BIYU | PRESENT

3.6K 357 14
                                    

Assalamu alaikum.

Let's do the tag thingy. Tag our friends in the comment section. And share on our social medias.
Thank you.

Dedicated to Saadah_Mohd.🌷

****

A hankali jikinta ya fara motsi, tana jujjuyawa kamar jikin nata ciwo yake. Hasken rana da ya bullo ta windo ne ya haske mata ido hakan yasa ta kasa bude idon nata da wuri.

Sai da ta dan bude daya a hankali, sannan ta kalli hannunta wanda taji yana mata zafi zafi sai ta ankara ma allurar qarin ruwa ce a jikinta. Zumbur ta tashi a tsorace tana kallon gefen ta inda wata mata itama take barci.

Me ya kawo ni asibiti? Ta tambayi kanta tana kalle kalle kamar wacce ta samu tabin hankali. A hankali ta fara tuna abun da ya faru.

Runtse idonta tayi cikin fargaba. Allah yasa dai ba'a fadawa su Ummah dalilin sumar ta ba. Tana cikin wannan tunani ne zai taga an bude kofa.

Likita ne, wani saurayi kyakkyawa da zai wuce shekara talatin ba ya qaraso wajen ta yana dan murmushi. Kau da kai tayi domin ita a duniyar nan babu wanda tafi tsana kamar namiji. Musamman ma idan yana nuna mata kula Sai taji duk ta tsani mutum.

"Sannu ko? Ya jikin malama...?" Ya qarasa tambayar yana neman yaji sunan ta.

"Lafiya lau. Ina su Umma?" Ta tambaya ba tare da ta bashi amsar tambayar ba. Kafin ta sake yin maganar sai ga iyayen nata sun shigo.

"Alhamdulillah. Likita me ka gani a test din?" Ummah ta tambaya gami da rungume Salmahn.

"Gajiya ceh, depression, da kuma..." Sai ya mayar da kallonsa zuwa Salmah.

Kallon da yake mata ne yasa ta sha jinin jikinta. Bata ankara ba taji zuciyarta na dukan uku uku a lokaci guda. Yau idan likitan nan ya tona mata asiri ya zatayi? Tab lallai yau tana cikin matsala.

Itama kallonshi ta shiga yi tana me roqon sa ta idonta. Murmushi yayi, haka kawai sai taji hankalinta ya dan kwanta.

Allah dai yasa bazai kwafsa ba.

"Sai kuma wataqila rashin barci. Amma ga magunguna da zaki siyo a waje Ummah." Ya miqa mata wata takarda. Da sauri Ummah ta karba tayi waje ya rage daga Salmah sai likitan sai wasu masu jinyar kuma.

Zagayo wa yayi, ya duba gudun ruwan da ake kara mata kafin ya gyara muryar sa.

"Me yasa kika sha qwaya?" Ya tambaya cikin wani irin salo da yasa jikinta ya fara rawa. Bata taba samun wanda yayi mata wannan tambayar ba kuma ba tajin zata iya bayar da amsar tambayar ko da kuwa tilasta ta za'ayi.

Kallon ta yayi, ya tabe bakin shi kafin ya sake magana. "Idan baki fada ba fa zan gaya wa Ummah saboda naga alama kamar basu san halin da kike ciki ba." A razane ta daga kanta tana kallon shi. Gaba daya ma ta rasa ta yanda zata yi mishi magana. Itakam ta sani cewa idan Ummah taji labarin nan kwanan ta ya qare.

The day Ummah will find out that she was using drugs was her biggest nightmare. She would do all it takes taga cewa ta boye wannan halin nata.

Gyaran muryan da likitan yayi ne ya saka ta dawo daga duniyar tunani. Toh yanzu shi me yake so tace masa?

"Ehmm, daman... Dan Allah ko zaka iya mantawa da wannan tambayar?" Ta fada a hankali. Shi kuwa likitan kallon fuskarta yakeyi sosai yana mamakin me zai saka kyakkyawar yarinya kamar ita shan qwaya.

"Da alama dai so kike su Ummah suji labari. Then, it will be easier." Ya juya zai fita sai ga Ummah nan ta shigo.

Hadiyan yawu Salmahn tayi tare da hade hannayan ta biyu a boye tana roqon shi. Gyada kai kawai yayi ya juya ya fita yana tausayin ta sosai.

MATAR SHEIKHWhere stories live. Discover now