POST 23

73 8 2
                                    

Abubuwa sai buɗe wa Zaid yake yi ga shi yanzu bai da matsalar kuɗi sai dai duk abin nan da yake yi ya rasa yadda zai tun kari Mai Faskare da batun kai kuɗin sadakin tun da Baseera sun kusan dawowa, da sallama ya karasa ɗakin Mai Faskare aka amsa masa sannan ya shiga tare da zama cikin ladabi kansa a kasa, Mai Faskare ya kalle shi ya ce.

"Malam Zaidu lafiya.?"
        Shuru Zaid ya yi don yawun bakinsa sun masa kauri da kyar ya iya buɗe baki ya ce.

"Baba dama akan maganar gidansu Baseera ne."

"Me ya faru a gidan na su? Ko wani mumminar al'amari ya afku ne a can gidan.?"
     Cewar Mai Faskare. Zaid ya ce.

"A'a."
     A taikaice. Mai Faskare ya ce.

"Ai yana yin da na ganka ne duk ya ruɗani ko wani abu yana damunka ne? Ko kuma auren ne ka fasa.?"
     Zaid ya yi saurin girgiza kai haɗe da cewa.

"Ba haka bane Baba dama maganar kuɗin auren ne nake son za a kai."
      Ya karashe maganar da sanyin murya. Murmushi Mai Faskare ya yi sa'annan ya ce.

"Yaro yaro ne yanzu kan wannan maganar ne yasa tun ɗazu kake kumbiya-kumbiya? To shi ke nan kwantar da hankalinka zan je na samu Babanka Harisu duk ranar da ba zai fita ba sai muje nema maka auren, hankali ya kwanta ko Malam Zaidu.?"
      Murmushi Zaid ya yi tare da sosa keyarsa ya tashi zai fita Mai Faskare ya ce.

"Af ka ga Zaidu dawo ka zauna akwai maganar da zamu yi da kai."
       Gaban Zaid ya faɗi tare da koma wa gurin da ya taso ya kuma tankwashe kafafuwarsa cikin ladabi da biyayya, Mai Faskare ya dube shi sannan ya ce.

"Abin da yasa na ce ka dawo shi ne a 'yan kwanakin nan na rasa in da ka ke samo kuɗi masu ya wa, sannan na je gurin Oga Hassan ya ce min rabon da ya saka a idanunsa tun ranar da wani tsautsayi ya gifta tsakaninka da customern ka tun wannan ranar bai ƙara sa ka a idonsa ba, amma kuma na ga yadda ka ke wasa da kuɗi shi yasa nake son sanin in da kake samun kuɗaɗen.?"
        Mai Faskare ya karashe maganar da kura wa Zaid ido ya na jiran jin abin da zai fito da ga bakinsa, tambayar ya zo wa Zaid a bazata bai taɓa tunanin Mai Faskare zai amsa wannan tambayar ba yawun bakinsa ne suka ƙafe a yayin da maƙogoronsa ya bushe da kyar ya iya tattaro murmushi ya ɗaura a kan fuskarshi ya ce.

"Baba dama ina son maka maganar sai kuma ka riga ni wato daman muna fita yin 'yan kasuwanci da Habu muna fita mu saro dabbobi mu kai kwata a siya kuma alhamdulillahi ana siya da kudi masu yawa, sa'annan kudin Allah na sa musu albarka shi ya sa ka ga ina wasa da kudi."
      Kyawawan 'yan yatsunsa ya ɗaura a kan keyarshi domin sharce zufar keyar da ta tsatsofo masa, murmushi Mai Faskare ya yi sannan ya ce.

