“Risina ki gaisheta....”

A razane Zinneera ta kalli Umma tana dafe da gefen cheek dinta.

“Risina na ce”

Umma ta sake a tsawace, da sauri Zinneera ta risina.

“Ina wuni”

Hajiya Karima ya daga kai ta kalli Umma.

“karki cilasta mata, kar ki saka ta fara tsanarki saboda ni, daman na zo ne kawai na duba lafiyarta, idan har zuwana yana haifarta matsala zan daina zuwa, daman ina da gab da komawa saboda mijina da yayan dana baro can suna da bukata ta”

Sai kuma ta kalli Zinneera wacce ke kuka.

“Zan nisanta da ke kamin na samu damar sake dawowa gareki”

Tana kaiwa nan ta mike tsaye ta dauki jakarta.

“Na gode sosai Safiya kin yi min duk yadda ake, Allah ya saka miki da alheri”

Da kwalla Hajiya Karima ta fita gidan, hakan ya saka jikin Umma yin sanyi Zinneera kuma tana durkushe a gurin tana kuka.

“Gaskiya Umma be kamata ki mareta ba, Zinneera tana cikin damuwa da yawa, kuma abunda wannan matar tai ko nice ba zan yi saurin yafewa ba balle kuma Zinneera”

Aleeya dake tsaye jikin kofar dakinsu ta fada cikin yanayin damuwa da abunda Umma tai. Umma ta nunata da yatsa.

“Daga ke har ita baku isa ku nuna min yadda zan yi ba, kuma abunda Zinneera take ba shi kyau ba kuma zan saka mata ido tana cin zarafin mahaifiyarta ba, idan ke da ita baku san darajar uwa ba, to ni na sani...”

Tana kaiwa nan ta shige dakinta a fusace, zuwa Aleeya tai ta kama Zinneera ta tashe tsaye tana share mata hawayenta.

“Yi hakuri Zinneera Wallahi ba a kyauta miki ba”

Hannunta taja har cikin dakin ta zaunar da ita.

“Amman kema kuma abunda kike be dace ba, ya kamata ki girmamata ko da ba za ki karbeta a matsayin mahaifiyarki ba”

Zinneera ta kalleta.

“Aleeya kin son Sadam ko?”

Aleeya ta kalleta baki a sake.

“Ban taba sonsa ba, ni yanzu ina son na cigaba da karatu na shiga jami'a kamar ke kamin na tsayarda wanda zan aura, kuma a tunani Sadam da wuri yake son aure, ni kuma ko candy ban yi ba, gaskiya ina bana son auren Sadam ko kadan”

Ta fada tana sauke ajiyar zuciya a hankali. Sai dai hakan be hana Zinneera fahimtar cewar Aleeya tana son Sadam ba. Sai ta kama hannun Zinneera.

“Sa ace Sadiq zai yanje neman aurenki da kin auri Sadam ko dan saboda Umma, domin ni dai ban shirya aurensa yanzu ba”

Yanayin yadda Aleeya take maganar ya karantar da Zinneera cewar Aleeya taji abunda tai, kuma ta sani sarai Aleeya na fadar hakan ne ba dan bata son Sadam ba, sai dan ita. Amman taya ita zata iya haka? Ta auri Sadam ba dan Allah ba? Ta raba shi da Aleeya dake son shi? Ta batawa Umma? Mommy da Daddy da suka riketa kamar yarsu ta watsa musu kasa a ido tabbas idan har ta yarda ta aikata haka ta bata komai. Amman kuma idan bata aikata ba ya Sadiq zai yi? Ina zai samu mafita? Tuna wannan yasa ta share hawayenta.

“Aleeya bana son Sadiq a yanzu, Sadam na ke so, kuma na san kinji, bana son kiyi min mummmunar... ”

“Na fahimce ki Zinneera, Wallahi babu komai a zuciyata sai son yan'uwana da farincikinsu, kin fini cancantar Sadam kuma na san shi ma yana son ki, kuma ni zan fahimtar da da Abbah ni da Umma zamu tsaya miki”

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now