“Shikenan but you should be very careful da Sadiq din nan”

Daddy Said.

“Thank you so much Dad In Sha Allah zan kula”

Mommy tana kallon Sadam da mamaki ta ce

“Ni kam wannan abun be min dadi ba, yo ina aka taba haka? Mutum yai kokarin hallakaka kuma kace kai ayi muku tsakani? Haba dai sai kace wanda ba shi da gata ko kuma be san abunda yake damunsa ba, ni wallahi har kotu na so aje dan aji dalilin daya saka yake neman ajalinka”

“Tunda yace a barshi mu daga masa kafa muga ni”

Daddy ya fada yana daga mata hannu.

“Ba dan komai yake son barin maganar ba sai dan kar Zinneera ta shiga ciki ko? Shine matsalar mutum ya fara soyayya da wrong person”

“Ba saboda ita bane Mommy, akwai abunda nake yi, kuma bana son maganar ta fita gari zan fi damuwa sosai idan mutane suka soma min jajen abunda ya faru, saman da tambayar sakin da nai mata haka kawai ba tare da wani dalili ba”

Tabe baki Mommy tai, ba dan idan ta sake wata maganar Daddy zai kwatse ta ba, da sam ba zata yarda a kyale Sadiq ya tafi hakan nan kawai ba tare da an musu tsakani ba, domin gani take kamar zai sake aikata wani abun ne against her beloved son.

ZINNEERA POV.

Kowa yana tsakar gida ana shan iska sakamakon zafin damina amman Zinneera tana daki ta dunkule da tsohon zanen atamfarta data bari gidan kamar ance dole sai ta rufa.
  Can dare ya fara yi Nabeel ya shigo gidan da sallama, Umma da Aleeya suka amsa masa domin suke kadai ba su yi bachi ba, Larai da Aliyu tuni suka lula wata duniyar. Dakinsa ya shiga ya cire rigarkinsa ya bar karamin wando ya fito tsakar gidan ya dibi ruwa ya shiga bandaki yai wanka ya fito ya sake komawa dakin ya saka short jean da vest ta fito ya nufo kitchen din dake tsakar gida ya dauki abincinsa ya kwantar da turmin daka ya zauna yana mika hannunsa ya dauko butar roba dake kusa da shi ya wanke hannunsa.

“Sadam dai ya kawo mata takardar saki dazu...!”

Ya bude tuwon zai ci kenan Umma ta fada masa wannan maganar, sai ya kasa kai hannunsa abaki kuma ya kasa cirewa daga cikin tuwon.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, abun har ya kai haka?”

“Ai ya wuce nan Nabeel, ransa fa take nema, so take ta kashe shi ta kwashe duniyar su gudu ita da Sadiq, to taya zai zauna da ita, yarinya ta zama yar ta'adda, muma ai dan ta zame mana dole ne”

“Amman kun bincike ta fadi cewar hakan take nufin ta aikata?”

“Sako ya turo mata a waya suraiya ta ganin, ta nan Allah ya tona asirinta...”

“Ko dai sheri ne Sadiq yai mata dan ya kashe mata aure? Amman wallahi Zinneera ba zata iya kashe wani ba Umma, kin fi kowa saninta”

“Ba a shaidun dan yau Nabeel, duk yadda kake tunanin mutum ya wuce nan”

Da sauri Nabeel ya tashi ya nufi dakinsu, yana shiga ya kai hannu ya fisge zanen data rufa da shi, sai tai zimbur ta tashi zaune idonta sun yi ja sun kumbura ga wasu kwalla na bin fuskarta.

“Zinneera da gaske kashe Sadam za ki yi?”

Kai ta girgiza masa sai ta kasa magana saboda kukan daya ci karfinta.

“Bude baki yi magana”

Ya daka mata tsawa.

“Aurena yace na kashe ba Sadam, sakon da Sadiq ya turo min Suraiya ta gani shine ta ce wai Sadam yake nufin na kashe, Wallahi ba zan iya kashe kowa ba....”

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now