POST 20

89 10 0
                                    

A shashin Fulani Zainab kuwa zaune take abin duniya duk sun dameta , ga ta dai sarautar cikin shi ta taso amma ace wai ɗanta tal a duniya shi ya kasa yin sarautar da ya gada kuma jininsa ce bawai ha ye yayi ba, gyara kwanciyar ta yi sa'annan ta ce cikin zuciyarta.

'Dole ka yi sauratar da ta zame maka gado ba zan ci gaba da zuba ido ina taimaka wa Mai Martaba a na lulluɓe abin da ya zama dole ya bayyana. Har ni za a fi taƙama da sarauta bayan cikinta na girma har na yi aure sannan yanzu kuma ɗana ɗaya ace shi ne bai yi sarautar ba? Hakan ba zai taɓa saɓu wa ba dole abin da ake gudu ya fito fili ala barshi in mun haɗu a ƙiyama na bai wa Mai Martaba hakurin abin da ya faru amma ba zan ci gaba da zuba ido ana mana mulkin kama karya a kan abin da ɗana ne ya dace shi ba.'
       Takun takalmin shi ne ya janyo hankalinta zuwa gare shi da basmala ya zauna sannan ya ce.

"Yau ina Jamila na ganki ke ɗaya a zaune bayan nasan zaman ki shuru babu abinda zai haifar sai tunane-tunane.?"
       Cewar Yarima Ameer, murmushi ta yi sa'annan ta ce.

"Bayan Ubangijin Al'Arshi ya bani kai kuma na amsa da hannu biyu ai babu ni babu tunani a duniyar nan, in ma ka ganni ina tunani to bai rasa nasaba da mutuwar Mai Martaba da yazo mana farad ɗaya babu ciwon kai kawai sai wayar gari a kayi babu shi!"
      Ta karashe maganar da rawar murya hawaye suka surnano a idonta, hular da take kanshi ya cire sannan ya ce.

"Ni kuma a duniyar nan mutuwar Mai Martaba bai taɓa damuna ba kamar yadda lokaci ɗaya Yaya shi ma aka wayi gari babu shi. Sa'annan Umma ace wai rana ɗaya suka rasu, ban isa in ja da hukuncin Allah ba amma ni nasan da sannun su........."
     Saurin ɗaga masa hannu Fulani Zainab ta yi sannan ta ce.

"Ina raba ka da zargi Ameer domin zargi mugun kulli ne da baka iya kunce kanka ko da kuwa a kan gaskiyarka kake, na sha kwaɓarka a kan abin da ba ka da tabbacinsa domin inuwar mutane bai zame maka hujjar da zai sa kace wannan mutanen ba ne."
           Ya ce

"Amma Umma a wannan daren na zo miki da maganar abin da naji da kunnuwana kika ce babu ruwana al'halin ɗan uwana ne mafi kusanci da ni, yanzu ma so kike in zuba ido har a zo kanmu? Kamar yadda suka gama da Ummi? Saboda da zarar sun gama dani kema baki da sauran daraja a gidan nan, Don Allah Umma ki yi hakuri ki barni na kwatowa Yayana hakkin ransa da suka raba shi da shi domin Yayana bai dace ya mutu a yanzu ba, Umma ki duba fa tun ina yaro suka kashe shi gashi harna girma so kike in ci gaba da zuba musu ido akan abin da suke yi?!"
       Kuka ne ya ci karfinsa, Fulani Zainab ba ta hana shi yin kukan ba saboda kuka ma rahama ne a gurin dan adam. Sa'annan ta ce.

"Ka bani kunya Sarkin dake jiran gado ne da kuka har da hawaye shaɓe-shaɓe sannan ka fita kana taƙama a gari ai sarki da jarumta da juriya aka san shi da shi ba ragunta ba."
       Dariya yake yi yayin da yake sharce hawayen da suka surnano masa babu abin da ya ce ba wai don kuma ya rasa abin faɗa ba ne, daga haka hirar ta ƙare.

Wannan Ke Nan

Zaid duk yadda ya san zayyi  don ganin kafin Baseera ta dawo ya kammala komai don basu mamaki da kuma ƙara daraja a idon Daddy'n Baseera dake Italian, amma babu abin da ya a jiye da sunan tarin aure ko ɗan kunne naira hamsin bai aje ba. Habu ne ya zo ya taradda da shi zaune a ƙarkashin bishiyar dalbejiyar dake kofar gidan su ya haɗe kai da gwiwa, taɓo shi Habu ya yi bayan yin sallamar da ya kwaɗa amma babu amsa, kallon shi ya yi tare da miƙa masa hannu sannan Habu ya ce.

"Ka ga angon Baseera ba da kanka a sare ka koma gida ka ce da Baba Mai Faskare ya faɗi."
     Ya kyalkyale da dariya domin ya san ya tono Zaid ne, aiko bai gama tsagaita wa da dariyar ba Zaid yaja dogon tsaki sannan ya ce.

"Wallahi Habu ina gab da ɓa ta wa da kai muddin ba za ka daina kiran sunan Baba da Mai Faskare ba. Mstw!"
      Ya karashe maganar da jan tsaki. Murmushi Habu ya yi sa'annan ya ce.

NADAMATA! PART ONE Where stories live. Discover now