POST 9

75 10 0
                                    

"In wa'azi za ki min ina tunanin zai fi kyau ki je masallacin da ke yamma da gidan nan ki yi, don ba zan laminci rashin kunyar nan ba, sannan ki sani wallahi in baki nutsu kin san abin da kike yi ba zan saɓa miki a gidan nan."
     Murmushi Badar ta yi sannan ta ce.

"Mummy yanzu wa'azin shi ne rashin kunya? Ni dai kin san ta gefe na ko kashe ni za'a yi ba zan faɗawa kowa wannan sirrin na ku ba, amma Mummy ki sani akwai ranar tonan asiri, a wannan ranar zan yi da na sanin fitowa ta tsatsonki, kuma a wannan ranar zan feɗewa kowa ai nihin abin da ya faru a wan cen ranar.!"
        Ta sharce hawaye tare da barin gurun. Jikin Fulani Bilkisu ya yi san yi sai kaiwa da komowa take yi.

'Dole in ɗau mummunan mataki akan Badar tunda har tana da karfin gwiwar faɗa min magana, dole na yi duk yadda zan yi don ganin asirina bai tonu ba. Kamar ni Badar za ta watsa min ƙasa a ido, har tana cewa zata faɗa haƙiƙanin gaskiyan abin da ya faru? To wallahi ba zai yuwu ba dole in san abin yi, tun kafin Badar ta tona min asiri, kai ba zai taɓa yuwu wa ba...."
       Tana maganar zucci tare da kaiwa ɗayan hannun ta naushi...

Wannan Ke Nan

      BABI NA BIYU

Zaid ya na  barin layin ga ba ɗaya ya gangara bakin titi ya sau ya kayan jikin shi zuwa na aiki ya mai da kayan yadda ya ɗauka, tun daga shigar shi garejin ya san akwai matsala sabo da yadda kowa ya tsaya yana zaman jiran shigowar shi, da sanyin jiki ya ƙarasa tare da fitowa a motar. Oga Hassan ne ya ta re shi da faɗa kaman zai ari baki don yau hankalin shi ya kai kololuwan tashi.

"No kar ka damu Hassan kila wani abun ne ya faru da har yasa ya daɗe bai dawo ba, kuma da mun ji ta bakin shi kafin mu yanke hukunci."
      Cewar wanda ya kawo gyaran mota, Zaid ne ya gyara tsayuwa sannan ya ce.

"Wallahi nima ba'a son raina har na daɗe haka ba, ina cikin tafiya ne sai tayar motar ta fashe, kuma da na du ba motar babu safaya taya, shi ne wasu bayin Allah suka taimaka min muka tura motar har zuwa garejin Mamman, a nan ne ya sa min taya nadawo, amma ni babu inda naje.!"
       Da raunin murya ya karashe maganar, jikin Oga Hassan ne ya yi sanyi saboda ya zarge shi akan abinda bai taɓa kamashi ya na yi ba, tayan mai motan ya kalla amma ya gaza gaskata abin da Zaid yake faɗa saboda shima bai daɗe da san ya sabuwar taya ba, kuma dai wannan tayar ita ce a jikin motar, amma ganin ba shi da hujja yabar maganar tare da sallamarsa yabar gurin. Zuciyar shi cike da zullumi akan abinda Zaid ya faɗa don bai gamsu ba, kuma ya ji zuciyarsa ba ta aminta da kalaman Zaid ba.
       
"Inna wallahi ko sisi ban maganin shi, ni rabon da na riƙe dubu na kaina ma ban iya tuna wa."
      Cewar Zaid, tausayin ɗanta ne ya cika zuciyarta ta ce.

"Ai kana ma kokari Zaidu, sannu kai dai Allah ya yi albarka, wanda ya kamata ya ciyar damu ma ba ya ta kanmu kullum burin shi yadda zai faranta ran shegiyar matan cen ne, bai damu da ci da shan mu ba. Tsakanina da mai faskare sai Allah ya yi mana hisabi!"
      Hawaye ne suka surnano daga idonta ta yi saurin sharce hawayen sabo da tsakin da Zaid ya yi. Cikin kunan zuci ya ce.

"Wallahi Inna kina da matsala yanzu ɗan wannan maganar ne ki ke kuka, ni fa shi yasa na gwammace na yi zamana a waje, sabo da irin wannan korafe-korafen, kuma na yi-na yi da ke akan ki kama sana'a duk sabo da gudun irin wannan ranar, ga shi abin da za kici ma yana gagaranki, kullum maganar ke nan Mai Faskare kuma fisabilillahi Old Man ɗin nan yana kokari kece dai kawai ba ki da godiyar Allah."
      Tun da Zaid ya fara magana ta nemi hawayen ta rasa dama don ta cusa tsana ne a zuciyarsa yasa ta yi wannan maganar, sai kuma hakarta ba ta cinma ruwa ba.

"Ai na yi shuru kuma nabar kukan tunda ɓata maka rai yake yi, amma dai kasan ana shiga hakkina ko? Yaushe rabon Malam da gayyata ta turakarshi? Kullum in na yi magana ni ce ban da gaskiya."
      Wani ƙululun baƙin ciki ne ya tokare Zaid a ƙahon zuci.

