Sadiq din ya fada yana kokarin kwantar mata da hankali domin tuni ta soma kuka.
Ummi ta ce

“Amman da sauki a kansa ne kawai ya samu rauni sai hannu da kafa, kuma likitan yace yana son magana da wani jigonsa idan ya zo”

“To ina likitan yake?”

“Yana office dinsa ki tambayi nurse din da suke gurin zasu fada miki, amman wacece Zinneera? Ko sunanki ne?”

Da sauri Sadiq ya kalleta kamar yadda Mama take kallonta.

“Miyasa kika tambaye ni?”

“Sunanta naji yana kira lokacin dana kade shi, kuma yau da safe na zo na tararda wata budurwa tana kuka tana zaune a inda kike zaune, na mata magana amman bata min ba sai kawai ta fita tana kuka”

Sadiq ji yai kamar yai ma Ummi naushi daya ta nutse a cikin kasa saboda haushi, Mama ta kalleshi.

“Zinneera kuma? Yarinyar da aka kai jiya gidan mijinta?”

“Wacece ita?”

Ummi ta sake tambaya.

“Tsohuwar budurwarsa ce jiya tai aure, kuma shi da kansa ya fasa aurenta dan haka ban da dalilin damuwar kansa da ita ba”

“Ko ita ce ta zo nan?”

“Ya za ayi ta zo nan yarinyar da a kaiwa aure jiya jiya, sai dai idan wata ce dabam, ya ma xa ayi taji hadarin ko an kirata ne?”

“Aa ban kira kowa ba, wayar daukewa tai shiyasa kema ban kiraki sai yanzu daya farka na bashi wayata ya saka layinki”

“Bari na je gurin likitan”

Mama na fita Sadiq ya kalli Ummi yace.

“Amman ke dai baki da hankali wlh mahaukaciya ce ke ta karshe, wawuyar banza marar kan gado, ina ruwanki da ko wacece da zaki damu da ki sani? Shashasha kawai”

Dan murmushi tai na rashin jindadi

“Wani be taba fada min magana irin wannan ba, ni ba mahaukaciya ba ce, kawai ina damuwa da shiga rayuwar mutane ne, kuma ina da sakewa da shi, saboda ina kokarin na manta komai ina son na koma kamar da nai rayuwa kamar kowa, ban yi dan kaji haushi ba, kawai na damu ne dana sani, nasan zafin rabuwa da abun mai muhimmanci a rayuwar bawa, amman kai hakuri”

Mikewa tai tsaye ta aje masa katinta.

“Idan wani abu ya taso wanda ya kamata na sani na wannan kadewar da nai maka zaka iya sanar da ni, anjima kadan za a akawo maka breakfast za a kuma biya hospital bill”

Tana gama fadar hakan ta saka hannunta jaka ta dauko wayarsa ta aje masa ta nufi kofar fita. Da kallo ya bita yana mai mugun jin haushin abunda tai masa a gaban Mama har ta fice sannan yaja tsaki ya juya yana kallon wani wajen. Wata ta zo wacece ta xo? Zinneera ce? No ba ita ba bace ya xa ayi ace an kaita jiya ta zo yau, ya ma aza ayi ta san abunda ya same shi? Amman idan ba ita bace wacece?
Shine abunda ya tsaya masa a rai.

ZINNEERA POV.
Lokacin data fito harabar asibitin Napep din dake bakin gate ta samu ta shiga ta fada masa unguwar da zai kaita, sai a lokacin ta fara tunanin abunda ta aikata, idan Sadam ya farka kamin ta dawo me zata ce masa? Ko kuma idan mai gadin ya fada masa cewar ta fita tace ina taje? Aa ba wannan ba wannan abokin nasa ma zai iya fada masa ya ganta a asibiti da me zata wanke kanta? A daura nata aure jiya jiya ace yau ta fito?
   Idan Sadam ya fara zarginta fa? Ko kuma ya gane gaskiya, tun ba ayi nisa ba zata bata komai? Idan har asirinta ya tonu a yanzu ta rasa kowa kenan ciki har da Umma da Daddy domin ba zasu goyi bayanta ba.
   Kamin mai Napep din ya isa unguwar sama road har fuskarta ta soma kumbura saboda kuka, hankali be tashi ba sai da ta kasa gane idan da za a kaita, sai yawo suke kwana kwana  daker da sudin goshi ta gano gidan shi ma sai da ta buga gate din taga mai gadin ya fito ya bude mata sannan ta sallami nai Napep din ta shiga cikin gidan ta faduwar gaba. A hankali ta tura kofar falon ta shiga, sai kalle kalle take gabanta na dukan uku uku kamar zai fito, saurarawa tai ko zata ji tsotsinsa idan ya farka amma shiru hakan yasa ta karasa ta tura kofar dakin da yake kwance a hankali sai ta hango shi a yadda ta barshi. Ajiyar zuciya ta sauke ta karasa cikin dakin ta zauna baki gado tana kallonsa idonta cike da kwalla.
  Ji tai kamar ta fadi ta mutu, nauyin abunda ta aikata take ji, da kuma. Nauyin wanda zata aikata nan gaba, da kuma Nauyin biyu da yake kanta, na Sadam da Sadiq, taya zata rayuwar aure da Sadam? Miyasa ma ta aikata tun farko? Da ace Hajiya Karima ta bata kudin da yanzu duk bata shiga wannan halin ba.

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now