32

2.3K 240 29
                                    

Tun rannan khalifa bai Kuma sanya zarah a idonsa ba duk sai ya shi ga damuwa, yau Kuma ya tashi da marmarin ganin ta, ya kasa samun mafita yanda zaiyi ya ganta shi ma mamakin Kansa yake yanda ya damu da ita kullum cikin tunanin ta yake har mafarki yake da ita, bai taba nadamar abinda yayi ta mata ba sai yanzun.

Gani tunani bazai amfane shi ba yasa ya dauki makulin motar ya nufi waje ya shiga motar, hanyar gidan su zarah ya nufa Dan ji yake in bai gan ta yau bah bazai samu sukuni bah


Zarah ♨️


Tunda aka salame ta daga asibiti kullum sai Samir yazo yayita jan tada hira tun bata sake jiki dashi har ta dan sake.

Yau ma zaune suke a garden in gidan su Zahra yana bata labarin umman sa, tana dariya saboda yanda yake labarin ta she's that type of funny women, suna cikin haka motar khalifa ya shigo dagowa sukayi suka Kai motar sannan suka kauda kai suka cigaba da hira kamar basu San da shigowar saba.

Cikin zafin nama khalifa ya fito daga mota ya nufe su, idon sa sun kankance zuwa ja, sai huci yake kaman wani Zaki, Yana isowa wurin su yace "Samir baka da hankali matar tawa kake...........

Katse shi zarah tayi tace " waye matar ka amma ba dai Ni kake nufi ba Koh" ta karasa maganar tana nuna kanta cikin masifa

Dariya Samir yayi yace "ka dai ji da kunen ka tace ita ba matar ka bace"

"Samir abinda zaka saka min dashi kenan, my wife Samir kana neman Mata na" khalifa yace cikin mamaki

"Da alama dai tsufa ya fara Kama ka, shi yasa ka manta sanda ka sake ta, Kuma da kake zancen Ina neman matarka, oh sorry tsohuwar matar ka da ka adanna abinka ba ka sake taba bazan samu damar neman taba" Samir ya karasa maganar Yana dariyar shakiyanci.

Aii Dan haushi khalifa bai San sanda ya naushe shi ba, daga Nan suka fara kokawa, Zarah kuwa sai kokarin raba su take tana Basu hakura su bari.

"Baza ku saki juna ba" Abba ya daka musu tsawa, sakin juna sukayi kowa na aikawa Dan uwan sa kalon tsana.

"Me yasa kuke fada da girman ku, in son ta kuke then let her choose between you guys not fight" Abba yace cikin taushin murya

"Kayi hakuri"  suka fada a tare sai Kuma suka juyo suka bankorawa juna harara.

"Is okay" Abba yace Yana murmushi Dan ya gan hararan da suka ma juna.

Daga nan suka Gaida shi, kowa ya nufi motar sa ya bar gidan, Khalifa kuwa gidan su ya nufa Dan yanzun abinda yaje ji a zuciyar sa yasa ya manta da gargadin da Abi ya Ma shi.

Tuki yake Hama hankalin sa bai wurin tuki, yanda ya hango su zarah yayi ta tunawa, har bai San sanda wasu hawaye masu matukar zafi suka fara safa da marwa a fuskar sa bah

Vote
Comment
Share

'Ya Mace (Completed)✅Where stories live. Discover now