"Zauna"

Sadiq ya fada yana nuna mata kujerar da Nabeel ya tashi akai, shi dai kam yana matukar tausayin Hajiya Karima, domin yasan kowa be wuce kaddara ba, a matsayinta na uwa zata fi su jin zafi da bakinciki abunda ta aikata.

"Wata kila ba zata so ganina kusa da ita ba"

Ta fada tana kallon fuskar Zinneera idonta cike da kwalla.

"Saboda? Ke ba mahaifiyarta ba ce? Idan baki sake jiki kin nuna mata so a yanzu ba, sai yaushe kike so ko kike tunanin zata fahimce ki?"

Bata sake cewa komai ba, har Zinneera ta fara motsawa alamar zata farka, sosai gaban Hajiya Karima yake faduwa tasan ita ce uwa Zinneera ya amman tana fargabar suyi ido hudu da ita. A hankali Zinneera ta bude idonta, sai ta saka hannun da aka saka mata drip din ta murza idonta.

"Sannu"

Hajiya Karima ta fada, sai Zinneera ta bude idon da kyau tai mata kuri da ido kamar bata taba ganinta.

"Sannu"

Wannan karon Sadiq ne yai magana, shi ma din kallonsa tai, kamin ta sake maida dubanta gurin Hajiya Karima.

"Miya kawo ki nan?"

"Ni na fada mata baki da lafiya"

Sadiq ya fada. Sai ta dauke kanta ta maida gurin kofar shigowa tana kallon kofar kamar bata damu ba.

"Bari na kira likita ance idan kin farka a kira likita"

Sadiq na fadar hakan ya juya ya fita da sauri, sai Hajiya Karima ta mike tsaye ta kara matsowa kusa da Zinneera.

"Kina da bukatar wani abu?"

Kallonta Zinneera tai.

"Dan Allah da gaske tambaya kike ina da bukatar wani abu? Miyasa baki tambaye ni lokacin da nafi bukatar komai na ki ba? Miyasa baki zauna da ni a lokacin da nake da wata takwas kin yi min duk abunda na ke bukata ba? Baki damu da irin rayuwar da zan yi ba kika yi tafiyarki?"

Maganar take tana hawaye, yayinda Hajiya Karima kuma take kuka.

"Da baki zo ba, da Umma batai ciwo ba, da ban ji na tsani gidan mu ba, da ban ji ina son kebewa ni kadai ba, da ba a kawo ni asibitin ba, da baki dawo ba da har yanzu ban san cewa Umma ba ita ta haife ni ba, miyasa kika dawo? Baki san rashin dawowarki ya fi dawowarki alheri a gurina ba? Kin kara ruguza rayuwata a yanzu, kin tarwatsa min farinciki ni da dan'uwana a tunaninki dawowarki zai saka mu so ki ne? Bayan ke kin kimu kin tafi kin bar mu?"

"Zinneera miye haka? Mahaifiyarki ce fa"

Sadiq wanda ya shigo a yanzu ya fada, domin ya ji kalmomin dake fita daga bakin Zinneera, sai da ya maida kofar ya rufe ya karaso inda gadon Zinneera wacce ke kwance tana hawaye. Tashi tai zaune ta kalleshi.

"Miyasa baka fada mata cewar mahaifiyata ce karta tafi ta bar ni ba? Bata damu da halin da zan shiga ni da dan'uwana ba ta tafi ta bar mu, wace mace zata rainemu? A wani yanayi zamu tashi? Zamu samu tarbiya ko aa duk hakan be dame ta ba"

"Amman bakisan dalilinta ba, kuma dan'adam azijine, ko ba komai kuma mahaifiyarki ce dole ki yi mata biyayya, dan haka ki yi mata uzuri Zinneera"

"Nima kai min uzuri Sadiq, amman wannan matar ba mahaifiyata bace, kalmar mahaifiya tana da girma, ma'anarta kuma tana da fadi da nauyi, akwai tausayi da jinkai da damuwa da fargaba da tsoro a idon mahaifiya da zuciyarta, na abunda zai samu danta ko yarta, Umma ce mahaifiyata ita ce kadai take dauka kalmar mahaifiya, matar da ta fifita ni akan yar cikinta, matar da take damuwa idan ban ci ba, matar da take nemana idan na dade ban dawo gida ba, ke kam uwace kawai kamar sauran uwaye da ake biyansu su haifi yaran kawai su yi tafiyarsu"

ZABIN RAIМесто, где живут истории. Откройте их для себя