PATCHED UP!!

1K 69 1
                                    

SANADI NE

KHAIRAT UP https://my.w.tt/BePbGnWUzX

TAQABAL MINNA WA MINKUM.

Ina ma kowa da kowa barka da shan ruwa ubangiji Allah ya karbi ibadun mu ya amsa mana bukatun mun na alheri amin summa amin, kuma ina muku fatan alkhairi da barka da sallah, Allah ya maimaita mana amin.

Pg 54

Tashi muje kiyi musu sallama gidan mu zamu tafi.
Tay narai2 da idanuwan ta yaya makyn a halin da ake ciki zamu tafi?.

Lallai ma ke din nan naga alama baki da imani da tausayi.

Ta waro idanuwan ta waje, yaya me na ma kuma?

Hararar wasa ya mata ya mike ina jiran ki a falo, ki hanzarta pls ya fada yana marairaice fuska.

Wallahi yaya na kunya nake ji
To waya ja?kina zaman2n ki a gidanki kika je wata ta zuga ki tay brainwashing dinki kika bar mijinki , kika bar martabar ki ae wallahi wayon ki na banza ne.

Tay sunkuyi da kai kasa alamun kunya , tace kayi hakuri kaji ka daina tuna mun dan allah kana sa ni naji kunyar ka da kunyar kan ka wlh.

Tashi ki kimtsa zanje na fadawa hajiya zamu wuce tare.

To ta fada a sanyaye ta mike ta soma hada kayan ta a gu daya.

A falo kuwa famiyn Omar na jimamin abunda yake faruwa kuma anyi2 mummy ta fadi laifin ta taki. Makyn ne ya tsinkayo muryar mummy na ce ai hajja burin hajia amina kam ai ya cika yau dama bata Kaunata kowa ya sani kums ita ce sanadin rabuwa ta da omaru amma ba komai allah se ya saka mu.......

Kasa hakuri yayi ya numfasa sannan ya tofa a tsanake bada fada ba ko tashin hankali ko wani alamun yana cikin bacin rai duk da yana tare da bacin ran kuwa kada ki soma saka hajiyr mu a maganan ki ae kowa yasan mugun halin ki kuma da zasu ji me kika aikata da sun miki hukunci fiye da wadda uncle omar din ya miki and daga yau se yau babu ke babu shiga hurumin hajiyarmu dan zan manta cewa ke din mahafiyar khusm ce kuma kin taba kasancewa matar uncle dina.

Hajiya amina ce ta bata rai duk da taji sanyi s ranta , kai makyn bana san rashin kunya jeka inda zaka.

Eh dama zaki fadi haka kin koya wa danki raina manya zski zo kina mun buyagin karya da wofi kaje ksi kuma duniya ce...

Hajja ce ta dakatar da muhawarar ta hsnyar daka musu tsawa yayin da makyn ya fita daga falon.

Hajja ta cigaba, to dukkan abunda ya faru ba haka aka so ba sedai haka allah ya rubuta ke mummyn su khsam ki tashi kije driver ya kai ki gidan ku tunda dai abu har ya kai da anyi saki bani da yadda zan yi amma kam ba haka aka so ba.
..

Hajja nikam ba inda zani zama daram dan na ajiye muku ya'ya har uku dole a bani daki zama daku dole ne wlh.

Dariya ma ta bawa hajjar ta ce shi kennan munji za a baki daki guda dal
Hajja ban katse miki ba, ni bazan bata ba bana kaunar ganin ta ko kadan a cikin rayuwata wannan matar da kike gani annoba ce wallahi annoba ce duk inda take sharri ne a gun babu alheri a gun aini hadina da ke kddara ce wallahi nagodewa Allah da ya kasance ya'yana basu bi ta gurbataciyar hanyar ki ba

Omar yanzu ni kake kira da sharri? Ka manta kaunar da nake maka? Tun muna yara, na haifa maka , na aurar da su , na baku kulawa sleflessly amma yau saboda laifin da be taka...

Ta kasa karasawa saboda kukan da ya sarke mata ta dinga yin sa .

Umma ta dafata ai a wulakance ta fusge ta zabga mata harara, kada ki kuskura in ma ina neman taimako a duniya kece last dazan so ki taimake ni a rayuwata mayya er mayyu er matsiyata me kwacen miji kin raba ni da miji na kinji dadi kada ki murna dan kuwa yadda ya sake ni kema haks ze miki butulcin d'a namiji.