"Alhamdulillah gaskiya ka yi farar dabara kuma zama da sana'a ɗaya tsautsayi ne ko nima nan da tun samartakana na yi kokarin yin dabarar nan da yanzu na fi hakan kuma na wuce yin faskare amma sabo da rashin mafaɗi sune dalilin shi ga na wannan yana yin da rashin uwa amma da uwata na raye ban taso hannun kishiyar uwa ba na tabbata nima da nazama nagartaccen uba a gareku, shi ke nan za ka iya tafiya dama maganar ke nan ita kuma wannan yarinyar in ta dawo sai ka sanar da ni saboda aje da maganar gaban magabatarta kamar yadda kake so."
     Farin ciki ne ya lulluɓe Zaid sa'annan ya ta shi ya fita, ko da isarsa ya tarar da missed calls sun fi ashirin murmushi ne ya suɓce masa saboda abin da yake so ke nan shi ma ya yi kuɗin da zai dinga tarar da missed calls bila adadin a wayarsa, lambar da ta fara kiransa lambar ya bi amma a kashe take ya gwada kiran lambar amma har yanzu kashe take. Lambar Baseera ya kira suka sha soyayyarsu kamar zasu cinye juna a waya ko wanne na kokarin nuna wa ɗan uwansa yadda ya damu da shi da zaƙuwarsa a kan lokacin auransu ya gabato. Zaid ya ce.

"Bassylurv wai yaushe Daddy zai dawo kasar nan ne don na zaku da son ganinsa wallahi."
      Shuru ta yi na wasu 'yan daƙiƙu kana ta ce.

"Z Guy Daddy yanzu haka yana kasar nan amma gaskiya ba a Kaduna ba don ba ma tamu yake ba, kira ce da gaggawa daga fadar shugaban kasa da yake kasan kwanan nan ministan lantarki zai aurar da 'yarsa, to shi ne fa shugaban kasa ya ce ya ɗauki nauyin takalmar da ango da amarya zasu sa tun da ga fara biki har ranar buɗan kai sannan kuma Daddy ne zai kawo musu takalma sabbin design wanda babu wanda ya taɓa saka irinsa to shi ne ya kawo musu su zaɓa. Sanfarin takalmar yanzu ya kawo don sun zaɓa to ka ga abin da ya sa Daddy yake Abuja ke nan, kuma ya ce min in da sarari zai shi go ya duba ni tun da yayyina biyu duk suna karatu a can ne, to shigowar tasa nake jira sai na faɗa maka shi ya sa ka ga har yanzu baku haɗu ba amma In Sha Allahu komai ya kusan zuwa karshe tun da ai dole ya zo aurena."
       Tun da ta fara magana annurin fuskar Zaid suka bayyana saboda abin da yake son ji ke nan.

'Wata rana nima shugaban kasa da kanshi zai ɗauki waya ya kirani har da magiya don kawai na kawo mishi takalma kirar Dubai, domin ni ba Italian zan dinga shi go dasu ba Dubai za ni saboda na ga duniya ita ma ta ganni, auren kawai nake jira a ɗaura ai zancen a ɗaki ɗaya nasa Baseera zai je kunnensa daga nan sai a bani kyautar katon gida mai cike da kayan alatu.'

"Z Guy kana jina kuwa.?"
      Baseera ta katse mishi maganar zuccin da yake yi, ya yi saurin cewa.

"Sorry baby, Ogana ne ya fito shi ne muke ɗan tattaunawa a kan maganar tafiyata Mexico gurin wani taro, amma gaskiya na ce basa ba zan samu dabar zuwa ba saboda hidimar bikin da ke kaina, ga shi ginin gidana ya yi nisa kuma ban son tafiya ne na bar gidan a hannun 'yan aiki duk sai a yi maka aiki mara inganci gwara ina lura dasu ko Sweedy.?"
      
