43

2K 162 1
                                    

Kallon kitse

Ashe da akace sojoji na dukan matan su gaskiya ne?
A'a ba gaskiya bane yaya don Allah kiyi hakuri." bata amsa mishi ba ta wuce da uwani daki.
Dakyar ya hakura ya wuce kaduna. Sai dai ransa ya baci sosai, tun ranar daya sumbace ta, sonta ya kara shigarsa ga tsananin sha'awarta dayake yi, "wai meyasa akeyi masa haka? Meyasa ita ba a ganin laifinta sai na shi? Ya bugi siterin mota, "hamza" ya fada a fili, saboda shi ake wulakanta shi? Zaiyi maganinsu insha Allahu.
Toh ya zaiyi maganinsu? Na farko dai Allah ya yiwa uwani wayau ko kebbi yaje bata yadda su kasance tare su kadai, inna kuwa idonta na kansu koda yaushe, toh wai me suke nufi? Yayi ajiyar zuciya Allah ka cika min burina in mallaki yarinyar nan." a haka ya isa kaduna, gwiwa a sanyaye.
Da isar sa gun jamila ya wuce, yayi sa'a tana nan kuwa dan haka anan ya sheke ayarsa.
Saida yamma likis ya wuce asibiti, aiki ya tarar dan emergency ne, nemansa akeyi ya shigo, accident ne akayi harda mai juna biyu a ciki, dan haka dole tasa aka shiga da ita tiyata, saboda jini daya tsinkewa matar, abun gwanin ban tausayi, gata kamar ba rai a tare da ita.
Jafar yana bala'in tausayawa matar, hardai a irin wannan stage din, in mace takai lokacin da zata haihu, yana son yara aransa, baima san nawa yake so ba.
Yanzu haka abunda ke damunsa kenan,
kaddai ace bai sake haihuwa? Ya sha yiwa mata ciki ana zubarwa tun yana universty, toh amma yasan anan kaduna bai taba yiwa wata ciki ba?
A zatonsa ko dan ai kaduna sun waye da yawa ne, da suke iya kare kansu, danshi baya amfani da kororo-roba, sam batayi masa ba, in banda marliya ba macen daya taba kwana da ita baiyi mata test ba, da yake anci gaba yanzu, akwai wata na'ura na aljihu da ake teste din jini, sannan kuma yasan Allah ne ke kareshi.
Yayi wannan aikin ma cike da nsara, ya fitar da 'ya mace, sannan anada tabbacin matar zata tashi, ire-iren aikinsa yasa jafaru yake da sa'a gun manyansa suke ji dashi, shiyasa kuma idan a nema zuwa kas a list ma shine na biyu.
Bayan sati biyu da komawarsa kaduna akayi bikin kara musu girma, yanzu jafar ya zama major, kowa ya shaida hakan, musamman ya bada mota a dauko su baba yunusa da kuma kawu hashimu, an sake masa gida anan cikin N.D.A, gida ne babban gaske, katon falo ne kashi biyu a kasa, sai dakunan bacci a sama, sannan daga cikin gida akwai katon fili, ga kuma parking space daga gaban gidan. Su Alh. Yunusa sunsa albarka.
Sun kuma yi addu'a suka kuma yi masa nasiha mai shiga jiki. Sannan suka wuce kebbi. Sai da ya sami kusan sati uku da kwana biyu kafin ya shiga kebbi.
Inna na daga bakin korido taji budewar gate din gidan ta tsaya taga wanda zai shigo, motoci biyu suka shigo toyota camry na 2005
ce, ta fara shigowa, fara ce sol! Sai jeep marun suzuki, wadda itace leatest a yanzu ta biyo bayanta,
jafar ta gani ya fito daga cikin jeep din, yana sallamar yaron daya tuko toyota, yaci gaba da gaisawa da mal. Mamman da mai gadi, sannan ya umurce su dasu kwaso tsaraba sukai cikin gida, yana gama fadar haka ya kama hanyar shiga cikin gida, anan ya sami inna, da sauri ya isa gunta cike da murnar ganinta, itama cike da fara'a ta rungume shi, abun ya bashi mamaki yaushe rabonsa da samun cikakkiyar kulawa irin ta yau, maganar bashir ta zama dutse, dan haka ya dauki alkawarin rike uwani da hujja.
Sun isa cikin falonta suna kara gaisawa, "inna ga wannan." ya mika mata makullin mota, ta ware idonta, nika saiwa mota?
Eh inna ko batayi miki ba a canza wata?
Tayi auta, na gode, Allah ya kare min kai yayi maka albarka, Allah yasa ka gama da duniya lafiya."
da sauri yake amsawa, "amin amin inna." daya ji tayi shiru, saiya dubeta yace, inna bakice Allah ya bani zuri'a ta gari ba."
tadan yatsine fuskarta kafin tace, "au dama kana son yara?
Kai inna inaso mana, Allah ne bai kawo ba."
toh Allah ya kawo jafaru, nima inaso inga jikoki na, Allah ya kawo masu albarka."
Amin-amin inna na gode, inna na biya muku umrah ku shidda watan gobe ishirin ga wata zaku wuce, Allah yay Albarka, aida hajji ka biya ni nafi son aikin hajji."
inna kiyi tayi min addu'a ina so daga yanzu na fara har sai dan kanki kince bazaki ba, insha Allahu."

KALLON KITSEWhere stories live. Discover now