chapter 31

886 63 1
                                    

SANADI NE

KHAIRAT UP

F.O.W

Vote@wattpad khairi_muhd

               31

a kid'ime ta tsuguna gefan sa ta ce subahanali, yah makyn ...innallinalahi yah makyn dan kayi hakuri wallahi na tuba na bi Allah na bika , ina san ka ka daina cutar da kan ka 😭. bama jinta yake ba dan jiri ne yake deban sa ya fincike hannun sa cike da zafin nama ya nufi dakin sa da karfi ya doko kofar har cikin hantar ta taji dukar kofar.

direct bandaki ya shiga ya kunna ruwa a fanfo ya sa hannun sa ya saki ruwan a kai yana wanke jinin, ya fito ya bud'e drower ya dauko first aid box ya dauko hydrogyn da auduga ya na shafawa a ciwon duk ciwon da yake ji haka ya daure ya sa bandage ya rufe ciwon.

a gun ya baje ya saki ajiyar zuciya yana jin wani irin d'aci a ran sa hakika san maso wani koshin wahala ne ya yanke wata shawara ya mike ya dauko biro da takarda ya yi rubutu.

ninkewa yayi ya mike ya fita a bakin kofar ya ganta a zaune ta hada kai da gwiwa tana kuka ya mika mata takardar hannun ta na rawa ta karba tana san jin karin bayani.

ya ce da ita ki karanta na baki yancin kan ki shawara ya rage naki ya koma dakin sa ya sa sakata.
 
      cewa take a ranta na shiga uku me yake nufi ya sake ni? bazan iya karantawa ba zan lallaba sa har se ya janye sakin da wane ido zanga hajiya da umma ta? me zan ce musu saboda mijin er'uwa ta na kaso aure na? innallillahi wa inna illahir raju'un ta dinga maimaitawa a sukwane ta mike ta nufi hanyar dakin ta kan gado ta fada tana jujjuya takardar dake hannun ta tama kasa budewa kuka kawai take yi wayar ta na ringing amma bata iya dauka ba ita ta kanta take bata waya ba.

bacci dai se barawo ne ya sace su badan sun so ba sedan shi barawo ne.
duk asubancin da ta yi a tashi seda ta samu baya gidan hankalin ta ya kuma tashi. da kyar tay wanka ta sauya kaya ta shiga kitchen ta dafa indomie dan yunwar da take ji ba kadan ba ce ba. tana nan zaune jugum ta na jiran tsammani taji ana bugun kofa daga waje.

isarta keda wuya ta ga mummy a kofar gidan ta wanda ta cika da mamaki da tashin hankali haka ta daure tana fara'a ta mata iso cikin gidan a fridge ta dauko ruwa da lemu da cake ta kawo mata.

mummy ta dinga bin gidan da kallo dan ya mata kyau ga kayan dakin ta me kyau sun mata kyau ta tabe baki a ranta tace gaskiya ne umar ya zuba ma er talakawan nan daula.

da murmushin karya ta sha ruwan ta dan ci cake din bayan sun gaisa da rabi.

nasan kina mamakin zuwa na gidan ku ko?

uhm um dadi ma naji wallahi

to madala dama ba komai ba ne illah nazo miki ne da wani batu me girma da kuma cigaban ki.

to mummy bismillah

youwa , nasan kina san muhd kuma nasan ba kya san makyn haka ne?

eh ta fada jiki a sanyayye.

to dama nazo miki da wata mafita wadda zata amfane mu ni da ke dan kuwa duk jirgi daya ne ya kwaso mu dan bana san auran nas da muhd na fi santa da makyn to me ze hana mu raba auran ni da ke ?.

rabi tayi jim tana kallan mummy tana mamakin shin wannan wacce irin uwa ce? wata zuciyar ta ce da ita ke ai cigaban ki ne zaki auri masoyin ki. wata zuciyar ta ce kada ki zama jahila mana ta ina zaki iya auran mijin er'uwar ki bayan tana da rai?.

mumy ta katse ta nasan me kike tunani ko haramun ne to kar ki manta shi so ae so ne kuma san kai yafi nidai zan baki lokaci ki yi tunanin magana ta idan kin shirya ki kira waya ta ni zan dora ki a hanyar da zaki rabu da auran alakakai.

to mummy nagode

to ina jiran wayar ki

tana fita ta ce shegiya se na raba auran nan naki saboda na tsane ki na tsani uwarki da farin cikin ki.

wuni zur tayi tana tunanin maganar mummy kuma tana tuna cewa fa makyn ya sake ta kawai ta bi maganar mummy saboda karta samu makyn ya maida ta dakin ta

eh hakan za a yi ta dau waya ta kira mummy.

mummy na yarda da shawararki.

alhamdulilah to kina jina?

eh

kiyi kokari ki kaso auran naku

ae ya sake ni jiya

😳😊 amma naji dadi barkan ki to kina ji na?

eh

...ta mata bayanin me zata yi  ki yi fa

to zanyi nagode.

to er albarka se anjima se na ji result din kuma.

to.

to jama'a me mummyn ta kitsa mata?

me zata yi?

muje zuwa

kuna hakuri dani bisa rashin posting kamar da nagode.

  SANADI NEWhere stories live. Discover now