6

2.8K 184 0
                                    

KALLON KITSE PRT<<<<>(6)

yadan saki ransa suna gaisawa, bashir ya dubeshi yace, yaya dai?
"mts...
Mtssss, wannan wanne irin abune kayi mana tsaki?
"wallahi yarinyar nan ce da nake baku labari,
shagwabarta sai karuwa takeyi, ni wallahi duk ta fice min a rai.
Safwan yace toh me ruwanka kaima da ita?
"ka gane yarinyar kazamiyace, sannan sam! Inna bata so taga haka, idonta ya rufe da son yariyar dayawa.
Toh kodai kishinta kakeyi, ta maye maka wurin, ai kaima haka kasan haka kake kai da har yanzu baka daina rumgume inna ba, saikace karamin yaro? Inji bashir.
"kasan Allah bata isa inyi kishi da itaba, danni nasan na fita a gun inna. Safwan ya girgiza kai yace "shiyasa a koda yaushe in ankiraka yaro ka rika jin haushi, yanzu dai kishin yarinyar ka keyi?.
Duka ya kaiwa safwan, suna dariya, "dan Allah kudaina fadan haka, kar wani yaji yayi min dariya.
Ahaka suke tafiya har suka kai inda zasu, wai gun budurwar safwan za a, sunyi sallama cike da yanga harira ta fito, ta gaidasu. Bashir kadai ya amsa jafar kam ko kallo bata ishe shiba, saida suka basu wuri shida bashir, yace kaiwai meyasa kakeyin hakane, duk sanda mukazo gun harirat sai ka nuna mata tsana a fili?
"na fadawa safwan ya rabu da yarinyar nan yaki, yarinya ba shape ba komai don Allah dubi yanda tabar kirjinta waje, sannan ta wani turosu, saikace dama tana dashi, gata nan sambal ba gaba ba baya, sai uban yanga, ni kasan bana son mace irin wannan, nafi son bul-bul, wadanda suka cika sosai.......
"kai jafar baka da dama.
"Allah kuwa abokina gaskiya na fada, me zaka shafa ajikin wacan yarinyar kaji, komai kyame, kamar sanda.
Bashir ya kwashe da dariya, kai nima fa bana son irin haka, saikaga wata dan tsabagen rashin shape saita tumbure..... ."
safwan ya katse masu hirar su daya bude motar ya shiga.
"wai dan Allah safwan da gaske auren yarinyar nan zakayi? Yayi ajiyar zuciya, toh gani nan dai, amma fa ta fara fita raina, har dai yau, yarinyar so tke wai....in....mts. Manta kawai ni nama fasa, ni wallahi nafasa.
"a'ah kar ka haukace mana, metace dakai?
"wai kasan 'yar iskar yarinyar nan cemin tayi wai ni wane irin masoyi ne da ban iya soyayya ba? Kun san ma'anarta? Bana smoshing dinta irin su hug dinnan, can you believe that, matar da kake so ka aura ta nuna maitar ta afili, tun kafin ayi aure? Jafar dariya yasaka masa sosai, dan har ya tsuko yakai dundu, "dan iska, mahaukaci ka maidani kakemin dariya? Sai ka manta da wannan dama bata da komai sai yanga, banza gata ba gaba ba baya, abunda nagama fadawa bashir kenan, kaga ka hakura da neman auren nan, ka gama karatu tukunna.
"gaskiyane amma ai insha Allahu next year zamuyi graduating ba gara mutum ya samuba, kafin lokacin, shege ka manta saika kara almost one-helf year kafinan
ka zama cikekken likita bayan wanda zakayi yanzu.
Toh Allah ya nuna mana lokacin, (ameen)
haka rayuwa ta ci gaba da tafiya gashi uwani ta shiga aji daya na primary, da yake makarantar babu nusery 3, shi kuwa jafar ya zama cikaken likita, murna biyu agun inna, saika ga yadda take washe baki, ranar da taje 'speach & prize given day' na uwani an bata kyauta a 'punctuality' wato mai zuwa makaranta da wuri. Inna ta gyarata a ranar sosai, don ribon ta saka mata, tayi kyau sosai, su jafar suna abuja zasu zana jarabawa na gwajin zama cikakken likita, anan ne ya hadu da wani tsohon abokinsa, wanda sukayi secondary school tare, soja ne, ana ce masa captain lawal. Shigar da yayi shiya burge jafar, shikenan yaji shifa dolene yayi soja, kota halin kaka. Da yake mahaifin lawal mahmud tsohon soja ne, tare sukaje suka sameshi, dan su nemi shawararsa.
Mahmud usman tsohon soja da yayi mulki ta fanni iri-iri, yaji dadi kwarai da gaske, ya kuma kara nuna masa muhimmacin yin hakan, yace yaro gaskiya in zaka daure ana bukatan irin ku sosai ma,
saboda kana da digiri, sannan cikakken doctor, Allah yayi muku albarka, irin haka akeso, ai Allah ya taimaka, insha Allahu zan taimaka kayi sa'a N.D.A suna sayar da form, sai zasu rubuta jarabawar, saikuje ku siyo,za a taimaka."
bai koma kebbi ba, saida yayi sati, don ya sami iri abokin da ra'ayin su ya zama daya, wato na mata.
Form din N.D.A kuwa sun saya har sun cika, sun maida.
Inna na zaune suna kallon film din hausa, ana waka, uwani ta mike sai rawa takeyi, ita kuwa inna harda yi mata tafi tana juyawa, sai sallamar jafar sukaji daga sama. Uwanikam taci gaba da rawarta, ya shiga saida ya zauna gab da inna ya dauki remote ya rage karan T.V din, sai a lokacin uwani ta nemi wuri ta zauna a jikin inna.
Yadaga murya sosai yace ke tashi daga gurin nan. Inna ta harare shi, kai bana son haka fa, daga shigowarka zaka soma ko? Ta zauna din kafarka ce?.

Kenya mi lari yimbe don nyama yam hande wala fulfulde nah? Toh hande miwadi ta beddugo nyama yam bo,
mi hofni on.

KALLON KITSENơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