HAJIYA KARIMA

Depuis le début
                                    

Umma tayi murmushi.

“Ba zance ba Zinneera hakan ma zai nuna min cewar kin yi hankali har kin fara sanin ciwon kanki da yi magana mai muhimmanci akan aurenki”

“Zan yi magana da shi anjima idan ya zo”

“Hakan yayi kyau Allah yai miki albarka, ni kuma zan daɗa magana da mahaifinki, ki kwantar da hankalinki”

Ta gyada kai tana sauke numfashi a hankali. Ido Umma ta kura mata tana mata irin kallon nan na tausayi da kauna dake tsakanin uws da diya, Zinneera ta natsu sosai fiye da tunaninta sai kwana biyun nan ta saka kanta cikin damuwa sosai tun daga ranar da Abbah ya tuntubi Sadiq da zancen auren da yace sai a watan mauludi, gashi watan ya kare har wani ya shigo babu wani labari. A bangare daya kuma tana tunanin halin da ita da Zinneera zadu samu kansu idan har abunda aka shekara ashirin da biyu ana boyewa.

   Misalin takwas Aleeya tai wanka ta kure adaka domin Abbah ya ce takwas da rabi Sadam zai zo su gaisa da Aleeya. Wannan karon Zinneera sai tsokanarta take.

“Aleeya ba ko kunya har da yin kwalliya”

Aleeya ta sakar mata harara.

“Oh ke da kike kwaliya idan Sadiq zai zo da ba'a ce miki komai ba sai ni?”

“Ai ni daman can ya sanni kamin nai kwalliya”

“Ni kuma aka ce miki ba san ni ba? Shi da kansa yace yana sona ai”

Zinneera tasa dariya.

“Lallai Aleeya baki da kunya”

“Ke wallahi yanzu an daina kunya, balle irin Sadam mai kyau”

Wannan karon sosai Zinneera take dariya.

“Shegiya, daman can kin ga abunda ke miki kenan”

“Haba dai Zinneera ai yana da kyau gaskiya”

Shigowar Umma ne yasa Zinneera hade maganar da zatai.

“Tashi kije Sadiq na kiranki”

“Ina kika ganshi?”

“Yaro ya aiko, Aleeya kwaliyar ce ake”

Umma ta karasa tana kallon Aleeya da murmushi, sai Aleeya ta rufe fuskarta Zinneera ta tashi tana dariya ta dauki hijabinta ta saka sannan ta dauki turaren Aleeya ta fesa, da sauri Aleeya ta fisge turarenta.

“Eh lallai sannu sai ki boye naki ki feshe nawa, ai kama baki da nasiha”

Gwalo Zinneera tai mata.

“Na ji dai amaryar Sadam ba kunya ba nasiha”

“Eh din”

Ta murguda mata baki. Da far'ar ta fito daga gida, kamar yadda far'arta ta dada karuwa lokacin da idonta sukai arba da masoyinta, yayi kyau matuka yana sanye cikin wata farar shadda sai kamshin turare yake kamar ango. Kallonta yake da murmushi har ta karaso ta jingina jikin motarsa tana kallonsa.

“You look very calm and quiet, kwanan biyu kin zama yadda na ke sonki”

“Baka tunanin akwai abunda ta kamata ya dame ni ne Sadiq?”

“Kamar na me? Na san dai baki cik tunani ba, irin tunanin wani abun ya dame ki ba, ko dai Umma ce tace kin yi wani abu ba daidai ba?”

Ya fada yana murmushi kamin ya mika mata ledar dake hannunsa.

“Ga yogurt na siyo miki na san kina so”

“Na gode”

Ta fada bayan ta karba.

ZABIN RAIOù les histoires vivent. Découvrez maintenant