55

2.2K 145 0
                                    

KALLON KITSE

Inna ta katse shi, ko sunyi arba'in babu inda zasu je, sai 'yar nan tayi kwari.
Yace haba inna kalleta fa tamkar 'yar wata biyu? Uwani tace "uncle bamuyi arba'in ba fa, ka manta ne?
Inna kam bata kuma cewa komai ba, ta gama shirya takwararta, ta mika ma jafar, bayan ta gama mata rawa da 'yar wakarsu ta manya, a ranta tana maijin dadi da ganin jinin jafar.
Ta fita tana fadin, bari na gani ko indo ta gama abinci ta zubo maka." yace toh"
dama ya kosa inna ta fita, ya koma bakin gadon kusa da uwani yace, babyna kalli 'yarki mai kyau kina sonta?
Kunyace ta kamata tace, kai uncle 'yar fari ce fa?
Dariya ma ta bashi, yasa hannu yana shafo dokin wuyanta, tare da fadin kina yin arba'in zaki tare fa? Tace amma ai mun zaga dangi ko? Yace zanko yarda? Kinsan fa bani so a kwaso mata iska." tace haba uncle." ya amshi man data ke shafawa yana fadin, "kawo na shafa miki." a cinyar shi ya kwantar da yarinyar, sannan ya kwance zanin data yi daurin kirji dashi, kirjinta ya tsaya kallo, wanda yake tsaye kyam, sha'awarta ya matsa mishi, ta ganeshi don haka taja zaninta tare da fadin jego fa nake uncle." cikin sigar shagwaba take maganar.
Yace, toh me nace zan maki? Zan dai dan tsotsekine kurum." kafin tace komai ya soma sumbatarta, sai ga inna tana fadin auta akawo maka, ko ko can falon za....." tayi sororo ta na kallonshi, ya soma 'yar dariya yana fadin, am me kika ce? Uwani kunya ta hanata magana, ta sunkuyar da kai. Inna ta soma fada, "me zan gani haka auta? Da wannan 'yar labubuwar yarinyar, kofa arba'in bata yi ba, wai meyasa baka da hakuri ne? Toh tashi daganan."
yace, me nayi ne inna? Nifa ba wani abu zan mata ba." inna tace taso dai, ke kuma in kina biye mashi ke zai kai ki ya baro, ni 'yar nake ji."
ta juya ta fita, uwani tace uncle kana bani kunya gaban mutane."
ya manna 'yar shi a kirji ya fita.
Kwanan uncle biyu, ya tafi, saboda yanda inna tasa mishi ido tace, sam kada ya matsa musu da fitinarshi, haka suka ci gaba da samun kula wajen inna, har sukayi arba'in, suka soma zaga dangi.
Daga gurin su shatu suka soma, sunyi kwanakin su, sannan suka dawo gidan zainab da salaha ma sun sha yawonsu. Ranar wata laraba data zo dai-dai da watan su biyu da kwana shidda, da yamma inna ta fita nan cikin unguwa don yin gaisuwa. Uwani tana kwance kan kujera a falo, baby zahra ce kwance kan ruwan cikinta.
