POST 6

87 16 2
                                    

Yau kwana uku ke nan rabon ta da Chocho ko da kuwa a waya ne, kuma ko da ta kira ba ya ɗaga wayan tun abin yana damunta har tazo ta sa ke kamar ba ita ba, yau ma zaune ta ke bayan ta dawo daga gidan su Haima da ke Malali a hanyar dawowarta ne ta haɗu da Zaid. Zaid saurayi ne ajin farko kuma dai-dai muradinta na shiga kawaye kuma na zuwa bikin girma, murmushi kawai take yi na farin ciki da farko gidan su Haima ta nuna mishi a matsayin gidan su, sai daga baya ta ce masa tana zaune yanzu a gidan kawun ta da ke Hayin Rigasa, saboda a cewar ta tafi son zama kusa da talakawa don rayuwar su yana birgeta, Umma ce ta yi tsaye tana kallon ikon Allah saboda murmushin yaki ci yaki cinyewa, ta'ɓo ta ta yi tare da cewa.

"An ya kuwa kina da lafiya ko dai in kira mai nani ne?"
    Turo baki ta yi sannan ta ce.

"Ni lafiyata ƙalau kuma Umma kullum sai kince mai nani sama da dubu a gidan nan, ni wallahi na tsani inji sunan.!"

"Au iye yanzu sunan mai nanin kika tsana Baseeratu? Gaskiya na fara yarda da maganar Innarki Lamingo da ta ce, shafin aljanu gare ki kuma wallahi sai yanzu na fara hango gaskiyar maganar ta."
     Cewar Umma

"Ni dai wallahi lafiyata lau kar a wani ƙaƙuba min aljanu ina zamana lafiya, kuma ni gaskiya Umma ki daina ce min Baseeratu, bayan duk hakurin da na yi nake amsa sunan Baseerar ma sai an kara da tu a karshe. Ai da gidan masu kuɗi na fito wallahi babu me samin wannan sunan sai dai sunan 'ƴan gayu!"
      Ta yi maganar da zubar hawaye a idonta, Umma kuma tausayin ƴarta ne ke ka ma ta don tabbas aljanun ne da ita.

'In ban da aljanu ya mutun zai ƙI sunan sa mai daɗi da ma'ana sannan kullum maganar ke nan ƴaƴan masu kuɗi, gaskiya dole Malam ya tsaya tsayin daka akan wannan lamarin, Allah sarki autana ko sune ma suka hanaki aure sai ɗan mai kuɗi?'
       Idon Umma ne ya cika da kwalla na tausayin halin da Baseeratu take ciki, ya yin da take maganar zucci.

Wannan Ke Nan

Zaid saurayi ne kykkyawa na bugawa a shafin farko na jarida, sannan ɗan matashi ne da ke ji da kan shi gurin yaudara da ƙarya ga ƴan mata, ba kowa ba ne shi fa ce ɗan Malam Haladu mai faskare, su goma sha biyar ne a gidan kuma duk cikin yaran shi ne kawai ya yi karatu zuwa karamar sakandare (ss3). Tun da ga lokacin karatu ya tsaya bai ci gaba ba sai gyaran mota da mai faske ya miƙa shi gurin abokin shi, da kyar ya ke zuwa amma da ya fuskanci ƴaƴan masu hannu da shuni su ke kawo motocin su don gyara, wannan shi ne dalilin da Zaidu ya mai da hankali gurin gyaran motan kuma duk gurin babu wanda ya kai shi iya gyara, shi ya sa yaran ma in sun zo su ke ba shi gyaran motocin su, zaune ya ke da abokin shi Habu suna hira kamar yadda suka saba, Zaid ya ce.

"Kai alaji yau na yi babban kamu kuma ga dukkan alamu yarinyar ta afka tarkona yasin."
    Cewar Zaid da yake bawa abokin shi labarin haɗuuwar su da Baseera, abokin ne ya ce.

"Zaid sarkin yaudara yau kuma wata abar tausayin ce ta faɗo tarkon ka? Don wallahi har tausayin ka nake ji a lokacin da za a rama maka abin da ka yi wa sauran ƴaƴan mutane. Kuma wallahi kamar yadda nake faɗa maka ne a kwashe-kwashen ka sai watarana ka kwaso mai irin halinka wallahi."

"Tsaya Malam idan har ba za ka iya addu'a ba to kaja bakin ka ka yi shuru don Allah, ya za a yi kullum in na kawo maka magana sai kamin baki ne, wai ubana ne kai da har za ka yi tunanin bakin ka zai yi tasiri a kaina? To wallahi bari kaji wannan dai na yi kamu kuma na cafko mai tsoka, don iyayen ta a tsakiyar Malali suke ita ce dai ta zaɓi yin rayuwa cikin talakawa, don haka Malam rike wa'azin ka don a yanzu kam ba zai yi amfani ba wallahi Habu."
       Zaid ya yi saurin amsar zan cen cikin nuna ɓacin rai. Tausayin Zaid ne ya kama Habu don yasan Zaid tun yaranta, tare suke komai kuma duk fushin da Zaid zai yi na ɗan lokacine zasu shirya tun kafin su tashi a majalisar na su, sai dai kowa da halin sa Zaid irin yaran nan ne masu ƙarya da son abin duniya, Habu kuma ya tsaya in da Allah ya ajiye shi. Habu ne ya girgiza kai sannan ya ce.

NADAMATA! PART ONE Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora