29

1.9K 156 2
                                    

KALLON KITSE PRT (29)

ga baki dayansu suka kasa amsa sallamar, sai da indo ta amsa ita dake cikin kicin, da sauri ta fito dan babu tantama tasan mai muryar, inna baki ta sake tana kallon kofar falonta, jafar ne ya shigo, yayi saurin isa gun datake zaune ya tsugunna ita kam uwani gefe ta koma, miyau ma ta kasa hadiyewa, sai kallon jafar ta keyi, yayi kiba, yayi kyau. Ita kuwa inna kasa magana tayi, shiya riko hannunta biyu, yasa a nashi shima kasa magana yayi, amma hawayene cike da idonsa, a idonsa yaga inna tadan kara tsufa, farin ciki tareda alhinin abunda ya faru yakeyi, bashir ne ya soma cewa dan Allah inna ayi mana afuwa, munyi laifin da bazamu iya tantacen irin yanayin da muka cusa maku bakin cikiba, amma gamu yau mun dawo muna baku hakuri, ba dan halin muba, a yafe mana." kukan da uwani ta saki shiyasa suka gane akwai wani kusa dasu. Inna ta kwace hannunta ta rumgume uwani, itama kwallan ne suka cika mata ido, amma tayi na maza ta maidasu ciki, ta mike tsaye tareda riko hannun uwani ta kalli bashir tace, na yafe maku, amma inaso ku tashi, ku koma gun wadda tafimu mahimmanci a rayuwarku."
zata wuce jafar ya rike kafarta gwiwarsa akasa, inka gani abun tausayi, idon nan nasa jajir kamar jan gauta yace, inna don girman Allah ki sassautamin, wallahi bada son raina haka ta faruba, nima bansan yadda akaiba, kinawa Allah ki yafemin ki daina fushi dani, hakane jafar naji nakuma yafe maka kamar yadda tun farko, saidai na hakura da kai na barwa matarka ai, bakomai, nan ta barshi suka shige daki da uwani, babu magiyar da jafar baiyiba amma taki saurarenshi, saida bashir ya riko shi zuwa kujera suka zauna yana bashi magana,

wannan shafin yadan yage kuyi hakuri

"haba bashir fadi shawararka, ai ita nake jira, don gaskiya banajin dadin yadda inna kemin, sai kace ba danta ba? Hakane sai dole kayi hakuri, sai shawarar da zan baka, why not ka auri uwani!!!.  Da sauri jafar ya dubi bashir, ya fito da idanuwansa waje, haba bashir wace irin shawarace wannan? Me zanyi da kankanuwar yarinya irin wannan kazamar? Da sauri bashir yace; ada ba take kazamar, amma kasan yarinyar nan  matan manya ce, don babu abunda bata dashi, tun jiya dana ganta nagano inna na matukae son yarinyar, sannan duk wanda zai aureta inna zata soshi, dan haka nake baka shawarar aurenta, sanadin haka zata manta da komai, ko baka ganeba?
Jafar shiru yayi yana girgiza kansa a hankali, anya haka zata yiwu bashir? Yarinyar nanfa bata fi shekara sha shidda, dama gata ta rainani, saboda inna ta faure mata, shiyasa ta shagwaba....
"kai aboki barin fada maka wani abu, wannan yarinyar tafi maka matan bariki dan inaga kai har yanzu baka kawo abunda suka koya maka ba, na wulakantaka, na yaudararka, na wulakanta 'yan uwanka, in baka saniba, jiya baba yunusa ya bani labarin irin wahalan da suka sha kafin Allah ya dawo dakai gida.
Saboda mace kabar mahaifarka, cikin bakin ciki harna shekaru hudu, amma duk wannan bai isheka tunaniba.
Kai inba son ganin KITSE GA ROGO babu abunda kakeso, macen bariki bala'in ne duk da ba duka aka taru aka zama daya ba, amma am warning you, kayi a hankali saboda ba duniyace mataba, kaje kayi tunani." ya mike ransa a bace.
Da sauri jafar ya jawo hannunsa, shima ya mike haba aboki yi hakuri mana, kasan Allah na amince dakai, duk abunda kafada gaskiya ne, na kuma amince da shawararka, amma inaso zan kara tunani akai. Bahir ya saki fuskarsa yakai masa duka, "haba ko kaifa yarinyar nan tanada tarbiyar inna, da wani can ya dauketa, gara kai ka aureta, nasan nan gaba kadan zaka gane abunda nake nufi, waikai me matan bariki suke dashine, wai daka manne musu?
Wallahi indai yariyar nan ka aura, toh zaka ga bambanci kaida kanka, saika bani labari.....

Toh saimun hade a littafi na biyu, dan mungama na daya da iznin Allah

KALLON KITSETahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon