17

1.9K 143 0
                                    

KALLON KITSE PRT (17)

Haba yaya ya zakice haka? Kinsan yanda nake son marliya kuwa? Wallahi bazanyi aure ba in har kuka hanani aure marliya.
Salaha tayi tsaki, mts! Kai har so ka sani? Bayan ance ma mutanen nan ba 'yan mutunci bane?. Kuka ya saki, baiji bai gani, nan da nan jikinsu yayi sanyi, tare suka hada baki, "kai hakuri mun daina, kaje ka aurenta, amma ashe soja na kuka? Ko ko shagwaba ce ta tashi? Toh inna bata nan, dan haka akama kai".
Ya kirne fuska, "ni wallahi dama nine babba, komai sai a danne ni ace nine karami.
"eh mana ko kai ba karami bane? Amma ai sai taurin kai da Allah yayi ma, toh Allah yasa ayi lafiya.
Ya washe baki, nagode dan Allah karku fadawa inna.
"um bazamu fada ba, amma kasani komai daren-dadewa gaskiy zata bayyana, mudai 'yan kallo ne"
nagode bari inje in sayo muku abinci tunda kunce yunwa kukeji.
"daka kyauta, ka siyo mana amala ma ya ishemu, da sauri ya fice, su kuwa sai tausaya masa sukeyi.
Haka akata shirye-shiryen aure, har gashi gobe daurin aure, a ranar uwani suka iso tare da iyayensu zainab. Washe gari aka daura aure, har a wannan rana basusa ido kan amaryarsu ba, saida yamma akace, a shirya aje akwai wani wasa da za ayi.
Da suka isa ko kallo basu ishi mutane ba, suka sami wuri suka zauna, dan sun san baza a basuba.
Suna zaune akazo aka wuce da amarya, abun mamaki basu yadda da hakanba, har saida suka kalla an bata fili tana wata irin rawa kamar maciji, shikuwa gogan yanata tare ta dan karta fadi, wai inta fadi za'a ci shi tara.
Iya kuwa su goggo ansha kallo, kayan abinci saidai sukaga an wuce dashi, badai abasu ba, harma sun saba, dan haka zasu zo da ruwan shansu a mota, tun suna fadawa jafaru, har suka sa idonsu ayima su tafi gida, dan sun gaji. Su uwani kam abun yabasu sha'awa, itada su hafsat, tunda su ina ruwansu, basu san maabunda ke faruwa ba, dan alokacin sunada shekaru goma sha daya da sauransu.
Sai karfe sha biyu suka bar wurin, suka koma gida, kowa da abinda ke ransa. Suna sauka suka soma bayanin abinda ke cikin zuciyarsu, goggo tace "anya yarinyar nan bata girme ma jafar ba? Zainab tace, "kedai bari goggo, ai wannan ba yarinya bace, daga ganinta takai shekara arba'in, wallahi tayi sa'a da salaha.
Salaha tace, "anya bata girme ni ba?.
Suka kwashe da dariya, tun abun na basu haushi, har ya soma basu dariya, wannan dare basu kwanta ba sai hira sukeyi, dan haka yasa sukai kusan makara.
Tun da safe suka shirya, suna jiran mota, dan mota uku ta wuce irin su goggo da jirgi zasu, dansu zasu karbi amaryarsu.
Da kyar da sudin goshi aka basu ita, shima saida sukace, sukam in baza a basu ba zasu wuce, dan bazasu kara kwana a wannan garin ba.
Karfe biyar ta wuce suka isa sokoto, dama mutane na jiransu, dan haka karfe bakwai suna gidan inna.
Abunda inna ta gani a idon yarinyar nan jikinta yayi sanyi, dan tasan ba karamin gamo danta yayi ba.
Ajiyar zuciya ta rinkayi, dan abun ya tayar mata da hankali matuka, duk da ta nemi ta boye da muwarta, amma saida 'ya'yanta suka gane, janta sukayi zuwa shashen indo, batasan sanda hawaye suka fito mataba, zainab ce ta gani itama saita soma kukan.
Salaha itake bada hakuri.
Inna tace, "shine baku bugo kuka fadamin ba?. Sai a lokacin suka kwashe komai suka fada mata. "toh shikenan tunda haka ya zabarwa kansa, Allah ya kare shi daga sharrinsu, ya kuma bada zuri'a daiyiba."
Amin, suka ce baki dayansu. A lokacin sukaji sallamar jafar din, sai sukai sauri sakin fuskarsu, ya shigo ya isa, ya rungume inna yace, "inna nayi missing dinki.". Ta tallabo fuskarsa, "kana cin abinci kuwa auta?.
Ya hadiye miyau da karfi yace, "rabona da abinci inna, har na manta.
"haba jafar so kake kayiwa kanka lahani?
Salaha ma za dauko abinci, ga makulli, zaki ganshi na shiryashi daban-daban, na kune nace a ajeshi daban, inasu uwani? Na gansu yanzu suka iso, Allah na gode maka, Allah shiyi muku albarka.
"Amin. Suka amsa baki dayansu.
Haka amarya ta tare a wani gida na Alh. Yunusa, daya ce a ara masa su dan zauna, da yake guest house ne, komai akwai aciki, dan haka basu da matsala.
Da daddare akayi dinner inka gansu wurin sun sha kwalliya da dinkin wani bakin lace, da zainab ta dinka musu, su uku tace, sune 'yan matan dake tasowa, sunyi kyau sosai sai kace 'yan uku , duk inda suke toh tare zaka gansu, dama gasu gwanayen rawa, sunyi rawa sosai, kamar bazasu dainaba. Ali jita aka kira dan haka ranan ba karamin naira aka saki ba, ba a tashiba, sai karfe dayan dare.
Amarya na daki, abokai sukayi ta barkwanci, basu tafi ba saida wajajen karfe biyun dare.
Amarya kuma ko digon kwalla babu a idonta, tana tare da jamila tace, "mikomin hodar nan, dan anzo da ita." ta mike ta nufi bandaki tasa dan ruwa aciki, sannan ta matsa, wai inji bokan laya ce, zaijita tamkar wadda ba a taba saduwa da itaba, wato budurwa daga leda, tayi murmushi tace "jafar na kamaka sai abunda nace shine zai zama dole, dole in rabaka da duk wanda zai rabani dakai." ta fito tace da jamila, ta wuce hakan zasu hadu gobe .

KALLON KITSEWhere stories live. Discover now