Mamaki ma ys hana hajja magana se abbi ne ya ce ke zuwaira tashi ki tafi gidan ku zan kira baban ki yanzu na masa bayanin rashin kirkin ki, jeki lada ya isa iya shekarun ma da muka yi dake mun kokarta jeki allah ya hada kowa da rabonsa.

Kallan abbie din kawai take ta mike cike da kunya da alkawarin rama wulakancin da aka mata, sumi2 ta bar gidan ko drivern bata nema ba ta fita.

Makyn na ganin wucewarta ya jijiga kan sa ya nufi cikin gidan.
Samin su yayi suna tattaunawa a kan maganar da jajanta mugun halin mummyn su khusam.

A kasa ya zauna ya tankwashe kafarsa hajja hajja manyab gari wae me kike ci ne na ga me makwan ki dinga ragwabewa a matsayin ki na tsohuwa se naga kina zama fresh kina wani murmurewa.

Murmusawa tayi ta ce to mal.muhammadu ya ranka ai mu da kake ganin mu kiwon mu na daban ne , a zamanin mu komai me lafiya ne ba wannan kayan zamanin naku me saka ciwuka da taki na bature ai dole ka gan mu daban jikin mu ba irin naku ba.

Dama haka kuke kare kanku zamanin ku kunfi kowa lafiya blablabla muma dai garau muke komsi tar muke ganin sa.

Hajja zamu wuce fa yau
Ina, kai da wa kuma?

Hajja ni da mata ta mana

To fa matar da bata da lafiya ina zaka da ita?

Hajja ki daina mun haka baki san me yake wakana ba kawai zan wuce da ita ne dan nima ba dadewa zan yi ba jibi zan koma kinsan yanayin aikin mu.

Duk da haka da dai ka barta kaga ciki ne da ita ga complications kuma kace zaku yi tafiya a mota me nisa nikam ban aminta ba gaskiya.

Hajiya amina tace hajja ki barsu su tafi in yaso suyi booking flight su bi ta jirgi su koma abujan ta jirgi hankalin ki se ya fi kwanciya ko?

Shi kennan Allah ya kiyaye ku ya kai ku lafiya.

Amin aka amsa.

Bara na je na ce ta hada kayanta.

Ae na fada mata ta ma hada kayan wucewa kawai zamu yi ni kam.

Au ai ce mun zaka yi kun gama tsara abun ku en zumudi to naji nima ku harhada naku ya naku ku bar mun gidan.

Aka sa dariya
Kedai hajja kina kishi ne nafi ji da amarya ta zan barki to ya zaki ki zama tsohuwar yayi.

Fillon kusan da ita ta jefa masa, ya mike yana dariya ya nufi dakin da rabi'a take ta gama hada kayan ta bata ankare dashi ba taji ya rungumo ta ,ta baya ya dan yi kissing din gefan wuyan ta haba MY LURV kin kasa gama hada kayan ki ni duk na matsu naji lafiyan babyna da taki .

Duk kunya take ji haka ya juyo da ita suna facing junan su ya dago habarta dan su hada idanun su gu daya

Rabi'a ki daina jin kunya ta ki daina cutar mu ki zage ki maidani dan lelen ki , ki nuna min kulawa da soyayya, pls ina hadaki da Allah ki taimaka ki cire kunyan dake san shiga tsakanin mu, pls my lurv,.

Sunkuyi tayi da kanta tana murmushi.

Salama aka yo hade da knocking
Bata rai yayi ya amsa ya ce a shigo.
Wata me aikin hajja ce ta shigo hannun ta dauke ds tray shaqe da lemu da ruwa me sanyi da wasu cookies a cikin wani bowl, gefe kuma tablets ne.

Ta ajiye a kan tebur tana gaida su suka amsa sannan tace yallabai hajja ce tace a kawo muku lokacin shan maganin ta yayi,kai kuma ka sha lemun me sanyi.

To mungode asiya!

Ta dan rusuna hade da juyawa ta bar dakin.

To mrs.makyn zauna mu bi umarnin er tsohuwa mu lallaba mu fita daga gidan nan wlh kar ayi abun kunya a gidan hajja.

To ai nima so nake mu je dan naga alama kunyan ka ta kare zaka iya yin komai.


  SANADI NEWhere stories live. Discover now