chapter 15

1.1K 76 0
                                    

😭SANADI NE!😭

NA KHAIRAT UP

vote@wattpad khairi_muhd

               15

"shi ko khusam hankalin sa a tashe ya koma dakin sa, zauna wa yay bakin gado ya dau wayar sa ya nemo number aysha! tana ta ringing ba a dauka ba sau hudu yana kira ta taki dauka yay tsaki ya bata rai ya jefa wayar a kan gado."

"aysha na fitowa daga bandakin ta dau wayar ta, tay mamakin ganin num da ta dade bata ga kiran sa ba tsaki tayi ita ma kamar ta maze sai ta kasa ta kira sa."

"yana ganin num ya dauka da sauri."

_ayshat haba,tun yaushe nake kiran ki kira nawa na miki haba ayshat!_

   _sai yanzu zaka kira ni ? me zan maka?_

_ayshat me hakan? zaki ce mun wai me zaki mun?_

_yo me zan ce maka ta zubawa wayar harara tamkar yana kallan ta_

_kina hararata ne ko ? sena baballa ki tukun sokuwa_

_hah, ikon Allah yau naga masifa?_

_to ni dai a bar maganar kina ji ko wai maganar da daddy ya fada gaske ne._

_eh haka ne ya ranka.😂 ta kyalkyal ce masa da dariya._

_haushi ya kama sa ya ce ayshat ki saurara mun fa kina ji na ko to yanzu ya za ae?_

_da me fa?_

_ki gane mana_

_hehe sannu ya jikin naka? ae nay nisa bana jin kira aji na ya wuce da haka na ...._

_ke dallah can da na ce miki mu jone ne? nifa ina tambayan ki ya zaki hada ni da rabi magana zamu yi da ita naji wayar ta a kashe._

_hah ta bude baki cike da mamaki da takaici ta kashe wayar_

_dariya yay shima tsokanan ta yake yi._

_tura mata text yay_

   _banda abun ayshat ae khusam sai ayshat.tsakanin mu ae tsohuwar alaka ce cool down babes_

_dariya ta yi da taga sakon ta ce se na wana ka wlh_

_tura masa tay ita ma_

          _maye na kawai ni bana yi kwalelan ka a kai gaba._

_ay karya kike ina nan zuwa garin naku gobe insha Allah_

_murmusawa tay ta shafa mayuka masu kamshi da dadi._

      ❣❣❣❣❣  

*katsina*
*(bugaje)*     

"umar da wan sa mubarak da abbie suka je neman iri a karo na biyu"

"hannu biyu2 suka amshi dangin umar aka dama musu fura aka nema masu kayan marmari suka amsa da murna ba kyama."

"umar ya gyara glass dinsa ya fara korawa yayan kulu jawabi"

    " _nasan nime laifi ne a gurun ku kun mun hallaci,kun sa ni a inuwa, baku kyamace ni ba, amma na saka muku da tsiya ku yafe mun dan Allah._"

     _abbie ya ce am malam mamman ni mahaifin umar ne kuma abunda ya faru kaddara ce kuma SANADI NE , saidai Allah yana san masu yafiya nima ina me baku hakuri a kan abunda ya muku kuma na hukunta shi."

" _malan maman ya gyada kai cike da kunyan dattijon yace dan Allah ka daina bani hakuri kai babba ne kuma mun riga mun hakura mun yafe masa mun yarda da kaddara da kuma uzurin sa.kawai dama haushin mu daya guduwar da ya yi ya bar matar sa da er sa amma yanzu alhamdulilah mun san dangin rabi na uba._"

" _haka ma yaya mubarak ya bada hakuri kuma ya fada masa kudirin su na neman auran hauwa'u_"

"malam maman ya ji dadi sossai amma ya ce dasu se ya tambayo hauwa saboda a fita hakkinta."

"haka ne inji abbie."

"ke hauwa fito kiji abun mamaki "

"tana daki ta fito"

"iyayen umaru ne suka zo neman auren ki a karo na biyu."

"mamaki ya cikata ta ce gaskiya nikam ban jin zan koma gidan sa."

"hauwa haka kike so ayi?"

"eh"

"ya juya ya fita daga      gidan ya sanarwa su abbhie abunda ta ce."

"abbie yace banga laifin ta ba ina san a mun iso nayi magana da ita."
"tsam malam mamman ya tashi ya koma cikin gidan ya sanar ma kulu bata wani jima ba ta fito tsakar gidan."

"a kan tabarma ta samu abbie ita kuma ta tsuguna a kasa, ya ce hauwa tashi ki zauna tashi kinji?"

"kanta a kasa ta ce uhm'uhm hakan ma ya yi"

"to hauwa'u naji sakon ki kuma banga laifin ki ba ko wa aka ma abunda umar ya miki ze ki shi, amma, ina san ki san wani abu guda daya ita rayuwa er hakuri ce kuma Allah yana tare da me yafiya ki tuna fa shi kan shi muna masa laifi yana yafe mana to mu su waye? ki tuna da er ki da zaman da kuka yi tare ki tuna irin san gaskiya da kika masa a baya wanda har a yanzu kina masa. kar ki manta shi fa hakuri da masoyi shi ne soyayyar in makiyin ka ne ae kadamar masa zakai. ba ina baki hakuri ba ne saboda umar da na ne ina baki hakuri saboda ke din ya ta ce.kin fiye mun umar ma wallahi dan kin raina mun jikata kuma kin rike amanar kauna na yaba da hallayar ki da kyawun dabiun ki"

"jikinta yay sanyi ta ce abbie na yarda ta mike ta koma daki.)

  SANADI NEWhere stories live. Discover now