40

2.1K 159 0
                                    

KALLON KITSE

Yayi tambayar cike da sha'awarta, dan yadda ya lura duk ta fita hayyacinta, daga can bayansu yaji inna na cewa, "me kuma ya kawoka kicin?"
da sauri ya juya inna ina wuni? Ya gaisheta, tare da barin wurin, "inna kin fita ne tun dazu na shigo ina sallama ashe tana kicin taki amsawa"
toh aini banji ba." uwani ta fada.
Inna taji da gangan taki amsawa."
toh ai kaji tace bataji ba, tunda ba kunne daya kuke dashi ba, ina zaka sani? Yayi murmushi, "toh ki kawo min abincina, bai jira amsarta ba ya wuce dakinsa.
Mirsisi tayi, saida inna tace, "ki dauka ki kai masa mana 'yar inna." ta dauka acikin sanda ta isa dakinsa, tana isa ta ajiye a bakin kofar, ta ruga cikin gidan. Ya kalleta, murmushi yayi, ya karasa dashi cikin dakin.
Washe gari ya shigo gaida inna, take ce masa, "tunda kasa aka daura ma aure da uwani, nima inada nawa sharrudan, na farko inaso saina shirya bana so kayi maganar tare warta har saini karan kaina nayi tunanin hakan, sannan zata ci gaba da zuwa makarantarta.
Yace, "na amince inna, a lokacin uwani ta shigo idonsa akan kugunta, 'yan kayan data sane ya fito mata da surarta, yayi ajiyar zuciya, amma idonsa na kanta, gun inna ta nufa ta zauna. "ina kwana uncle? Ya amsa aciki, tayi kamar bata lura da yadda yanayinsa ba a ranta tace kai ka sani, kar ma ka amsa mana."
taci gaba, "inna inaso inje gidan amarya balaraba, nida lawisa."
"toh saikin dawo, ko kallon inda jafaru yake bata yiba, ta shige dakinsu.
Jafar ya cewa inna zai fita sai ya dawo.
Uwani ta fito, ta rataya dan karamin gyalenta, wanda ta saba sawa, ji tayi an jawota, jafaru ne.
Bai saketa ba har saida ya kaita, cikin dakinsa, "ke ina zaki? Gabanta faduwa yakeyi kamar zai fado, ta tsorace sosai, bata iya ce masa komaiba, da ganin ya kulle kofar dakin da key, "bakiji abinda nace bane?
Uncle dan Allah kayi hakuri."
bazanyi ba, inaso inja miki kunne, ki sani yanzu bakida ikon kanki, saida iznina, yanzu kin zama matar aure."
"yi hakuri." ta kara fadi, "wai miyasa in kina gaban inna kin fiye rashin kunya, dakin bar wurin saiki zama kamar wata salaha? Toh bazai yuwu ba, kada ki sake ki fita gidan nan, sai da iznina." ya matso inda take, da yake idonta na kasa, sam bata san yana gab da itaba, sai jin kamshin turarensa tayi cikin hancinta, da sauri ta daga idonta ta dubeshi.
Shikuwa yayi kamar bai san irin tashin hankali day gani a idonta ba, yasa hannunsa na dama akan bango, dai-dai kafadarta, yayi magana kasa-kasa, "Baby ina sonki, ki soni dan Allah."
da sauri ta girgiza kanta, a'a ni bana sonka! Ya hade fuskarsa, idonsa kuwa sun canza kala, bugun gabanta ya karu, har shima yana jin faduwar gabanta, "kin san Allah dole ne ki soni, dan ni abun sone."
da sauri tace "ga wasu matan ba, amma bani ba." duk tsoronsa data keji bai hanata magana ba, "toh zamu gani nida ke wa zai sauko."
zan fita, ta fada tare da zuwa bakin kofa, ya jeho mata makulli,
"zaki shiga hannuna ne yarinya, sai yadda nayi dake, sannan ina kara ja miki kunne ki rika neman izinina kafin ki fita, kin gane ko?
Ta bude kofar har sai da ta fita tukunna, sannan ta kalleshi tace, "inba a nema bafa me zakayi... ." kafin kace kwabo harya biyota, a guje ta isa cikin gida, tana kiran inna, a zaure ya tsaya yana dariya, "yarinya sai tsoro, amma kuma tsiwa ya mata yawa.
Haka yayi hutunsa na sati daya sannan ya koma kaduna, marliya dai tana nan a tunaninta tunda yaki sakinta, toh ba shakka yana sonta, kawai yana sone ya nuna mata kuskurenta dan haka ta dauki aniyar ganar dashi irin son data ke masa. Yana zaune a falo yana waya da bashir, can itama ta leko tana kallonsa yayi mata kyau sosai a ido dama suna shiri saita je ta rungumeshi.
Yau kwanansa biyar da dawowa daga tafiya amma bata ganshi ba, sai yau...." ya tsinka mata tunani data ji yace amarya lafiyarta lau, kasan mene bashir? Wallahi na matsu in sami yarinyar nan a hannuna, kona tashi yin wani abu, saina kasa dan ina shakkar inna, sam inna bata goyi baya naba, sai abunda yarinyar nan ta fada, shine dai-dai a gun inna na rasa dalili......"
marliya ce ta katse masa maganar da yakeyi, tayi tsugunne gabansa, tare da dafashi, "aure kayi doctor? Na shiga uku na lalace ni marliya na shiga uku, gaskiya bazan yadda ba, wulakancin ya isheni haka, yau saika fadamin matsayina a gunka." nan da nan idanunsa suka sauya kala, yana dubanta, so kie kisan matsayinki? Da sauri ta amsa "eh! Inaso na sani."
"toh shikenan dama akwai littafi kusa dashi, yayi rubutu ya mika mata. Ihu tayi, "ka sakeni, bakince in nuna miki matsayinki ba? Toh shine na nuna miki." ya riko kunnuwanta duka biyu ya murde, "wannan saki daya ne, saura na biyu, dan haka inaso ki zama mai fita daga harkata, kuma kika sakeyi min maganar nan saki niyu zai biyo baya, dama kin daina.
Ya tureta, ta fadi kasa tana kuka mai tsimar da zuciya, duk taji tausayin kanta, ta rasa inda zata sa kanta taji dadi, bakin cikinta daya datayi masa magana, amma bazata sake ba, ta fada a ranta, "wannan wace irin rayuwa ne ta shiga haka? Bata da ikon fadan magana saita samu matsala?

KALLON KITSEWhere stories live. Discover now