POST 8

92 14 1
                                    

Tun ɗazu ake kiran wayar amma bata ɗauka ba saboda yau sarautar suna kusa kamar yadda ya raɗa mata sunan sarauniya Baseera, Umma ce ta juyo gefen da Baseera take kwance ta ce.

"Da kin san wulakanci zaki musu tun farko ba ki basu numbern wayar ki ba, haba tun yaushe bawan Allahn ke kiranki amma kinki ɗagawa don tsabar wulakanci, to in ba za ki ɗaga wayar ba ki kasheta don tana cika min kunne kuma ta hanani bacci cikin kwanciyar hankali."
      Gyara kwanciyarta ta yi sannan ta ɗauko wayar a in da ta jona caji kusa da ita, ta kara a kunne haɗe da cewa.

"Amma dai kasan wannan lokacin ba ya cikin lokutan da nake amsa waya ko.?"
      Daga ɗayan ɓan garen ne ya yi murmushi don dama yasan dole hakan ce zata fito a bakin ta, yaudararriyar murmushi ya yi mai sauti ya ce.

"Sarauniya Baseera ke nan har yanzu kina nan yadda na barki baki canja ba."
      Janye wayar ta yi daga kunnenta ta kara kallon numbern da ta kirata, tabbas in dai ba gizo idonta ke mata ba numbern Chocho ne da ta goge a wayarta, gyara murya ta yi cikin salon yaudaran ta ce.

"Chocho manyan gari dama har yanzu kana duniyar?"

"Ina duniya Babyna sai dai duniyar ta min zafi rashin ki tare da ni, ban taɓa sanin ke ce farin cikina ba sai da na rabu dake, kuma bawai na rabu dake ba ne sai don fushin da na yi dake, ke kuma girman kai ya hana ki kirani ki bani hakuri."
    Cewar Fahad. Ita ma murmushi ta yi sannan ta ce.

"Kamar yadda ka sani ne Chocho bana bawa namiji hakuri in har ban masa laifi ba, haka kuma ba zan taɓa sau kar da girmana a matsayina ta 'ya mace don kawai mu shirya da namiji ba. Amma kaima ai kasan dole na yi missing ɗinka sosai."
       Filo ya janyo jikin shi sannan ya ce.

"Tunanin ki ya addabi kwakwalwata har bana iya gane komai na duniyar nan, ki taimaka min da ɗumin jikin ki ko nawa ne zan siya."
        Ya riga da yasan weak point ɗin ta kuma yasan ba za ta taɓ tsallakewa ba, gefen da Umma take kwance ta kalla sannan ta juya zuwa harshen nasara ta ce.

"Kai kasan yadda nake jinka a zuciyata kuma babu abin da zaka ce ban maka ba sai dai abu guda ɗaya, Chocho a yanzu ba zan iya siyar maka da mutuncina ba saboda girman darajar ta, amma zan iya ba ka jikina akan farashi mai kauri in ka yarda."
      Murmushi ya yi don dama tarko ya ɗa na mata a wannan lokacin kuwa ko da karfi ne sai ya amsa abin da ya da ɗe yana lallaɓa ta ta ba shi amma ta na mishi yanga, cikin harshen nasara shi ma ya ce.

"Karki damu nima zan ta yaki killace mutuncin ki Babyna, in na aure ki zan fi ganin ki da daraja. Ni dai ki bani wannan damar kinji.?"

"Ba komai Chocho kaddara ma na baka damar amma ina kara tabbatar maka, iya ɗumin jikina kawai ban da mutuncina."
     Cewar Baseera

"Kar ki damu sarauniyata nima iya abin da kawai na nema ke nan, bayan shi bana bukatar komai a gurin ki."
      Cewar Fahad da muryar Baseera ya gama kashe mishi jiki, duk jikin shi ya yi weak. Ƙara narkar da muryarta ta yi cikin shagwaba ta ce.

"Chocho yanzu ina son jin alert saboda akwai abin da zan yi da kuɗI gobe."

"KuɗI ba matsalar ki bace sarauniyata yanzu zan turo miki."
       Cewar Chocho. Sun taɓa hira kaɗan har zuwa karfe biyun dare sannan suka kwanta. Washe gari Umma ta zaunar da Baseera a ɗaki bayan fitan su Abba ramfar da yake nanin takalma, ta ce.

"Baseera ki saurareni da kunnuwan Basira kuma ki nutsu kiji abin da zan faɗa miki,  ni uwace wacce take lura da duk motsin 'ya'yan ta, Baseeratu karki ɗauka ban san abin da ki ke yi ba ne, kuma karki ɗauka zaki yaudareni da turanci don cinma wata manufa na ki, ina son kiji tsoron Allah akan rayuwar ki wallahi ki sani duk abin da ki ka yi a waje ke ma za a miki. Mun barki kiyi duk abin da ki ke so haka kuma mun barki kina fita duk lokacin da kika ga damar fita, ni da Abbanki babu wanda ya taɓa miki iyaka akan yawan fitan da ki ke yi waje, to amma kiji tsoron Allah Baseeratu."
     Kirjin Baseera sai dukan uku- uku ya ke yi don yau kam kashin ta ya bushe, kuma babu bakin tsiwa. Da sanyin jiki ta ce.

NADAMATA! PART ONE Where stories live. Discover now