DAYA | PRESENT

4.5K 386 21
                                    

Assalamu alaikum.

Da sunan Allah mai rahama mai jin qai.

Chapter one is here. Show some love by sharing!

****

Daya daga cikin tiyatocin jami'ar cike take dan'kam da dalibai suna ta kai komo. Kowannan su yana harkar gabansa. Wasu kuma suna zaune a gefe suna danna wayoyinsu, wasu suna hira da abokansu wasu kuma sunyi shiru suna jiran isowar manya manyan malamin garin.

Wani taro na qarawa juna sani a kan addinin musulunci zasuyi da kuma qara fadakarwa da waye wa jama'a kai akan abubuwan da su ka musu duhu.

Zaune take ita da qawayen ta suna ta hira abunsu. Daya daga cikin su ce take ta tsaki tana duban agogo. Ita Allah ya gani bata son taro irin wannan.

"Wai dan Allah malaman nan ba zasu qaraso bane? Nifa na gaji." Ta fada tana bin qawayen nata da kallo.

"Hmm ki bari kawai nima tun dazu baya na ya gaji da zama." Dayar ta bayar da amsa.

"Ke dalla malama kina jin mu amma kinyi shiru duk ke kika jawo muka zauna fa." Dayar ta buge kafadar Salmah. Salmahn ce ta dan sosa wajen kafin ta ajiye wayarta a cikin jaka ta kalle su.

"Toh ni yanzu da kuka kafe ni da ido me kenan? Ban fa ce dole ku zauna ba nima saboda bin umarnin Ummah zan zauna." Ta tabe bakin ta tana mayar da idonta kan mutanen da suke shigowa.

"Kullum maganar kenan, sai ta dinga yi kamar wata salaha, kamar irin ta fimu sanin Allah amma kuma duk kanwar ja ce." Qawarta ta mayar mata da magana, taja hannun dayar suka fice suka bar ta. Ko ta kansu ma bata bi ba ta cigaba da kalle kallen ta.

Duk kanwar ja ce... Abun ya dawo ya tsaya mata a wuya. Tabbas ba qarya bane to amma me yasa zaiyi mata ciwo? Jijjiga kanta tayi cikin dana sani da kuma cewa ina ma zata iya mayar da hannun agogo baya.

Ta na cikin tunani, sai ji tayi ko ina yayi tsit, kafin ta ankara taji ana gyaran murya a lasfika.

"Bismillah, wassalatu wassalamu ala rasulillah..." Tun kafin ya qarasa taji lallai tana son ganin fuskar mutumin nan amma bata samu damar hakan ba saboda mutanen da suke gabanta sun kare ta. Haka dai ta zauna don dole tana jira a gama ta tafi. Tsawon awanni biyu ne suka shude kafin malaman su tafi ba tare da taga ko daya a cikin su ba. Ita dai taji wannan me muryar da taja hankalinta yace sunan shi SHEIKH MUHAMMAD SALIM.

*****

Sauri sauri takeyi ta qarasa gida saboda ta huta. Yau tayi bala'in gajiya. Tana shiga gida ta tarar Abba yazo gida, ta gaishe shi zata wuce kenan sai taji ya ce ta dawo, sai da gabanta ya fadi kafin ta sunkuyar da kai ta nemi waje ta zauna.

"Ina kika tsaya?" Ya fada idon shi a kanta. Yana daga cikin qa'idojojinsa akan lallai sai mutum ya dawo daga makaranta akan lokaci. Qarin minti sha biyar kadai ya bayar.

"Ah, ni nace ta tsaya ta saurari lakcar da malamai zasu yi akan addini." Ummah ta fito daga kicin tana goge hannunta da wani tsumma kafin ta nemi waje ta zauna.

Wata ajiyar zuciya Salmah tayi kafin ta miqe ta bar wajen tunda an bashi amsar tambayar sa.

"Wannan tsaurin da kake mata fa bashi da wata rana." Ummahn ta fada tana kallon Abban da kamar ba hankalin sa ba akanta ya ke ba.

Numfasawa yayi kadan. "Kullum haka kike cewa amma ni na fiki sanin wacece Salmah." Ya miqe tare da daukar hular sa da ya ajiye a kan tebur din tsakiyar falo domin fita sallahr Maghreb.

"A dawo lafiya." Ta fada a taqaice tare da barin wajen itama.

Jim kadan, sai ga Muhammad ya shigo da abokanan sa suna ihu. Bangaren sa ya wuce da su suka kunna talabijin. Tana kamawa aka kai tashar ball. Kafin mintina biyar, gaba daya sun cika gidan da hayaniya suna ta ihu.

Salmah ce kwance a dakinta tana qoqarin yin bacci amma sabida hayaniyar su sai ta kasa. Shikenan ace duk daren duniya sai an ishe su da ihu, tab lallai yau kam sai tayi musu magana.

Hijabin da ya tsaya mata dai dai gwiwarta ta saka ta nufi falon da suke kallon.

"Yaya," ta kwalla masa kira amma kamar ma be ji ta ba. Tsaki tayi ta nemi inda rimot din yake, sadaf sadaf ta dauka sai ji sukayi an kashe TV.

"Ke! Kina hauka ne?" Ya daka mata tsawa har sai da gabanta ya fadi amma ta dake.

"Barci fa nake ji amma kun ishe ni da ihu. Ni gaskiya..." Katseta yayi.

"Dalla malama bani remote dinnan tun kafin ranki ya baci." A sanyaye ta miqa masa tana qunquni.

"Bace mun da gani." Ya yi mata nuni da bakin qofa ta juya zata tafi.

"Woooo maza kana wuta wallahi." Daya a cikin abokan ya daki bayan sa. Duk suka kwashe da dariya.

Hawaye ne ya taru a idonta, nan da nan ya fara zubowa. Ita kam a duniyar nan ta tsani a ci mata mutunci a cikin mutane sannan ayi mata dariya.

Toh yau ba abin da Muhammad yayi mata bane ya bata mata rai, sai dai kawai ya tuno mata da abunda ya taba faruwa da ita wanda duk gidan babu wanda ya sani.

Saboda shima abun, anyi embarrassing dinta ne sosai da qasqantar da ita.

Juyi takeyi a kan gadon baqin cikin yana qara taso mata. Ta rasa inda zata kanta. Sai kawai ta tuno wani abu. Ta dauko jakar ta a qarqashin gado ta fiddo da wasu kwalabe tana qura musu ido.

'Kar ki sha!'  zuciyar ta ta raya mata.

'Ki sha kiji sauqi a ranki.' Wata zuciyar ta ayyana mata.

Runtse idonta tayi tana tunani wace zuciyar zata bi. Kusan minti biyu tayi tana nazari kafin ta bude kwalbar ta kwankwade qwayar dake ciki.

Babu bata lokaci, ya gwaraye mata jiki, taji yana fisgar ta. Ba shiri taji duk wata damuwar da ke damun ta ta bace, driving her out of the real world.

A world, full of deceits!

****

First chappie is down!
Your thoughts?

MATAR SHEIKHWhere stories live. Discover now