"Gaskiya hakane ni karma su min ɗakuna ƙanana saboda kayan da zan kawo don yanzu haka 'yan uwan Mummyna suna Saudia suna haɗo min kaya kuma a kalla ina son ɗaki biyu da ƙaton falo yadda zai wadace mu, nima naso zuwa to kasanni da son kauye don ganin rayuwar da suke yi mai ban sha'awa ya sa nace su tafi kawai ni zan je kauye kuma nasan ba za su siyo min kaya mara inganci ba yadda Daddy ya cika su da kuɗi."
      Cewar Baseera. Shi kuwa gogan sai murmushi yake yi yana hango kanshi a manya-manyan motocin da ake ya yi kuma burin ko wani saurayi, haka suka ci gaba da hirar soyayyarsu da tana jin kulawar da suke wa junansu, Gwaggo Ramu ce ta zauna kusa da Baseera haɗe da murmushi ita dai tun da Baseera ta ce mijin da zata aura a kasar waje yake aiki take lillike wa Baseera saboda ko da an yi auren ita ma a dinga tuna wa da ita a duk lokacin da Zaid ya dawo da ga tafiya, ajiye wayar Baseera ta yi bayan sun yi sallama ta ce.

"Gwaggo Ramu lafiya na ga kin kura min ido ai irin wannan kallon har muni na zaki hango."
     Dariya Ramu ta yi sannan ta ce.

"Wallahi birgeni kike yi 'yar Yayana komai naki mai kyau ne kai hatta maganarki abin kallo ne wannan dalilin ne yasa nake son zama kusa da ke 'yata."
      Dariya Baseera ta yi sa'annan ta ce.

"Kai Gwaggo Ramu da abin dariya kike wallahi ina kyau ɗin? Ai kyau yana gurinki Gwaggo Ramu ga shi Allah ya baki gashi har gadon baya kina da tsawo ga jiki mai kyau, fuskarki madubi ne da zai haskaka zuciyar duk wanda ya yi dacen samunki matsayin matar aure, wallahi har wautar Kawu Bala nake gani da ya sake ki don kawai bakya kwalliya kuma ai kwalliyar ba ta yuwu wa sai da koshi sai anci a ke kwalliya, ko ni ce ban koshi ba ba zan yi kwalliya ba wallahi.
          Ajiyar zuciya Gwaggo Ramu ta yi domin Baseera ta sosa mata inda yake mata ƙaiƙayi ta ce.

"Bari kawai 'yata Bala ya cuceni ba rashin kwalliya ba ne ya raba ni da Bala sai dai cin amanata da na gano yana yi shi ne gudun karna tona musu asiri sai ya sake ni kuma dama sakin nake nema don na gaji da ƙaryar arzikin Bala."
     Da sanyin murya ta yi maganar.

"Makaryacin namiji ai bai yi ba wallahi na tsani makaryaci shi ya sa jinina bai zo ɗaya da talaka ba saboda da sun ga ubanka na da kuɗi sai suma su ari rigar arziki su zo gurin ka babu abin da suka iya sai karyar abin da basu da shi, shi ya sa ni dai kam babu ni babu talaka yaje can ya karata da karyarsa amma ba dai ni Baseera Bashir Bilal ba don nafi karfin namiji ya kalli idona ya sharara min karya, kuma kin ga shi wannan da zan aura Gwaggo Ramu? Ko motar hawansa abin kallo ne balle kuma gidan da ya fito tabbas kina kallonsa kin san da ga gidan alfarma yake, yanzu haka maganar gidan da zan zauna muke yi wata tafiya ce tazo mishi amma saboda ginin da yake yi ya fasa zuwa."
      Ita dai Ramu tun da Baseera ta fara magana take kallonta saboda a duniyar nan ta na son namiji mai kuɗi kamar mijin da Baseera za ta aura............

Wannan Ke Nan

______________________________

Hmmmm ashe dai Baseera gado ta yi a gurin Gwaggo Ramu tab! Uhnmmmmm mu je dai zuwa jirgin ƙara lula wa yake yi da sannu zai dira a garin feɗe gaskiya. Ranar da gaskiya za ta yi halinta a wannan ranar............

Wattpad @Basira_Nadabo

Basira Sabo Nadabo Ce.

NADAMATA! PART ONE Where stories live. Discover now