13

2.5K 267 11
                                    

BISMILLAHI RAHMANI RAHIM

Shiru kowa yayi bayan ta gama bada cikeken labari yanda abin ya faru suka hau jimami wannan alamarin sagir da suke ganin shi kamilalen mutum ta yazai aikata wannan abin toh in bah shi bah wa dan shi kadai suka sani a matsayin saurayin zarah tun tasowar ta bata taba saurayi bah sai sagir, Baba ne yayi gyaran murya Wanda ya karkato hankalin su gare shi yafara magana "Zarah kin tabatar da cewa wannan shine aini kuma gaskiya abinda ya faru" Hawaye na cigaba da silowa daga idanuwanta tace "eh baba shine"

Iska mai zafi Baba ya furzar yace "a Kira sagir din a tambaye shi kin yarda" cikin murya mai cike da rauni Zarah tace "eh na yarda"

"zan sake tambayar ki akaro na biyu sagir ne Koh ba sagir bah"

"wlhi baba sagir ne"

"Toh Muhammad bugo masa kace ina son ganin shi yanzun" Baba yace cikin bacin rai.

"Toh" Abba yafurta cikin sanyin jiki gami da zaro wayar sa yadanawa sagir Kira ringing biyu ya daga gaisawa sukayi da Abba a'mutunce sannan Abba yafada mishi sakon Baba cikin girmamawa yace "toh gashi nan zuwa" nan ya kaste wayar ya hau tunani me zaisa Baba ya nime shi can wani tunani ya darso mishi kodai zarah ta sannar dasu abinda ya faru ne, sai kima ya girgiza kai dasauri yace "a'a I know zarah she will never do this to me" toilet ya shiga ya fara wanka Yana sake sake me yasa Baba zai nime shi.

Aka dai ya gama wanka yayi shiri ya nufi wajen motarsa ya shiga bai zarce koh Ina bah sai gidan baba, da salama ya shiga falon Wanda kamar jira suke duk suka juyo suka zuba mishi ido ko Salamar shi basu amsa ba sai Baba da Abi dasuka yi karfin halin amsawa shima sagir gani irin kalon da mazaunin falon suke aika mishi yasa ya fara jin sanyin guyiwa, ko dai zarah ta fada musu ne a'a ya fada yana mai tabattar wa kansa zarah bazata taba tona musu asiri bah cikin taushin murya ya gaida dasu amsawa sukayi cikin takaici,  ba yabo ba fallasa baba yace "zauna" a kasa ya nimi guri ya zauna kaman wani munafiki.

"zarah" Baba yakira ta cikin kakkausan murya, jiki na rawa ta ansa da "na'am Baba" maimaita abinda ki kace ahankali zarah ta fara maimaita musu duk abubuwan datace  dazun, aii bata gama ba zufa ya fara tsatsafo ma sagir tako ina sai zazare ido yake kamar mara gaskiya, sai da Zarah ta dasa aya sannan tayi shiru "sagir ka dai ji abinda tace shine ina son tambayar ka dan girman Allah da darajar iyayenka kafada mana gaskiya shin kaine ko a'a"

sagir da tunda zarah ta fara magana jikin shi duk ya mutu, tambayar da baba ya jefo mishi ne ya kara adasa masa rawar jiki duk ya rude shi me zai ce yanzun ya yarda shine ko ya ki, tsit kake ji a falon kaman ba mutane sagir ne yafara magana muryarsa na rawa "uhmmn ehmn eh a'a uhm" sai kuma ya fara sosa kai saboda yarasa me zai ma ce musu Abi ne yayi karfin halin cewa "toh akan na nufin kaine???

Wani irin dum kirjinsa ya bada sai dukan uku uku kirjinsa yake bakinsa kuwa rawa suka Fara dakyar yadan samu yafurta "uhmmn a'a bani bane" sagir ya fada kaman zai yi kuka a firgice zarah da tun dazun kanta ke kasa ta dago ido hudu sukayi da sagir din.

TOH WATA SABUWA SAGIR DAI YACE BAH CIKIN SHI BANE SHI NE ZASU YARDA DASHI ???KUBIYO NI DAN JIN YA ZATA KAYA

WAITING FOR YOUR VOTES AND COMMENTS

Don't forget to check out my new novel Masarauta

Follow my account Meenarlee ❤️

Thanks 🙏

'Ya Mace (Completed)✅Where stories live. Discover now