SHIMFIDA | STORYDUCTION.

9.2K 443 39
                                    

Assalamu alaikum.

Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin halittu. Kullum ina qara godewa Allah da ya bani lafiya da duk wasu necessities na rayuwa. Alhamdulillah!

Hmmm😂😂😂 bari na dan baku labarin yanda idea din MATAR SHEIKH tazo min... Ko da yake shikenan dai. Lol.

So, littafin zai fara zuwa neh nan ba da jimawa ba. Kuyi adding, tagging, sharing kafin na fara rubutawa ba qaqqautawa😂😎. Jokes aside, ugh! Hausa da wahalar sha'ani take wallahi. Anyways, I'm a proud Hausa Fulani girl😻🙌.

Zan kawo littafin ne cikin harshen Hausa amma za'a iya tsintar ingilishi jefi jefi in sha Allah.

NOTE:

Labarin nan qirqirare ne. Duk wasu gurare ko garuruwa ko sunaye da zanyi amfani dasu (ko da sunyi kama da gaskiya,) nayi hakan ne don labarin ya tafi daidai ya kuma isar da right message. All I mean is, it's totally a work of fiction! Any resemblance to reality, is a mere coincidence.

SOMIN TABI.( something like_prologue or so😂💔).

2014.
Kano, Nigeria.

Kallon kwalaben da ke gabanta tayi amma bata iya karanta komai daga jikin su. Idanunta sun kada sun yi ja wur, kanta har wani juyawa yake tana ganin abubuwa uku uku.

Hannu tasa ta dauki wata kwalba da babu komai a cikinta, ta bude wata da bata ma iya karanta sunan ta zuba rabi a kwalbar da babu komai ta ajiye hannun ta na rawa. Wata kwalbar ta bude ta hade da wancan rabin ta jijjiga sannan ta shanye duka.

Cikin mintuna kadan ta sake buguwa sosai kasancewar magungunan sun ratsa mata jiki sosai. Duk da a yanayin maye ta ke, tana iya tuno dalilin da yasa ta fara shaye-shaye.

Zafafan hawaye ne suka zubo daga idonta tana dana sanin rayuwar ta. A haka dai tana tunane-tunanen hankali da shirme da ma wanda magungunan ke kitsa mata su, bacci ya dauke ta.

****

Hoton dake hannunsa ya ajiye yana ajiyar zuciya. Har izuwa yaushe ne zai manta da matar sa, Jamilah? Anya zai manta da ita kuwa? Jijiga kansa yayi hawaye na neman zubowa daga idonsa.

Qarar wayarsa ne ya katse masa tunani.

"Ya Sheikh, jiranka akeyi." Yaji Sheikh Usama ya fada. Sannan ya tuna ashe ana jiransa zasu je da'awa a wani qauye.

A gaggauce ya shirya ya fice yana kewar matar sa da ta rasu shekaru goma baya.

****

Sheikh Muhammad Salim shine sunan sa. Babban malami wanda ake ji dashi saboda tarin ilimin da yake dashi. Toh amma kafin ya zama abun da yake a yanzun, ya aikata abubuwan da yake da na sani akan su sosai da sosai. Zamu iya cewa rayuwarsa ta baya akwai matsala a cikin ta. Domin kuwa ya dauki alhakin mutane da dama. Ya muzantawa mutanen da ya kamata ace yafi kyautatawa.... Abubuwan da yawa sai kawai mu zuba ido mu karanta a cikin littafin....

Salmah Bello sunan ta kenan. Mai shaye-shaye a miskilance ba tare da ansani ba. Sai dai an ce komai yana da dalili. Ko meye dalilin da yasa ta fara shaye-shaye? Yaya zata kaya a yayinda na tsinci kanta a matsayin matar Salim wanda bata san komai game dashi ba?

Yana da tabo a rayuwarsa. Sai dai kuma na ta tabon ya taka nashi ya karya! Taya wadannan biyun zasu zauna tare? Taya Salmah zata yi haqurin zama MATAR SHEIKH bayan ta fahimci zaman da Salim yayi da matar sa JAMILAH?

Labari ne daban, me tarun darussa da yanayin tafiyar da rayuwar yau da kullum. Zamu yi dariya, zamuyi kuka, zamu dauki darasi in sha Allahu.

A tafiyar zamu gamu da mutane kala-kala zamu leqa labarin rayuwarsu domin mu tsinci abun tsinta, mu watsar da marar kyau.

#shortstory
#MATAR SHEIKH
#FOLLOW AeshaKabir.

So, a sneak peek?
First chapter on the 10th of November in sha Allah.

MATAR SHEIKHWhere stories live. Discover now