Ya dafe kansa.

“No Doctor ba zaki gane ba, nifa ma tsani zuwa meeting dauko wacan sa hannu a nan kula da wannan tura wannan karbi wannan kana da meeting a kaza karka rasa kaza dole a samo kaza, zuba hannun jari this and that i completely hate it”

“Favorite...”

Mommy ta kira shi a hankali sai ya dago ya kalleta.

“Mahaifinka yana son ka a kamfanin nan please don't disappointed him, ba zai hana ka aikin da kake so ba, na masa magana yace min idan aikinka ya fito zaka iya zuwa office idan ka kawo sai kaje kamfani he just wanted you to be part of it, kasan yana da yayan yan'uwa amman ya zabi ka kula masa da wannan you should atleast say yes to him, but idan baka so i will talk to him sai mu samu wata mafitar, amman ku din nan ku uku ku kenan Allah ya bashi, kuma kai ne namiji idan baka masa ba wa zai masa?”

Yai shiru alamar tunani kamin yaja wani dogon numfashi ya sauke.

“No zan yi domin ku, i promise”

“Thank you Son Allah maka albarka”

Ya tashi tsaye sai Suraiya ta kira.

“Mr Kazaure”

Juyowa yai ya kalleta daman ta kan kirashi haka idan tsokanarta ta motsa.

“Mommy tace na samu in-law”

Shafa kansa yai yana dariya.

“Har kin tuna min ya kamata na tambayi Daddy inda zamu je yau, ina son na hadu da ita as my cousin”

“Who's that lucky girl?”

Suraiya ta tambaya yana wara ido.

“You shouldn't ask that, kawai ki jira ki gani”

Ta ware hannayenta irin bata fahimta ba, tana kallon Mommy bakinta sake. Mommy ta daga mata kafada irim itama bata sani ba.

“Kaji Mommy yanzu kamin na shigo ba gulmana kuke ba...”

Sadam ya fada yana dariya, sai duk suka sa dariya, shi ma ya wuce yana dariyar. Suraiya ta dawo kusa da Mommy

“Dan Allah wacece Mommy?”

“Zinneera...”

Suraiya ta zaro ido tare da rufe baki.

“Amman Mommy ba tana da miji ba? Ko an fasa da wacan ne?”

“Ba a fasa ba, shi kanshi be san an mata engaged ba, and bana son fada masa Wallahi saboda zai ji ba dadi, kuma kin san idan Daddy ku yaji zai masa fada ne yace ya kyaleta tana da miji balle ma yar yar'uwarsa ce kin san kumayadda yake jin yan uwansa”

“So sad kuma da alama yana son ta sosai Wallahi”

Suraiya ta fada cikin yanayin damuwa.

“Yana son kan, yai ta bani labarinta dazun nan na fada masa cewar yar'uwarsa ce kin ga yadda yai ta farinciki kamar zai hade ni”

“Amman Mommy ai kara a fada masa da wuri kar yai zurfi cikin sonta at the end abun ya taba shi”

Mommy tai shiru bata sake cewa komai ba,sai dai fuskarsa na nuna tsantsar damuwar dake ranta, domin ko kadan bata son damuwar yaranta balle kuma Sadam da take jinsa har kasan zuciyarta...

Daya fita Part din Mommy komawa gurin Daddy yana masa godiyar kamfani, Daddy yayi mamaki ganin farincikinsa bayan dazu ko da ya fita yana cikin damuwar dake nuna baya son kamfanin.

“Ko dai kun hada kai da Mommynka ne amin zagon kasa na san dazun baka farinciki da kamfanin nan ai...”

Daddy ya fada yana kallonsa ta saman gilashin dake idonsa, sai Sadam yasa dariya.

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now