19

2.3K 259 15
                                    

"ummi khalifa" zarah tace bakin tana rawa "eh shi din me ya faru?" ummi ta tambaya ganin yanda duk ta firgice "fara daidaita nutsuwarta tayi tace "a'a bakomai" girgiza kai kawai ummi tayi tace "toh sai kiyi sauri dan yana falon baki" cikin sanyin jiki, tace "toh ummi" murmushin ummi tayi zuciyar ta cike fal da farin ciki, ganin khalifa bai ki yarta bah duk ba'a budurwa zai aure taba, haka dai tafita a dakin.

Zarah kuma jikin ta duk a'sanyanye tamike tafara shiri, tunani take yanda zata hada ido da ya khalifa "toh uwar me zata mishi" aka dai ta yita tunane tunane har ta gama shiri ta nufi, falon da khalifa ke zaune.

Kamar wacce kwai tafashe wa ajiki tayi Sallama sannan ta shiga, amsa mata yayi fuskar nan a tamke kaman wanda akace uwarsa ta mutu, ganin yanda fuskarsa babu anuri ko kadan yasa cikin zarah kara sanyi tace"uhmmn gani" wata uwar harara ya bankaro mata da jajayen idanuwan sa, yaja wata doguwar tsaki yace "ba ganin ki na zo yi bah, gargadi nazo na miki, Dan wlhi tallahi bilahil azim kin ji nayi rantsuwar muslimi  in kika kuskura kika bari aka yi wannan auren, toh ki sa rai cewa bara ki taba samun farin ciki a rayuwar ki bah, yanda kema yanzun kika bakanta min rayuwa aka zan miki, dan sai na dandana miki bakin cikin da kika a dasa min, yanda kika bari Abi da Ammina suka yi fushi dani, toh aka nima zansa Abba da Ummi suyi fushi dake, kuma yanda aka lika min ke toh aka zan mai dake karamar bazawara, saboda aka ina mai gargade ki,  kiyi gaggawar fada ma su Abba a dakatar da wannan auren" ya fada yana zuba mata idanunsa.

Tsaki zarah tayi sannan tamike tsaye sanda tagama mishi kalon sama da kasa sannan tace "ka gama? Toh bari kaji auren kane baka son nayi koh, toh  aure da kai dole ne kuma baka isa ka sake ni bah, ehhe kuma da kake batun na je na gayawa su Abba bana son auren, why not kai ma kaje ka sanar dasu tunda baka da sauran kunya atare da kai"

Wani mahaukacin mari khalifa ya kifa mata sanda ta fadi a'kasa sannan yace "waye mara kunya, har kina da bakin kira na mara kunya, karamar karuwa kaman ki mazinaciya kawai"

Jin furucinsa yasa Zarah dagowa dasauri tana kallon shi wata irin bakin ciki na tokarar zuciyarta, wato itace karamar karuwa kuma mazinaciya uhmmn bata gan laifin shi bah, tun da ita taja ma kanta, fara maida hawayen dake taso mata tayi tace "ni ba karuwa bace, kuma kai ne mazina....

Sauran magana makale mata yayi saboda marin da khalifa ya kara mata "wawiya, dakikiya, shegiya, kuma nakara fada karuwa, mazinaciya, mara hankala wace ta zubar da mutuncin ta dana gidansu a titi, wace ta kunyatar da iyayen ta a idon mutane, wace ta bata tarbiyar da uwarta ta mata, mara kunya kawai har kina da bakin kira na mazinaci bayan karuwancin da kike acikin wannan garin, bari kiji wannan auren sai an daura shi kaman yanda kika ce amma karki manta sai na saka miki ciwon zuciyar, saina kuma bakantar miki da rayiwa" wasu zafafen hawaye ne suka fara zubo ma zarah............

SORRY FOR THE LATE UPDATE❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

LOVE YOU GUYS

VOTE
COMMENT
SHARE

'Ya Mace (Completed)✅Where stories live. Discover now