“Husaini ina da kishi sosai bana son na kusanci mace da wani namijin ya kusance ta, musamman Zinneera”

“Amman ko dan ka bawa Sadam haushi ya kamata ka aureta, kuma ita wannan yarinyar ba budurwa ba ce? Sai ka hada su biyu ka aura, g budurwa ga Zinneera wannan kishin da kake ji duk zai yaye, amman gaskiya be kamata ka juyawa yarinyar nan ba ya ba”

Sadiq ya busar da iskar bakinsa.

“Gaskiya ba zan iya ba Husaini, wani ya riga ya fasa ta, wanin kuma Sadam kazamin mazinaci be kamata mu yi hako rijiya daya ba no way”

“To shikenan Allah ya kyauta, ni zan wuce a gaishe da Ummin”

Husaini ya bude motarsa ya shiga, sai da ya bar gurin sannan Sadiq ya nufi tashi motar ya shiga ya dauki hanyar gidansa cike da tunanin maganganun abokin nasa. Be tuna da surprise din da Ummi tace ta aje masa ba har sai da ya isa gidan, yana ta sake saken abunda zai tarar da zarar ya shiga falon, sai ya samu babu komai a falon ya duba ko'ina a dakin be samu komai ba. Sai a lokacin ya tuna da ya ma za ayi ya samu wani abu a dakin bayan bata da keys dinsa ko abincin da take kawa masa ai a bakin kofar dakinsa take ajewa ko kuma ta aiko masa idan yana cikin gidan. Wayarsa ya ciro da zimmar kiranta sai yaji ana knocked kofar falon be fasa kiran ba sai ya kirata ya kara wayar a kunne ya nufi kofar falon ya bude. Wani matashi ya gani a tsaye rike da wani karamin akwati baki ya mika masa.

“Wai gashi inji Ummi tace ka kirata”

Hannu ya kai ya karba yana fadin.

“Gani nan ina kiranta”

Sai matashin ya juya shi kuma ya maida kofar ya rufe yana ta mamakin abunda ke cikin akwatin. Zaunawa a saman cushion dinsa yana amsa maganar da take masa.

“4486 shine numbers din bude akwatin”

Ya saka kamar yadda ta fada masa sai ya danna akwatin ya bude. Dollars ne a ciki adadin da ba zai iya kiyasinsu a take ba.

“Ummi kudi na gani”

Ya fada bakinsa a sake hankalinsa a tashe.

“Eh ai nasan kudi zaka gani, naira miliyan ashirin ne, so nake ka biya mutumen mai binka kudi ta yadda zamuyi rayuwarmu cikin aminci”

“Ummi ina kika samo wannan kudin haka? Wa kika roka?”

“Ban roki kowa ba, kuma babu wanda yasan na baka wadannan kudin, yanzu dai ka fara jirashin yanzun nan ya fada maka inda zaka kai kudin, idan ka biya zamu yi magana daga baya”

“Baby i love you, amman wannan zai iya zama sirri a tsakaninmu?”

“Da ba zai zama sirrin ba, da babu dalilin da zai saka na baka har naira miliyan ashiri”

“Thank you”

Ya fada yana lumshe ido cike da tear of joy. Ita kuma ta kashe wayar tana dariya, sai a yanzu yake jin Allah ya masa sakamako da hakurin da yai da kuma musanya masa Ummi amadadin Zinneera, jin sonta yake ko'ina a jikinsa. Cikin sauri ya saka number mutumen ya kira shi, sai da tai ringing ta katse ya sake kira sannan ya daga.

“Ina za a kai maka kudin da bindigoginka?”

Sadiq ya fada kai tsaye. Mutumen yai shiru kamin yai dariya.

“Good boy ashe kana tsoron abunda zai biyo baya kamin nan da shekara daya ko? Sakona ya saka ka maida hankali har ka samo kudin ko? ”

Shiru Sadiq yai yana kokarin gasgata maganar da Zinneera ta fada masa cewar saboda sakon yasa ta auri Sadam ta samo masa kudi kamin nan da shekara daya, be taba yarda ba sai a yanzu ashe da gaske ya turo masa sakon kuma takaranta sai ta goge saboda kar ya gani hankalinsa ya tashi.
Can cikin tunaninsa ya tsinkayo muryar mutumen yana fadin.

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now