Ya kai hannu ya rika hannunta.

"Kishi ne?"

Ta daga kai ta kalleshi idonta cike da kwalla.

"Ba ni da tabbacin ko minene"

"Ko ma minene ya tafi can ya bar min matata da ita kadai zan rayu"

Hango hasken motar da tai ne yasa tai saurin janye hannunta daga rikon da yai mata taja baya.

"Ina ganin Abbah ne fa"

Sai yai saurin gyara tsayuwarsa. Kusa da 406 dinsa Abbah ta faka golf 3 dinsa ta jigila ya fito rike da bakar leda, yana kawowa kusa da su Sadiq ya risina har kasa ya gaisheshi, ita kuma ta karbi ledar ta shiga da ita. A baki kofar dakin ta tsaya tai gyaran murya irin yadda Abbah yake idan ya dawo gida sannan ta kwaikwayi muryarsa tai sallama.

"Assalamu alaikum"

"Allah ya shiryaki"

Cewar Umma tana girgiza kai. Sai tai dariya ta aje mata ledar ta juya, tana fitowa Abbah na kawowa bakin tsakar gida, sun sun tai da kai sannan ta fice. Hasketa Sadiq yai da motarsa hakan yasa tai saurin komawa sai ya danna mata horn yai ma motar key ya wuce yana daga mata hannu. Cikin daki ta dawo ta zauna kusa da Abbah tana kallon ledar da Umma ke kokarin budewa.

"Abbah mi ka siyo min?"

"Yar lele lemu da abaya ne"

Ya dan bata fuska

"Kai Abbah na fada maka yau agashe nake so fa"

"To yau Katsina muka je, bamu dawo da wuri ba, wannan ma tasha na siyo kar na shigo gidan haka nan"

"To mun gode Allah kara arziki"

Ta fada tana murmushi, tare da kai hannu ta dauka sai Umma ta buge mata hannun.

"Ba na ce ki rika jira ana baki abu ba"

"Ka gani ko Abbah sai ta rika min abu kamar ba Babana ya siyo ba"

"Kyaleta ai sabuwar Uwa zan kawo miki"

Umma tasa dariya.

"A kawo uku mu zama hudu ai dai ni ce uwargida ba komai"

Gaba dayansu dariya suka yi. Sannan Umma ta tashi dan hada masa ruwan wanka.

Washe gari ma tun da asuba ya bar gidan saboda aikinsa na direbansa ci da yake. Zinneera kam bata tashi ba sai kusan bakwai ta tashi a gaggaucw ta shirya dan suna da lacca 8am. Wani farin lace ta saka da Hijab ta fito rike da jaka da littafai a hannunta.

Nabeel na zaune kusa da makwarara yana wanki baki, sai yasa mata dariya.

"Sannu yar makaranta a rayata jaka a rike takardu a hannu"

"Yes kara a san yanzu Jami'a na ke, na wuce ajin yara"

Ya sake kyalkyalewa da dariya.

"Dan baka sababa, ana ganinki za a ce wannan daga gani yar kauye ce, yar kauyen ma ta can ciki kauye ji wani dress na ki, blue Hijab farin lace chaiii"

Sai ta soma bata rai, sai ta kalli kanta ta kalli Umma.

"Umma kin gani ko?"

"Ke kike kula shi ai, zo ki sha koko ki wuce"

"Eyy tab koko Wallahi State University nan duk yayan manya ne, babu mai shan koko a cikinsu, gaskiya ni ba zan sha ba"

"To zo ga dumame"

Ta buga kafa a kasa.

"Haba Umma dai, ni ba zan sha ba"

"To sai me?"

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now