POST 17

77 11 2
                                    

Zaune yake cikin manyan kaya kalar sararin samaniya kafarshi tankwashe cikin ladabi ya sadda kai ƙasa nutsuwa da kamalarsa duk suka bayyana a lokaci ɗaya ya zama babban mutun mai cikar kamala, shirun da ya ji Mai Faskare ya yi ne na 'yan mintuna ya sa shi ɗago kan shi don tabbatar da zaman Mai Faskare ko kuma ya ta shi ya fita ne don shurun ya yi yawa, gwaron numfashi Mai Faskare ya sauke sannan ya ce.

"Yanzu kai Zaidu kana da kuɗin aure? Kuma kana da in da zaka a jiye 'yar mutane? Ko kuma kana da abin ciyar da ita ne? Ina son ka ba ni amsoshin tambayoyina Zaidu."
        Kirjinsa ne ya buga sannan cikin nutsuwa ya ce.

"Baba dama tunda ina aikin kanikancin nan kuma daidai gwargwado ina samun rufin asiri saboda a rana na kan yi gyara in samu dubu uku zuwa biyu, kuma na tabbata da ɗan wannan rufin asirin zan iya riƙe ta da kuma cikin gida ko da kuwa bani da shi sai taci duk abinda za a ci a gidan nan, saboda ba ta da girman kai ko raina abinda mutum yake ci sai ma girmama shi da mutunta arzikinsa."
     Shuru Mai Faskare ya yi na ɗan wani lokaci kana da ga bisani ya ce.

"Zaidu ba wai auren ne bana son ka yi ba sai dai ina hango abinda kai ka kasa hangowa saboda har yanzu zuciyana ya kasa aminta da auren, ba kasafai nake jin hakan a zuciyata ba sai in har abin babu alkhairi a ciki abu, amma zan yi kokarin mai da shi alkhairi saboda ku samu nutsuwa a rayuwar auren ku sai dai wani hanzari ba gudu ba, Zaidu ni bani da karfin taimaka maka a auren nan kana kallo faskaren ma da kyar yanzu muke samu saboda zamanin ya canja babu mai amfani da icce sai kayan wuta, zan dai taimaka maka da in da zaka tsuguna ɗakin da ke kusa da zaure ɗaya ɗaya ne sai dai yana da girma da faɗi zai isheku rayuwa kafin ka yi naka."
           Murmushi ne kwance a kan fuskar Zaid yana murnar ɗakin da a ka ba shi ko ba komai an rage masa wani hidimar.

'Na san ba za ta damu ba saboda ba ta ɗauki kan ta komai ba don kaunar da take wa talakawa zai sa ta yarda ta zauna a nan ɗin, kuma zan yi hakan ne don jefar tsuntsu da dutse ɗaya domin na san yadda Daddy'n su yake son ta in a ka ce mi shi a ɗaki ɗaya muke zai bamu gida a G.R.A na zamani wanda zamu yi rayuwa a ciki, sannan da sannu zai bani aiki mai tsoka nima in dinga zuwa Italian ina saro takalma kamar yadda yake yi saboda na san yana son ta kuma dole ya so abinda take so, da sannu sunana zai canja da ga Zaid zuwa Don Zaid a lokacin nima zan buɗa duniya ta sanni a dinga dama wa da ni a harkokin ƙasar nan kamar yadda a ke yi da mahaifinta.'
          Gyaran muryar da Mai Faskare ya yi ne dawo da shi da ga duniyar tunanin da ya lula, ya ce.

"Lafinka ƙalau kuwa Zaidu? Sai murmushi kake yi sannan ka kafe kujera da kallo kamar kana son gano maƙerin da ya sassaƙo iccen da a ka sarrafa kujerar.?"
        Sosa ke ya ya yi cikin jin kunya sannan ya ce.

"Ina murnar gurin zaman da ka bani ne saboda a yanzu gurin zamar shi ne mai wahalar a wannan lokacin, saboda ciki da falo sai ka ji an ce dubu hamsin in kuma sun saka ɗan matsatstsan bayi da kitchen a ciki kuma sai ya zama dubu saba'in ko tamanin, shi yasa nake murna da taimakon ɗakin da ka min har bakina ya gaza rufuwa."
  
"Yanzu har an kai lokacin da matsuguni ya yi tsada haka? Gurin da mutum zai zauna na ɗan lokaci ƙalilan shi ne kusan ɗari haka? A gaskiya zamanin nan na ku babu tausayi ko jin ƙan ɗan uwa, ke nan a yanzu in gemun ɗan uwanku ya kama da wuta maimakon ku taimaka masa da ruwa don kashe wa sai ku kai mi shi fetir domin ƙara hura wutar ko? Ai da wannan kuɗin sai ka samu gida mai ƙafa ɗari har da canji a kai amma gaskiya a na tsadar rayuwa yanzu."
         Ci gaba da hira suka yi a ya yin da Mai Faskare ke ƙara jaddada wa Zaid ba shi da kuɗin da zai ba shi ya yi aure a haka dai hirar ya ƙare.

Wannan Ke Nan

Duk wani shiri da za su yi na zuwa ƙauye sun gama har da Yaya Sani saboda shi ma ya dawo da ga camp sauran fara bautar ƙasar kawai ya rage masa, mai motar unguwar su ne suka yi wa magana a kan zai kai su har kofar gidan Sarkin Takalma da ke unguwar Mariri da ke Karamar Hukumar Kumbotso a Kano, ham (horn) yake yi ba yan idar da sallar asubahi da a ka yi da sauri Yaya Bilal ya fito haɗe da cewa.

