“No ni zan kaita ba zan jira ka dawo ba”

Tana fadar hakan ta saki Zinneera ta shiga ciki ta dauko veil dinta ta keys din mota ta janyo hannun Zinneera suka dauko dan karamin stairs din dake gurin tana fadin.

“Nooriyyah ki ku tsaya a gida har na dawo”

“Okay Hajiya Allah ya tsare”

Nooriyyah ta fada cike da tausayawa. Tun kamin su karaso Suhail ya bude motarsa, haka yasa Hajiya Karima ta fasa shiga motarta ta saka Zinneera a motar Suhail ita ma ta shiga motar sai ya rufe musu ya zagaya ya shiga driver side ya fisgi motar kamar zai tashi sama. A haka sai da Hajiya Karima ta matsu kamin su isa asibitin, a asibitin da yake aiki ya nufa da ita already ya kira waya ya sanar da zuwansa, ko da suka isa har bude mata file an kawo mata kujera da zata zauna ana dorata sai yasa hannu ya karbi wayar hannunta ya mikawa Hajiya Karima shi kuma ya bi bayansu da sauri....

A gurin Umma ta wuni har sai da Aleeya ta dawo daga makaranta, idonta a bude yake amman komai bata ganinsa daidai, har lokacin dakin juya mata yake gashi ta kasa ko motsi balle ta tashi. Tunda Aleeya tai sallama bata ji Umma ta amsa mata ba, ta san akwai abunda ya hana ko dai ta zagaya makota ko kuma tana sallah ko tana bandaki, dakinsu ta shiga tana cikin cire uniform taji muryar Umma na kiranta daga dakin ta amsa bata fito ba sai da canja tufafin sannan ta nufo dakin Umma.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, Umma lafiya”

Ta fada tana zagayowa ta gaban Umma ganin yadda take kwance kamar an tureta. Hudu hudu Umma ta rika ganin Aleeya ba ko biyu biyu ba.

“Aleeya ku nawa kuke?”

Aleeya ta waiga bayanta ta ga ita kadai ce a dakin ta kalli Umma da dan tsoro ta ce.

“Ni kadai ce ni da wa kika gani?”

“Ku takwas ne ga hudu can daga yamma ga hudu nan daga gabas”

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, Umma me ya same ki?”

Aleeya ta tambaya tana kokarin rikata ta tasheta, sai Umma tai saurin girgiza mata kai.

“Aa Aleeya ke kadai za ki rika ni dan Allah, ba da su ba”

“Su suwa?”

“Gasu nan tare da ke”

Aleeya ta sake juya taga ita kadai ce a dakin, ita kuma Umma Aleeya takwas take gani idan ta duko ta rikata sai taga duk sun duko zasu rikata.

“Umma rufe idonki”

Aleeya ta fada ganin ta ki yarda da cewar ita kadai ce, itama Aleeyar tsoro duk ya kamata. Da sauri ta rufe idon sai Aleeya ta rikata ta tasheta zaune, Ayatul kursiyo ta karanta mata kafa bakwai ta tofa mata a kai sannan Umma ta rika ganin Aleeya daya sai gumi ya karyo mata ta samu yar salama.

“Umma wai miya faru? ”

“Ni ina zan sani? Ni dai rike min kafa sukai”

“Su su wa?”

“Su dai”

Umma bata son cewa aljannu gani take kamar suna nan a cikin dakin suna jinta.

“Ina Zinneera...?”

“Bata nan”

“Ina taje?”

“Ban sani ba ni dai ban tarardar ita cikin gida ta ba”

“Je ki nemota duk inda take dan girman Allah ki ce ta zo ta shafa min kafata ko zan tashi dan Allah ki nemo ta”

Aleeya ta fita da sauri da dan tsoro. Umma ta hada hannayenta guri daya tana rokonku.

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now