'Yanzu fisabilillahi me tsohuwar nan za ta nema a wani har kan turaka? Me ya rage gareta don Allah? Yanzu in na yi magana ta ce dama bana son laifin Babana, a ƙalla za ta kai shekara hamsin amma ta ma yar da kanta kamar 'yar shekara saba'in a hakan take neman a gayyaceta turaka, ko ina wari yake fitarwa gashin kanta ma a dankare yake sabo da dauɗa, hakora duk sun yi gansakuka bakin na ba da wani kalar wari, wai ya ma za'a yi miji ba zai auro mai tsafta ba amma duk da haka laifi Old Man take gani.'
         Cewar Zaid da yake kare mata kallo tare da yin magana a zuciyarsa....

Wannan Ke Nan

"Ummu Aisha ki yi hakuri komai na rayuwa mai wuce wa ne kuma da yardan Allah komai ya kusan zuwa karshe, ni babban burina kar yaran nan su ji wannan zan cen don hankalin su ta shi zai yi."
       Hawayenta ne suka ci gaba da surnanowa a idonta, sharce hawayen ta yi ta ce.

"Haba Abban Baseera yanzu haka za mu zuba ido ba za'a ɗauki mataki ba? Wannan gurin shi ne madogaranmu, shi ne farin cikin mu!.
     Ta karashe maganar da surnanowan hawaye, janyota jikin shi ya yi sannan ya ce.

"Waye ya ba mu aron gurin?"
          Ta ce.
"Allah."  
      Ya ci gaba da cewa.

"To ki ɗauka yadda Allah ya kuma ya karbi abin shi don haka muna zaune zai ƙara bamu wani, don haka mubar wa Allah kawai, don Allah kar ki bari yaran nan su san da wannan maganar."

"Amma Malam ya kake ganin za mu yi da Baseera? Ka san halinta kasan yadda take ji da sana'ar na ka ma, ta na raina abin da ka kawo gidan nan, balle kuma yau a wayi gari babu abin da zamu saka a bakin salati.!"
      Cewar Umma

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un!!!"
      Abin da Mai nani yake ta maimaitawa ke nan, har ya samu nutsuwar zuciyarsa.

  BAYAN SATI UKU

Annurin fuskarta ka ɗai ya isa ya shaidar maka da tana cikin farin ciki mara misaltuwa, Chocho ne a gefen hagunta hannunta maƙale da na shi sai murmushi yake yi, ɗayan hannun shi kuma cek (Cheque) ne daya rubuta mata sakamakon farin cikin da ta sa ka shi yau, direba ya kira da sauri ya ƙaraso gurin da mota ya buɗe mata gidan baya, ta zauna tare da zuro ƙafarta ɗaya waje cikin harshen Nasara ta ce.

"Choco you made my day and i will never ever forget this day in my entire life. Am blessed to have you as my love."
   (Choco ka faranta min wannan ranar kuma ba zan taɓa mantawa da wannan ranar ba a rayuwata gaba daya, na yi murna da na sa me ka a matsayin masoyi.)
      Murmushi ne ya suɓuce masa sannan ya ce.

"Oh! Common babe just chill, we made our day and besides who's blessed among us? Am i, because i am supposed to say that."
      (Ah! Haba 'yan mata ki yi farin ciki, mun faranta wannan ranar sannan wa ye yafi da ce wa ya ce hakan a cikin mu? Ni ne saboda ni ya da ce na ce hakan.)

"Oh! Really?"
    (Ah! Da gaske!)
        Cewar Baseera ta yi maganar haɗe da murmushi har sai da wishiryarta suka bayyana.

"Yes baby!"
     (Eh 'yan mata)
           Ya bata amsa da mayaudarin murmushi.
 
"Chocho i have to leave because am running late, and you know this our oldest parents there will be starting asking were have you been? This and that."
      (Chocho ya kamata na tafi saboda na yi latti, kuma kasan iyayen mu na da, yanzu za su fara tambayar ina ka ke? Wannan da wancen.)
     Dariya ya yi sannan ya ce.

"Oh! baby you're big enough of all this is, you have to started doing what you want not what they want, you are a classy and unique baby. Babe you are big of all this, that's just it."
     (Ah! 'yan mata kin yi girma da duk wannan abin, ya kamata ki fara abin da kike so ba abin da suke so ba, ki na da aji kuma kin haɗu 'yan mata, 'yan mata kin girma da waɗannan abin, shi ke nan.)
          Shuru ta yi halamun maganar shi suna son yin tasiri a zuciyarta, ta yi saurin kawar da zan cen da cewa.

"Chocho zamu yi waya, ka kular min da kanka."
      Ta jan ye ɗayan kafar tasa a mota direba ya ja motar har zuwa kofar gidan su, tsayawarta ya yi daidai da tsayawar mai adaidaita sahu a kofar gidan su, bayan shi kawai ta kalla amma sai da gabanta ya yi mummunan faɗi.

"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un."
     Ta ambata a fili, tare da da fa kirji cikin ta ya ba da wani irin kuka.


_______________________________

Ku yi hakuri kun jini kwana biyu shuru, hakan ya faru ne sabo da lalacewar transformar unguwar mu, amma yanzu komai ya daidaita zaku jini yadda ya kamata In Sha Allahu.


Wattpad @Basira_Nadabo

Basira Sabo Nadabo Ce

NADAMATA! PART ONE Where stories live. Discover now