Sunyi wanka da kwalliya, sai kamshi suke yi, fuskarta tana kallon T.v, amma zuciyarta tana ga tunanin uncle dinta, don bacci ya soma dibanta. Sam bata ji shigowarshi ba, sai da taji an cire yarinyar daga jikinta, cikin sauri ta ashi a tsorace kwarai. Jafar ya saka dariya. Tayi ajiyar zuciya, sannan ta dubeshi da murmushi, uncle sannu da zuwa." yace, yauwa," yazauna yana fadin ina inna? Tace ta fita gaisuwa."
ya zauna yana tashin yarinyar, tashi zahra baby, ga dadynki ya iso." uwani ta fita tana dariya, don kawo mishi abinci. Inna ta dawo ta same su, nan ta zauna cike da fara'a, "autana ne ya iso? Yace, "nine inna." suka gaisa.
Tun a ranar ya soma damun inna da son tarewar matarsa, za a mata jerenta a gidan daya saya na nan, amma zai tafi dasu kaduna. Inna tace a'a bazan bada 'yata ba, kaje da ita can ku hadu kaida matarka ku gasamin ita. Yace haba inna ya zan gasa Aisha da kaina? Kuma ai matar da kike magana tuni mun rabu."
tace, zan da yi shawara in tace zata toh shikenan."
bayan sallar isha'i ta iske shi a dakinsa tana dauke da baby zahra a kafadarta, ya waya ne, sai da ta shigo falon ya zo rungumesu ga ba daya. Bayan ya gama wayar yace, "aisha kinji inna tace, saikin yarda sannan zaki tare ko?
Ta daga kai, ya kara manneta a jikinshi, don Allah kice mata zaki je, ina tsananin bukatarku kusa dani. Taba wuyana kiji, ban rame ba? Tayi dariya, "uncle rama anan? Dubi yanda ka kara kyau da burgewa? Ya dago fuskarta yana kallonta yanzu harna kaiki? Ya soma shafarta.
Jikinta yayi laushi, bambacin kadan ne dana baby zahra, ya dubeta dama in mace ta haihu haka jikinta yake kara zama? Tace "kai zan tambaya likita.
Yayi 'yar dariya, "toh kila tawa matar ce haka." a ranta kuwa cewa take yi sirrin nan yana ga inna data hada mata sabulu na musamman dan gyaran jikinta, duk mace data juri wanka da sabulunin lallai zata kasance mai tsanani laushin jiki, ga mai son sani zai kira number uwani don jin karin bayani.
Yasa harshe ya lashi lebenta, "tunanin me kikeyi ne baby? Tace, "ga babynka nan a hannunka." yaso ya huta da ita amma taki, saboda wai yanzu ba da bace, uncle ka ga...." ya katseta ban gane ba."
saboda zahra ko?
Ya kwantar da ita ya jawo uwani jikinshi, "ki bani hakkina kawai, ke kin san na damu." ya rufe kofar sannan ya dauketa tamkar yadda zai dauki bab zahra, shafal batada nauyi, yayi bed-room da ita.
Sha daya ta wuce sanda ta fito zuwa daki, shikam ji yayi tamkar yau ya dauketa budurwa. A fili yake fadin kai macen sunna daban take, dan duk sanda ya kusanci uwani, yakan jin nishadi na daban, wanda duk matan bariki baya ji game dasu. Yabar komai na tafiya.

