Ya bata lokaci gurin shiryar kansa kamar wanda zai je wani buki ko wani taro, he just did it for Aleeya, so kawai yake yau ya burgeta, and ya shirya karbarta a matsayin mata, weather he loved her or not. Sai da ya shiga motarsa sai kuma ya dawo ya dauki kayan wasan na tennis ya saka a motarsa sannan ya dauki hanyar gidansu zuciyarsa nata nanata masa tambayar Sadiq ya kai Zinneera gida ko aa? Shi kuma yaki bata hadin kai balle har ta saka shi a damuwa.
   He didn't arrive in time ko da ya isa Daddy ya fita, Mommy ce kawai a gidan sai su Suraiya da Siyama, they are both in parlor suna ta tattauna yadda taron jiya ya gudana.

“Good Morning Sweet Mommy”

“Morning Favorite”

Mommy ta fada idonta sanye da farin gilashi tana kallonsa. Siyama ta fara mika masa gaisuwa tana cin cucumber kamin Suraiya.

“Morning Mommy's Favorite looking cute”

“Thank you”

Ya fada yana kara kallon kanshi, blue t-shirt ce a jikinsa, sai bakin jeans da blue facing cap da blue shoes wandnda ya shigo da su har cikin falon.

“Ina Aleeya?”

“Bachi take”

Siyama ta shi amsa tana mika masa cucumber. Karba yai ya kai a baki sannan ya mike tsaye ya nufi dakin da yake zaton tana ciki wato dakin Suraiya. A hankali ya tura kofar dakin ya leka sai yaga wayan bata ciki.

“Tana dakina”

Siyama ta fada. Sai ya nufi dakin ya leka ya hangota kwance tana ta sharar bachinta, chubby cheeks dinta sai shining suke. Janyo kofar yai a hankali ya rufe ya dawo gurinsu ya zauna.

“Congratulations Favorite Allah yasa albarka kuma yasa maka hannu a ciki kuma ya hada da abokan aiki na gari”

“Amin Mommy thank you”

“And i pray Allah yasa wannan zabin da mahaifinka yai maka ya zama alheri a gareka, Allah ya hada kanku ya kawarda fitini da shaidan a tsakaninku”

“Amin Mommy”

Ya sake amsawa da Amin shi da Siyama Suraiya kam bata ce komai ba, kawai dai bata son Sadam ya auri Aleeya ba dan komai ba sai dan tasan ba zabinsa bace and Aleeya bata daga cikin irin mata da Sadam yake so domin ita tana da jiki kuma ba fara ce tas kamar yadda yake yawan zana kalar matar da yake son ya aura ba, afterall wulakancin da Sadiq yai masa yasa ta tana son ya auri Zinneera ko dan Sadiq din, sai dai babu yadda zatai tunda yai accepting and now Mommy support him. Tashi tai ta nufi dakinta tana fadin

“Bari naje na shirya akwai inda nake son zuwa”

Da kallo ya bita sai da ta shige sannan ya ciro wayarsa ya aljuhu ya shiga online ya duba messages, daga masu masa ya gajiyar jiya sai masu ce masa idan za a dauki ma'aikata suna so, sai masu taya shi murna da dora hotonsa a status. He just feel bad tunawa da alkawarin da yai ma Sadiq na sama masa aikin a kamfaninsu akaiki tare, but akan Zinneera komai ya tarwatse ciki har da abotarsu.

After like one hour ya tashi ya nufi hanyar Garden, ba Garden din ya nufa kai tsaye ba, wani fili na gurin ya nufa inda aka gyara masa yana wasansa tennis dinsa kusa da gurin da Daddy ya aje dokin nadin sarautar da aka bashi lokacin da aka nadashi a matsayin kogunan sokoto, ba dan kuma ya gaji sarautar ba sai dan yana dan siyasa kuma yana da rufin asiri.

Baya jindadi yi kadai, lokacin da yake waje yana zuwa gidan da ake buga wasan ne ya buga, a nan gida kuma ya taba bugawa da Siyama, and now shi kadai yake abunsa sai duk yaji babu dadi bayan be taba jin wasar ta gundureshi ba. Jikinsa ne ya bashi ana kallonsa hakan yasa yai saurin waiga idonuwansa sukai arba da Aleeya tana tsaye rungume da hannayenta fuskarta dauke da murmushi.

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now