"Amman Umma idan Sadam yaji an zubar da cikin zai iya dora mana laifi shi da Daddy da Abbah"

"Eh ai shiyasa na fada miki, dan bana son kowa ya ji, ai banga ta zama ba dole ayi abunda za ayi a zubar da cikin tun kamin ya girma ko aji, ai shi kina ganin Sadam din kamar be yarda ba zai iya kokarin mayarda aurensa"

"Amman Umma idan ni baya so na fa?"

"Yana son ki ai, ba ke ya fara so ba kamin ta zo ta wargazar da lamarin, sai yanzu na gane ma hassada ce tsagwanronta Wallahi, daman idan baka haifi dan ba dan kishiya ba zai taba son ka ba"

Ya karasa fada tana tana janyo hijabinta. Aleeya da ke binta da kallo tana nazarin maganganunta ta tambaye ta.

"Ina zaki je?"

"Ai ban ga ta zama ba, dole na je na samu yan abubuwan na fara tun yanzu"

A hanzarce ta fice daga dakin har ta kai kowa sai kuma ta dawo ta shiga dakin da Zinneera take kwance tana aikin kuka.

"Ke lafiya"

Jin muryar Umma yasa ta dan dago tana share hawayenta.

"Cikin kike yi ma kuka? Ki kwantar da hankalinki za a samu yadda za ayi a zubar kin ji?"

Ta fada cikin sigar rarrashi.

"Umma ba kyau zubar da ciki, kuma zubarwar ba zai amfana mana komai ba"

Cike da mamaki Umma take kallon jin irin furucin daya fito daga bakinta. Zaunawa tai kusa da ita tana kokarin fahimtar da ita.

"Zai amfana mana, ke za ki samu damar auren Sadiq din, kin ga idan har ya san kin haihuwa zai iya fasawa, kuma daga karshe Sadam din ya wulakanta ki da abunda za ki haifa"

Dagowa tai ta kalli Umma da jajayen idanuwanta.

"Ba zan iya sake aikata wani kuskuren ba Umma ko da hkan na nufi ba ni da hankali, ba zan iya kashe rai ba, ran ma kuma wanda yake a jikina, nasan Sadam ba zai so cikin nan ba, amman ni zan rumgume shi a matsayin kadddarata...."

"Amman ban taba tabbatar baki da wayo da hankali ba sai yau Zinneera..."

"Ban taba yin komai daidai ba, komai nai shirme ne, nawa tunanin dabam yake dana kowa, amman wannan karon Umma ko me za ki kira ba zan zubar da cikin nan ba"

"Ke baki da wayo, a cikin ba a busa masa rai ba, dan tayi ne, sun fada miki ko wata nawa ne?"

"Aa sai gobe idan sun dibi jinina"

"To kin gani, gobe sai kije a auna a gani idan be kai wata hudu ba, salun alun za a cireshi, kuma kin ga idan kika bar cikin nan Sadam ma zai iya cewa ba nashi ba ne, kuma mutane za su tai miki zargi...."

Zinneera ta fashe da kuka.. Har ga Allah bata son zubar da cikin nan, ko da kuwa Sadiq ne ya cilasta mata balle kuma Umma, tasan gaskiya ne abunda ta fada, ta ci amanar Sadam akan me zai so abunda zai fito daga jikinta. Amman ita ta shirya zama da cikin ko da kuwa hakan zai zama wani kuskuren. Umma ta tashi har zata fita sai kuma ta dawo ta karbi wayar Zinneera ta fita ta ita, hankalinta zai fi kwanciya da aje wayar a hannunta gudun kar Zinneera ta kira Daddy ko Sadam ta fada musu kamar yadda tai lokacin da zata fada musu cewar tana son Sadam.
Wunin ranar Zinneera kuka tai ta yi, kukan daya zame mata kala biyu, kukan butulcin da Sadiq yai mata, da kuma kukan cin amanar Sadam da tai, sai a yanzu take gane cewar abunda ta aikata babban kuskure ne, ga cikin da take da shi bata san makomarta ba.
Sai bayan sallah isha'i Umma ta shigo dakin dauke da kwanon ruwa mai wani garin magani a ciki, kusa da Zinneera ta zauna fuskarta gwanin tausayi ta ce.

"Zinneera ya jikin"

"Da sauki"

"Ungo wannan ki sha"

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now