yabar komai na tafiyan su zuwa sati mai zuwa zaizo ya tafi dasu.
Su hafsat da fa'iza duk sun kara yin sallama dasu, harda lawisa, akwai wasu sirrika namu na mata da inna ta hada mata, duk da tanajin nauyinta, amma tayi kamar bata kula da hakanba, bayani takema uwani cikin fahimta dalla-dalla.
Kayan setine tun daga sabulun wanka zuwa lalle, banda kaloli nasha, "cikin tsari na addini zakiyi amfani dashi, sannan in komai ya kammala saiki tsabtace jikinki, sannan kiyi nafila tare da rokon Allah yasa dukkan abinda kikayi amfani dashi ubangiji ya amsa."
inna taci gaba da cewa kidaina jin nauyina uwani, inban gaya miki ba wa zai gaya miki? Nasan halin mijinki dan rashin hakuri, sannan ciwon 'ya mace na 'ya mace ne.
Tasha gyara gurin inna kafin ya iso, inna taja mishi kunne kan ya kula da uwani, domin amana ta bashi, yace, kada ki damu inna zaki sha mamakina." tace "shikenan auta, Allah ya saukeku lafiya.
A daki kam cema uwani tayi, "inkinji yaya kimin waya, zan zo in daukeki ki dawo." tace toh. Sosai inna taja mishi kunne.
Sun iso kaduna duhun mangariba ya shigo. Rayuwa suke mai dadi da burgewa, daya dawo gida zai samu sunyi wanka da girki mai dadi suna jiranshi, daya dawo zai hadasu ya manna a kirjinshi, cikin farin ciki su ci, su sha, su shiga soyewa, jafar mabukaci ne sosai, shida kanshi yasan Aisha tana kokari dashi, shi kuma yana samu nitsuwa da ita, jinta yake kullum tafi jiya, wani sonta mai tsanani ne yake shigarsa, haka nan yana mutuwar son 'yar sa mai kyau, mai kama dashi.
Gaskiya suna soyewa, yanzu ya gama yarda cewa, uwani tana sonshi, don haka bai cika harkar mata ba, sai dai wanda baza a rasa ba, game da giya kuwa yana sha sau daya a rana, sannan in zai shata kamin yazo gidane zai sha, sannan ya saka sweet a bakinshi, tare da cingam, duk da cewa uwani tana jin tsami gurin kissing dinsa, sai dai ta rasa gane na menene.
Yawanci lokaci tana tsamanin tsamin na sweet da yake sha ne, dan ba kala daya yake shaba, bare ta gane, sai dai zuciyarta na zargin wani abu.
Jamila zaune kan kujera hankalinta a matukar tashe, tun sanda labari ya zo mata wai jafar ya komo da matarshi ta mike, ita jafar zai yaudara, yayi mata alkawarin aure, amma ya karya? Ta koma ita kadai tana cewa zan bawa jafar mamaki, ni jamila saina koma cikin rayuwarshi, saina ruguza masa dukkan farin cikin shi, zai sha mamakina." ta soma sheka dariya, "zai san yayi da 'ya".
Uwani ta fito kicin da sauri, ta gama shirya abinci, sannan tayo wanka, ta kamo zarah dake guje-gujenta, yarinya 'yar wata tara amma tana zuwa ko ina, ga son suutu ta iya kiran uncle. Haka take cema jafar, saboda taji mamanta tana cewa uncle, sannan zata ce "mummy" da sauran kananan surutai. Taje tayo mata wanka, ta sheka mata kwalliya, sannan ta gyara mata fakin din gashinta, dama gata da gashi mai kyau da tsawo.
Wayarta ta soma ringing, kafin ta tashi har zahra ta ruga ta dauko.
Tana gwarancin fadin "uncle mummy. Uwani ta saka dariya, lallai yarinyar nan, wato har kinsan lokacin da uncle yake kira ko? Ta amsa saita ga ashe inna ce, da murna ta ce, "inna ina yini? Tace "lafiya lau uwanina, naga yau baki kirani ba, shiyasa nace bari in kiraki." tace wallahi inna kudi na ne ya kare a cikin wayar, sai dai nasan in uncle zai shigo zai shigo min da kati." inna ta ce toh kuna lafiya ina takwarata? Tace gata nan." takamota zo kiji inna." dama akwaita da sauri cafke abu, tayi caraf tace inna...inna." uwani ta manna mata waya a kunne, dama ko yaushe sukayi waya sai anba zahra tayi wannan shirmen, tunda suka zo kaduna basu taba zuwa birnin kebbi ba, sai dai jafar idan ya samu dama zai leka ya dawo. Inna tace uwani badai wata damuwa ko? Tace babu komai inna muna lafiya."
ji tayi an rungumeta ta baya, ta dubeshi tare da yin ajiyar zuciya, inna tace "toh sai anjima." jafar yace inna ni baki kirani ba." ya amshi wayar suna gaisawa, uwani na manne jikinshi. Rayuwa anayinta a gidan nan mai ban sha'awa.
Uwani kwance kan doguwar kujera tana kallon fim tashar MBC 2 Taji ana kwankwasa mata kofa, ta tashi ta bude, wata mace ta gani 'yar doguwa fara, irin wanda farin ne ya rufa musu asiri, kan nan taf! Da gashin kanti, kumbuna zaka-zaka tamkar mai cin kare, ta dubeta cikin yatsina fuska, "me gidan yana ciki?
Uwani ta dubeta, "me gidan kuma?
Tace, "malama bawai inason tambaya bane, ina son jine, yana nan? Tace menene dalilinki nason ganinshi?
Taja tsaki tareda bi ta gefen uwani, ta shige ciki.
Sororo uwani ta tsaya tana kallon ikon Allah, wannan wace mace ce da kokari harta zo mata gida, ta shige kai tsaye, kuma wai mijinta take nema, ko ko matarshi ce wadda yake fadin ya saka?
Uwani ta bita ciki, abin al'ajabi kai tsaye dakinshi ta shiga, kenan tasan gidan? Ta tambayi kanta.
Jamila kam kaya ta cire ta shiga toilet din uncle, tayo wanka, sannan tazo ta shige kitching, uwani kam daki ta shige tare da kulle kofa, kuka ta shiga rerawa cike da takaici, batasan lokacin da jamila tabar gidan ba, ko bude kofa bata yiba bare aje ga batun girki,

KALLON KITSEWhere stories live. Discover now