Ta Karas tana kallon kawayen nata, ita kan dama tai gaba abun ta. Zaunawa Zinneera tai a gurin ta fara rera kukan abunda zai biyo baya tun yanzu. Suraiya take driving sai da ta fara sauke kawayen nata sannan ta wuce family house dinsu, a gaggauce tai fakin dan ta matsu ta shiga ciki ta fadawa Mommy abunda ta gani, tana rufe motar ta ciro wayar ta kira Sadam wayarta ta dade tana ringing sannan yai picking.

“Kazaure ka zo gida yanzu yanzu tana nemanka”

“Wani abun ne ya faru? ”

“Wani abun babba ma akan Zinneera”

Tana kawai nan ya kashe wayar, ita kuma ta nufi kofar shiga falonsu. A falo ta samu Mommy tare da mutane cikin falon kasancewar har yanzu akwai sauran yan bikin da basu koma ba.

“Mommy ta so ki ji yi sauri”

Ta fada tana nufar upstairs. Yadda Mommy ta ganta da kuma yadda taji furucin ya tabbatar mata da cewar abunda Suraiya take son fada ko yi mai muhimmanci ne, domin ba kasafai suke katse mata fira idan tana cikin mutane ba, sai idan wani abun ne mai muhimmanci. Tashi Mommy tai ta soma taka stairs din cikin takunta na manyan mata ta doshi dakinta inda Suraiya ta shiga.

“Har kun dawo”

Shine abunda Mommy ta tambaya daga shigarta dakin. Hannayenta Suraiya ta kama ta zauna da ita bakin gadon ita ta zauna, sai kuma ta fara tunanin yadda zata fadawa Mommy tasan abun ba zai mata dadi ba, amman babu wata mafita bayan fadin domin ita a ganinta rayuwar dan'uwanta ake nema.

“Mommy yanzu da muka je gidan Sadam, sai muka zauna falo sai Zinneera ta fito tace mana bari ta kawo mana abun tabawa, akan center table ta bar wayarta, ana ta kira bata kusa na dauka zan mika mata kenan sai kiran ya katse sako ya shigo....”

Haka ta zayyana wa Mommy abunda ya faru ciki har da kukan da Zinneera tai da kuma maganar da tai mata na cewar ba Sadam ake nufin ta kashe ba. A take hankalin Mommy ya tashi jikinta yai sanyi daman can idan abu ya shafi yayanta bata wasa da shi balle kuma akan Sadam dan lallenta.

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, amman Zinneera tana cikin hayyacinta kuwa?”

Kaminn Suraiya tace wani abu Sadam ya turo kofar dakin ya shigo sanye da manyan kaya wando da riga na farar shadda mai kyau da tsada. Tsaya yai karantar abunda ke fuskarsu bayan ya rufe kofar.

“Zauna”

Mommy ta nuna mishi kujerar gadonsa. Kujerar ya nufa ya zauna yana cigaba da kallonsu zuciyarsa cike da fargabar abunda zasu fada masa, a tunaninsa wani abun ne ya samu Zinneera. Yadda Suraiya ta fadawa Mommy haka Mommy ta fadawa Sadam fuskarta na nuna tsantsar damuwa da firgice.
Murmushi Sadam ya fara yi kamin murmushin ya zame masa dariya, dariya irin sosai din nan har sai ka dauka ko ya tabu. Mommy da Suraiya suka shiga kallon kallo.

“Sadam ka fahimci hakan abunda Mommy ta fada maka kuwa?”

Suraiya ta tambaya tana kallonsa da mamaki.

“Na fahimta mana, amman ku duk kun dauka da gaske? Taya Zinneera zata iya kasheni?”

“Zata iya Favorite idan har wani ya saka ta, kasan Zinneera mata da hankali Sadiq kuma makiyinka ne zai iya aikata komai”

“Na yarda amman ban da kisa Mommy Zinneera tana da tsoro ba zata iya aikata kisa ba”

“Yes Zinneera tana da tsoro da wani zai iya saka ta yi mata cilas kuma dole ta aikata”

“Ballantana ma ba cilas akai mata ba, domin yace ta bar maganar kudin zai samo”

Cewar Suraiya.

“Haba dai maybe ma ba daidai kike karanta sakon ba”

Sadam ya fada yana kokarin mikewa tsaye fuskarsa shimfide da bacin ran dake nuna be jidadin maganar ba.

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now