa mu kwana da ita ga ciki ga Nabeel ga ni, idan ina son na ci na koshi sai idan na karbo wanki na wanke an biyani ko kuma na yi surfe na hada kudin na siye wani abu kuma tare da shi ake ci. Amman daya tashi saka min kin san me ya ce?”

Ta yi kasa da kanta hawaye na sauko mata.

“Cewa yai yar da zan haifa bata da kashin arziki, wai wani cikin tun yana karami ake samun wadata har a haifeshi, amman ke tun da na samu cikinki kullum cikin bala'i yake kullum da kalar abunda yake samunsa, na ji babu dadi saboda na san dukan abunda zan haifa a cikina yake kuma jinina ne, a haka ya dauki karan tsana ya dora min kamar ni na aiko masa da abubuwan da suke samuwarsa, kwana hudu ina nakuda ba akaini asibiti ba kuma be kula daya kai ni asibitin ba idan nai magana sai yace ba haihuwa ba ce saboda ba ki kai wata tara ba, a lokacin kina da wata bakwai a cikina, ranar wata lahadi na haife ki da taimakon wata makociyarmu, yar karama kika fito har ake cewa sai an saka ki cikin kwalba sai an miki kaza amman ban nunawa kowa ina son zuwa asibitin ba, saboda na san ba ni da kudi kuma shi ba zai yi wani kuzarin nema ya kai ki ba, domin da an taba shi cewa yake ba shi da gabas ba shi da yamma ba shi da kudi, tun da na haife ki ya dora min karan tsana sai dai ya saka min ido ba zai nemo ya bani na ci ba, da jegona nake wankakau na ciyarda kaina, icce wannan na ruwan zafi mahaifinki be siya ba, da tsohon zanena na ke goyaki ko na tara ki ciki, tufafi ka sai wadanda mutanen arziki suka ba mu nake sawa, ana saura kwana biyu ayi suna ya samu mota aka masa lodo zuwa enugu, tun daga lokacin ban sake saka mahaifinki a ido ba, sai da aka yi sati biyu da sunanki, be yanka miki ragon suna ba, be aiko a tambayi lafiyata da ta ki ba, balle ta Nabeel be aiko mana da komai ba, mutane unguwa suna ta mana gulma wai na yi wankakau na samu na ci, har gyaran wake na ke irin na masu shago su biyani na ci, na kwana da kuka na tashi da bakinciki har ya dawo. Da ya dawo nai masa gana na kai kararsa gurin yan'uwnsa sia ya ji haushina ya ce ya sake ni, nasam daman yana neman dalilin rabuwa da ni saboda ya samu damar saka bazawararsa domin a wacan lokacin gidan daki daya ne, da na buga waya na fadawa mahaifiyata cewar ya sake ni sai tace bata yarda na zo da dansa ko daya ba, a dole tasa na aje ki na barki tare da Nabeel na hada yan komotsun karana da suka rage na je gidan wani dan'uwan mahaifiyata ya bani kudin mota na koma kaduna, shiru babanki be biyo bayana ba kuma be aiko min da ku ba, sai kawai na samu labarin abubuwa sun bude masa har ya samu wata ya aura ta rike ita ma take shayar da ke, kuma ya gyara gidan ya siye motar kansa ta jigila, hakan yasa na maida hankalina gurin neman abunda zan dora da kaina, ina kokari na cireku da mahaifinku a raina amman na kasa, mahaifiyata ta kulla min jari ina hada turaren wuta ina kaina manyan ma'aikatu ina siyarwa idan wata yai sai naje ka karbo kudina, wasu na min kallon yar iska, wasu kuma suna taya min iskanci har na rasa wanda zai zo gurina da sunan neman aure sai fasikanci, a lokacin na yi ta kuka ina bakinciki mutuwar aurena domin ina ji ina gani auren ya gagareni ga tunanin makomarku sai abun ya zame min biyu, ga zaman gida babu dadi kane su rainaka kowa ganin damar ma yake, iyaye ma su yi ta ganin kamar kana takura ma kanensu ga gulmar mutane sai na rasa inda zan saka kaina.
Ina cikin haka na hadu da mahaifin su Suhail ya nuna min yana so na kuma aurena zai yi, kasancewar mahaifiyarsu Suhail ta rasu, na gabatar da shi a gurin iyayena akai bincika muka fahimci juna har aka daura mana aure, a nan na gane wahalar ba ta kare ba, domin yana da manyan yaya mata sai suka rika kishi da ni suna nuna min ni ba uwar ba ce, kamin su yi aure na sha wahalar su sosai, sai da na rika neman ya rabu da ni da kansa Suhail ne kawai na ke jindadinsa, shi yake tsawata musu har na samu aka aurar da su tare da shi, sannan na fara jindadin rayuwar aure ina yin yadda na ke so daga ni sai yaya a cikin gida, amman duk da haka bana da walwalar zuci saboda tunaninku, shi da kanshi ya fahimci haka shiyasa ya bani damar zuwa na zauna a sokoto saboda na samu fahimtar juna ni da ku.... Na san ban be dace na tafi na barku ba musamman ke da kike shan nono amman dole ce ta saka saboda bakin halin mahaifinku amman ina godiya ga Allah daya ba ku uwa mai tausayi kamar Umma”

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now