"Ka ɗan ƙara hakuri mana Malam Dauda gamu nan fito wa yanzun nan In Sha Allahu."

"Ɗan boko don Allah ni dai ku yi sauri saboda yana yin hanyar kasan titin ne har yanzu gyara a ke yi fita nan shiga nan ne haka titin take to so nake muje da wuri don na dawo da wuri."
        Cewar Malam Dauda direba. Yaya Bilal ya ce.

"Na sani Malam Dauda yanzu cikin yardan Allah zamu fito ba tare da ɓa ta maka lokaci ba."
        Direban ya ce.

"To don Allah a ƙoƙarta ɗan boko."
        Sunan da suke kiran gidan Mai Nani ke nan gidan 'yan boko musamman da suka ga Baseera ta girma a gida kuma ba ta ɗauki kan ta 'yar Mai Nanin Takalmi ba. Ƙaton buhun tsaraba Yaya Sani da Yaya Bilal suka riƙo zuwa gurin motar Baseera kuma ta na biye da su a baya da wata ƙaramar buhun but ɗin motar suka rufe tare da shi ga motar, Malam Mamman ne ya zo gifta wa ta gurin su da sauri Abba Mai Nani ya yi mi shi sallama ya ƙarasa kusa da shi don ƙara ba shi hakuri a kan rashin biyan hayar da bai yi ba, Malam Mamman ya yi saurin washe baki haɗe da cewa.

"Haba Malam Bashir Mai Nani ai ni tuntuni gida ya fita a hannuna ya zama naka."
      Shuru Abba ya yi na 'yan sakwanni sannan ya ce.

"Malam Mamman ban gane abinda kake nufi ba yaushe gida ya zama nawa kuma a yaushe na biya ka kuɗin gidan? Kaina ya ƙulle Malam Mamman."
       Malam Mamman da dai ya ga Abba da gaske yake bai san da maganar gidan ba sai cewa ya yi.

"Ai autarka ranar ta zo min da wani ɗan farin yaro kyakkyawa a mota muka yi ciniki ya siya gidan kuma ya ce ya baka kyauta halak malak yanzu haka takardun gida sunan ka ne a ciki sauran wasu abubuwa ne kaɗan ya sa ka ga ban kawo maka ba amma da tuni na kawo maka."
     Tunda Malam Mamman ya fara magana jikin Mai Nani ya yi sanyi kallon Baseera ya yi da take tsaye a kofar motar cikin sanyin jiki, tunda Abba ya tare Malam Mamman ta san yau kashinta ya bushe don babu mai cetonta sai Allah Yaya Sani da Yaya Bilal ta san su kamar yunwar cikinta kiris suke jira abu ya ɓillo ta gefenta, Mai Nani ne ya dawo da sanyin jiki ya shiga motar ba tare da ya ce wa kowa komai ba, Yaya Bilal ne ya rufo gidan da kwaɗo saboda tun jiya Abba ya sallami mutanen layin sannan suka kama hanyar tafiya, duk farin cikin da Baseera take ciki ya kau saboda shurun Abba masifa ne don Allah ka ɗai ya san abinda ke zuciyarsa duk yadda Umma ta so janta da hira abin ya faskara har ta hakura ta yi shuru barci ya ɗauke ta. Abba ne ya kalleta da ya tabbatar da Yaya Sani da Yaya Bilal hankalinsu ya yi nisa cikin hirar da suke yi ya ce.

"Ban taɓa tuhumarki a kan in da kike samun kuɗi ba saboda na san tarbiyyar da na baki ba za ki watsa min ƙasa a ido ba, zuciyata da tunanina basu taɓa miki mummumar zato ba saboda na san mutuncinki yafi karfin kuɗi da kyale-kyalen duniya Baseera, amma a yanzu zan tambayeki ba wai don ina zarginki ba ko kuma ina mummunar zato ko tunani a kan ki sai dai don zuciyata ta samu nutsuwa a kan ki Auta, ina son ki faɗa min in da kika samu kuɗi har kika siya min gida.?"
      Tunda Abba ya fara magana kirjinta ke buga wa jikinta ya yi sanyi tare da tsanar rayuwarta gefe ɗaya na zuciyarta na kara tir da watsi da tarbiyya da yardan da iyayenta suka mata, yanzu me za ta cewa Abba? Da wani kalma zata kare kanta da wani bakin za ta buɗe ta cewa Abba Chocho ne ya siya musu gida? Bayan babu wanda ya san Chocho a gidansu wata kalma za ta yi don kare kanta a gurin mutumin da ya yarda da ita? Yarda da tarbiyyar iyayena da suke min ya ta shi a banza ke nan? Allah ka kawo min a gaji cikin gaggawa. Mai Nani ne ya katse mata tunaninta da cewa.

"Amsarki nake jira Baseera kin barni cikin zullumi ina son ki faɗa min in da kika samu kuɗi har kika siya min gida Baseera.?"
      Ya kara mata tambayar babu wasa don har yana yin fuskar shi ya canja.


_______________________________

Readers ku taimaka wa Baseera da amsa don kanta ya ƙulle. Ina jiran amsoshin ku. Sannan ina bukatar shawarwari a kan labarin nan ta numbern ta please.

My Wattpadians ga kyautar chapter naku ne ku kadai, ina jin dadin comments dinku. Na gode

Wattpad @Basira_Nadabo

Basira Sabo Nadabo Ce.

NADAMATA! PART ONE Where stories live. Discover now