"tsugunawa yay ya gaida su"

"a cikin su babu wanda ya amsa masa gaisuwar sa sai ma zallar bakin ciki da bacin rai da ya gani a idan su."

"a sanyaye ya ce dasu"
       "ku mun afuwa nasan ni me laifi ne a gare ku gaba daya amma ni din dan adam ne ajizi ne ni kuma na amsa laifi na wanda kaddara ce kuma na amshi kaddara ta a haka se dai ina neman afuwar kin sanar muku tun a baya duk da aure na da na hauwa'u *SANADI NE* kuma rabo ne na diyar mu rabi'a wadda na cuce ta da gatan ta na maida ta marar galihu marar asali wannan shi yake ci mun rai ba kadan ba. a yanzu na yarda da komai na duniya me wucewa ne kuma darasi ne ga ko wanne dan'adam."

         "ya juya ya kalli rabi ya hade hannayen sa 🙏🏻 ya ji wasu hawaye sun zubo masa yana neman afuwar ta. "

"ita din ma zuciyar ta ce ta karye taji ta saki kuka ta mike ta sauke masa hannayen sa ta ce dashi."

   "kai mahaifina ne be kamata kana mun haka ba ni zaka yafewa dana gaya maka maganganu marasa dadi ,ka yafe mun na manta cewa iyaye ba abun wasa bane su kuma duk kyan takalmi se an sa shi, haka zalika ba a canjawa tuwo suna a  tuwon dai ze tsaya na yafe maka nima ka yafe mun saidai bazan biku ba zan zauna a gun hajiya saboda na samu kusanci da ummata."

"duk da ba haka yaso ba hakan ya hakura ya ce ba komai ina san na fada..."

"dakata abbie ya fada masa kai a ganin ka Allah ze barka cutar da baiwar sa da kayi? to la shakka se ya mata sakaya matukar bata yafe maka ba kuma kayi gagawar zuwa da en'uwa na a maida auran ku gobe ba wata ran ba saboda hauwa'u mace ce macem ma ta arziki er aljanna wadda ta damu da kai ta yarda da kai ta aminta da kai ta ki yarda cewa yaudarar ta kayi idan irin wannan matar mara san duniya da abunta ta kubuce maka ka shiga uku kuma ka sa ta daina yarda da soyayya."

"hajja ta ce ae dama haka dan'adam yake ka masa rana ya maka dare!"

"dama abbie maganar da nake kokarin fada maka kennan cewa zan maida hauwa dakin ta."

"hawayen murna suka zubo ma rabi da godewa Allah saboda ta samu zata ji ummata a tare da ita koda yaushe."

"hajiya ma taji dadi ta dinga addu'ar fatan alheri koda zasu tafi hajja rike takwarar ta tayi wai zata kwanan mata biyu. ae nasreen ma ta cafke tace nima zan zauna wlh haka ma khadijat."
❣❣❣❣❣❣

"sanye yake cikin wasu kananun kaya wando da riga kan shi sanye da hula me kyau wadda ta rufe masa kunuwan sa , idanun sa boye cikin wani arnen glass brown in colour hannayen sa sanye da bakar safa wadda ta rufe tafin hannun sa. agogon hannun sa rolex ne  da takalmin sa na brand din jimmy coo,.kan wani tebur yake a zaune yana dadana laptop din sa hankalin sa duk yana gun abun da yake yi gefan sa cup din coffe ne da chips a gefan sa da kaza rabi a gefen chips din. "

"kamar daga sama ya jiyo maganar wata matashiyar budurwa wadda shekarunta baza su wuce 28 ba fara ce doguwa er siririya tana sanye da arabian gwon ja tayi rolling fuskar nan ta dau make up ga space an maka fari me kyau tana taunar cingum ta zauna a kujerar kusa dashi."

"har a lokacin be dago kan sa ya dube ta ba sai ma kaimi da ya dada bawa aykn da yake yi."

"am MAKYN baka gan ni ba ne?"

"tamkar da dutse take magana hakan ya mata shariya."

"hakan be sa ta zuciya ba, ta ce da shi MAKYN kenan duk wannan miskilancin naka burge ni yake wallahi me makon ya nesanta ni da kai kara kusantani da kai ma yake yi. i just love ur attitude da style din ka wallahi ka hadu ka mun 100% 😄"

"tamkar wata wawuyi haka ta dinga zuba ba aji ba zuciya."

"uhm ya ma sunan ki?"

"bata ji haushi ba ta ce IHSAN manta sunan ka ke?"

"yeah mantawa nake saboda ba kya gaba na  bana san mace ma magana,mara aji,mara kamun kai,me cusa kai, me bin saurayi, kuma ni na riga da na bawa wata amanar zuciyata and if u dnt mind please ki bani guri kina damuna ina ayki me muhimanci kin katse ni ."

"wani haushi taji ta mike a fusace "

"and yes koda wata ran ne kika gan ni dan Allah ki daina kula ni saboda ni MAKYN AHMAD mutum ne me aji da  san mutunci idan ana gani na da irin ku ae girmana zubewa ze na yi dan Allah a kula."

"takaici ya kamata ta ji kuka ya kwace mata."

"shi ko ko a jikin sa aykn sa ya cigaba na ce oh MAKYN manya likafa ta cigaba an karo wulakanci."

❣❣❣❣❣❣

"a daren ne umar ya kira matar sa vidio call ya sa ta kira khusam da kayyum suka zauna. nan ya fada musu abunda ake ciki."

"tashin hankali kenan dan khusam suma ne kawai be ba da yaji wai rabi kanwar sa ce wadda take bin sa a haihuwa uban su daya. innalillahi wa'ina illahir raju'un  ya dinga fada yana hawaye."

"mummy ko masifa ta fara yi ita an cuce ta kar ma ya fara maida auran su dan ita babu kishiya a policy dinta. daga ita se yayan ta kuma tana nan zuwa nigerian ya jirata."

to kunji wata sabuwa
muje zuwa

more comment's more typing

  SANADI NEWhere stories live. Discover now