POST 19

87 15 6
                                    

Shawarar da ɗayan zuciyar take bata tabi saboda in har a ka rufe bakin Badar hankalinta zai fi kwanciya domin Badar ba razana ce a rayuwarta, amsa masa ta yi cewa

"Eh Malam kayi duk yadda za kayi don dai kawai bakinta ya mutu, ban damu da rashin aurenta ko rashin samun jikokin da zan yi ba ni dai bukatata ta biya kawai, saboda Sameer yana da yaran da zan kalla in kirasu da jikokina."
     Ƙuri ya yi mata da ido sa'annan ya fara sirkullensa kamar yadda ya saba cikin minti biyu Badar ta bai yana a madubin tsafinsa tana zaune da Al'kur'ani tana karantawa, da sauri ya rufe madubin tare da kallon Gimbiya Bilkisu ya ce.

"A yanzu babu mugun da zai iya kusantarta don ya cutar da ita sannan na lura 'yarki ba ta rabu wa da addu'a musamman na safe da yamma in ko har tana cikin kariyar Allah to duk tsubbun mutum ko sheɗancin shaiɗani ba zai taɓa iya zuwa kusa da ita ba, amma a duk lokacin da kika tabbatar bata da tsarki ki yi maza ki sanar da ni saboda a wannan lokacin ne kaɗai zan samu galaba a kan ta."

"Tabbas kullum za ka ganta da Kur'ani ko kuma littafin addu'oi tana karantawa, kai ko da silisilin dare ka je ɗakinta zaka same ta zaune bisa darduma, to amma in ta san wani ai bata san wani ba yanzu zan mai da hankalina kanta har saina gano ranar da take fashin sallah domin a raba ni da ita."
       Cewar Fulani Bilkisu. Malam ya ce.

"In ko kika yi hakan kin taimaki kan ki ne don ni bani da lokacin tsaya wa duba ranar da za ta yi fashin sallah don ba ke kaɗai bace wacce nake wa aiki, ki tashi ki tafi ina jiran kiranki in kuma ya wuce wannan satin."
      Sai ya yi shuru na ɗan lokuta daga bi sani ya ce.

"Abin da a ke gudu ne zai afku kuma karshenki da ni ba zai taɓa yin kyauba don mun yi sanadiyyar mutuwar salihin bawa, mai addini da yawaita azumi sannan tofin Allah ya isan da bakin da mutane suke yi a kan mu zai iya kama mu Gimbiya Bilkisa."
         Ta shi ta yi ta fita ba don bata da amsar da zata ba shi ba sai don gudun wani tashin hankalin da ba ta son a faɗa mata, da zuwan ta gida ta riski Badar na chatting a waya kusa da ita ta zauna tare da cewa.

"Badar 'yata yau kuma ina ƙungin naki na ganki ke kaɗai zaune a nan?"
      Saurin kallon Fulani Bilkisu ta yi domin har ta manta da Fulani Bilkisu na kiranta da wannan sunan amma sai ta kauda mamakinta saboda ta yarda da sauyin Fulanin a 'yan kwanakin nan tabbas ta tuba, tubar har kuyanginta sun san da sauya warta a 'yan tsakakkanin lokutan nan. Cewa ta yi.

"Mummy kin san ni ba cika son hidima nake yi ba kuma bana son naga mutane na wahala a kaina wannan dalilin yasa nake cewa suma suje su huta, domin suma mutune ne kamar ni kuma yadda nake son hutu haka suma jikinsu yake bukata Mummy."
     Harara ta aika mata a kaikaice sannan cikin zuciyarta ta ce.

'Tabbas ke kuwa kike bukatar kula war bayi domin nan gaba kaɗan za su miki rana a wannan lokacin kuma kika fi bukatarsu Badar, saina mai da ki abar kwatance a masarautar nan a yayin da ni kuma zamu ci gaba daga in da muka tsaya har sai na ga jikana ya yi sarautar garin nan.'
      Amma a fili sai cewa ta yi.

"Allah sarki 'yata 'yar albarka wallahi kin tabbata jinin Bilal Fu'ad saboda duk wannan ɗabi'un tasa ce, haka shima ba ya son ganin wani na masa hidima sai dai a fada ne kaɗai yake bari saboda mutanen majalisa shima a hakan da kyar ya saba har yake bari, kai duniya yau nice na wayi gari babu farin cikina wanda ya min so don Allah ba ya nan sun kashe min shi saboda giyar mulki ta ɗibe su, kai ba zan yafe wa kaina ba in ban ɗauki fansar abin da a ka min ba domin nice a ka ma wa Sarki Bilal mutumin kirki ne ga addini da son jama'a ko wani ɗa na shi ne.......!"
        Kuka ne ya ci karfinta Badar ma sai matsar kwalla take yi, kokarin tsayar da hawayen ta yi tare da sharce wanda yake surnano mata ta ce.

"Mummy don Allah ki yi hakuri har gobe mutuwar Abun tana yawo a jinin jikinmu amma babu yadda muka iya domin wanda ya fimu son sane ya amshi kayan shi mummy, kuma wallahi da Abun yana da sauran shan ruwa a gaba to fa ba zai mutu ba a wannan lokacin har sai lolaci da ranar da Allahu ya ɗiba masa, ki yi hakuri kawai mummy addu'a Abun yake nema ba kuka ba."
         Sharce hawayen ta yi sannan ta ce.

NADAMATA! PART ONE Where stories live. Discover now