“Hello”

Ya danyi jimmm sannan ya ce.

“Kin tashi lafiya”

“Lafiya kalau, ina asibiti”

“Miya same ki waye ba lafiya?”

“Bana jindadi ne shine Umma tace na je asibiti”

“Ba kya jin dadi?”

Ya tambaya da sauri.

“Me ke damunki?”

A take ta lisafa masa kamar yadda tai ma Dr Suraiya kanwar Sadam.

“Zinneera ina son ganinki idan kin fito asibitin nan”

“Amman tare da Aleeya na zo”

“Ki yi duk yadda za ki iya mu hadu, and ki fada duk abunda likitar ta fada miki kinji”

“To.. ”

Daga haka ya kashe wayar, ita kuma ta nutsa kai cikin ward din, zauna kusa da Aleeya tana jiran sai kowa ya gama fita sannan ta shiga ta kai mata fitsarin,  bata san ta nemi alfarma ta shiga ba.

“Ni na gaji da jira gaskiya gidan zanje, idan an gama sai ki dawo tunda dai ai kin san hanya”

Ban da binta da ido babu abunda Zinneera tai, wani abun daya tsaya mata a makoshi ta hadiye idonta ya cika da kwalla. Sam bata jindadin yadda Umma da Aleeya suke mata a yanzu, Abbah ma kansa ya canja mata bata taba sanin abunda zata aikata zai juyo mata kamar haka ba. A gurin ta zauna sai da kowa ya gama shiga sannan ta mike ta shiga dakin da sallama nikab dinta a hannu kamar dazu. Ko da ta shiga ta tarar Suraiya na hada kayanta da alama ta gama aikinta  sai ta gama komai sannan ta dago ta kalli Zinneera.

“Ya akai?”

“Ga fitsari”

“Je ki aje can”

Ta nuna mata wani guri mai kama da inda ake wanke hannu. Safar hannu ta saka sannan ta nufi gurin ta dauki wani dan abu mai tsawo ta bude fitsarin ta saka ciki, for few seconds ta cire ta zubar da fitsarin a gurin ta zuba wasu sinadaran kashe kwayoyin cuta ta gurin sannan ta zuba ruwa. Sai da ta gama sannan ta dawo gurin abun ta duba shi ganin layi biyu yasa ta juyo da mugun mamaki ta kalli Zinneera, sai ta sake duba abun ta sake kallon Zinneera again. A kwadon shara ta saka abun sannan ta dawo ta zauna still idonta na kan Zinneera baki bude take kallonta. Sannan ta dauki wata farar takarda ta rubuta mata magani ta mika mata.

“Kinje gurin text din?”

“Eh amman ban yi ba saboda ba kudi, kuma sunce da safe zan zo kamin na karya”

“Yes, wannan maganinki ne kije ki siya, and kina da ciki sai dai ba za a iya gane ko wata nawa ba ne sai anyi wacan gwajin fitsarin babba...”

Cikin rudewa Zinneera ta dafe kirjinta.

“Na shiga uku wane irin ciki?”

“Ciki na haihuwa mana”

Suraiya ta fada mata rai a hade. Da sauri Zinneera ta tashi ta fita daga dakin tana hawaye kamar ba gobe... Da sauri Suraiya ta tashi ta cire safar hannunta tana murmushi.

“Oh my God at long last Familyn Kazaure zasu samu first grandchild, am so excited”

Ji tai kamar ba zata iya jira har ta isa gida ta fada ba, dan haka ta dauko wayarta ta kira Mommy.

“Mommy Albishirinki”

“Goro”

“Wane irin goro za ki bani? Albishirin babba ne to all family”

ZABIN RAIDonde viven las historias. Descúbrelo ahora