TARA | PRESENT

2.4K 228 11
                                    

****

Ta rufe idonta kenan tana jira taji yaja motar sai taji shiru. Abubuwa da yawa ne suke yawo a kanta. Har wadanda ta manta dasu. Zuciyarta ce ta fara bugu da sauri sauri. A hankali ta bude idanunta ta sauke su akan na Mansur.

"Wai meye damuawarka ne?"

"Kin san me nake so Salmah. So nake ki zo muyi aure!"

"Aure fa kace Mansur! Kanka daya kuwa? Wai tsaya ma. Bibiyata kake yi duk inda nake ko toh wallahi tallahi ka fita a idona. Kar ka ga wai wancen karan nayi kuka ka zata I'm not over you. Ya kamata ka gane cewa baya ta wuce kuma ba zata dawo ba!" Tsayawa yayi kawai yana kallon ta.

Shikam bai san ta a haka ba.

Ganin hankalinsa kamar baya kanta ne yasa tayi dabara ta bude kofar ta fice. A guje kuwa ta qarasa masallaci inda Mansur ya fito shima ya biyota.

Wayarta kawai ta dauka bata ko jin abunda qawayen nata ke cewa. Sheikh take kira amma waya taqi shiga. Zuciyar ta tafasa takeyi a lokacin kuma Salim kawai take son yi wa magana.

Har ta koma gida ranta gaba daya a jagule yake.

****

Jamilah

Page ;4

Ummah's trick.

Duk wanda ya zaunar dani zai mun magana in dai akan sheikh ne to daga ranar na dena masa magana. Har Hadizah ma sai da muka koma idan na hango ta, canza hanya nake saboda kar ta min magana.

Abun haushin shine ni sam ban yarda gaskiya suke fada min ba balle ma na duba lamarin ko na shiga bincike da kai na.

A haka na kafa, na tsare ni fa dole shi nake so.

Yau ma kamar kullum ina faculty dinsu muna hira sai nace masa akwai abunda nake son gaya masa.

"Dama ce min akeyi wai ba mutumin kirki bane kai..." Ban qarasa ba ya katse ni da ihu.

"Ai dama na sani! Na sani akwai wanda zasu dinga zuga ki. Wato kin fara daukar zugar mutane ko? Shi kenan babu dama mutum ace yana da abun duniya sai a fara masa sharri. Toh kin kyauta. Nace kin kyauta da kika fara daukar maganar mutane." Ban san bakina a bude yake ba sai da naji kuda na nema ya shiga saboda mamakin da nayi.

Ko tsayawa yaji bayani na baiyi ba fa ya hau ni da masifa. Lallai wannan babban al'amari ne da ban taba cin karo da shi ba.

Mota ya shiga ya tayar yayi gaba abunsa ba tare da yace mun komai ba. Kallon qurar da ta tashi nayi sannan na girgiza kai na wuce ajinmu. Dama fitowa nayi.

Ko da muka tashi nayi mamakin ganin motar sa a qofar department dinmu. Da saurina na qarasa ina murmushi.

"Kiyi haquri na miki fada dazu. Dama raina a bace yake ne." Wani sanyi ne ya ziyarci zuciyata. Sabon qaunar sa na qara yaduwa a ko ina na zuciyata. Dama na san sheikh dina mutum ne na qwarai. Nasan ba zai mun fada haka kawai ba.

"Dama banji haushi ba." Na fada da qarfi. Bayan a gaskiya dazun raina ya baci sosai kawai danne zuciyata nayi saboda ina neman na masa uzuri tunda bai saba yi min haka ba.

Na qara da cewa; "Amma dai kasan babu kyau fushi ko? Kamata yayi ace duk sanda kake cikin fushi to ka gaya min sai na dan nisanta kaina da kai har sai ka huce. Inda ruwan sanyi a kusa ma, sai na baka ka sha." Sosa qewarsa naga yayi sannan ya kalle ni cike da soyayya.

"Haka ne sarauniyar zuciyata. Ina matuqar sonki wallahi saboda hankalinki. Ga kyau ga hankali. A idon sheikh fa kinfi ko wacce mace kyau a duniya." Kunya ce ta rufe ni yayinda naji dadin kalamansa sosai.

MATAR SHEIKHWhere stories live. Discover now