page 31

7K 442 35
                                    

*Haske writer's Association* (home of expert and perfect writer's)

*SIRRIN MIJINA*

*Billy Galadanchi*

  Sadaukarwa ga qawata
*Nafeesatu sani kibiya....(Pheey)*

          31

Shirin tafiya gun boka sa'ade tai da kanta sabida bazata iya haqura da wannan baqin cikin ba tana kallo Hisham na zuwa gun wata banza, cen bayan bokan ya gama.jin baya nin ta yace

"To zanyi asirin daze dena san uwar ita kuma er ya kikeso ayi da ita?"

"So nake a kasheta tukunna, ita kuma uwar ya saketa ya koreta a gidan gaba daya" qawartace data rakota ta kalleta jinta ambaci kisa

"Sa'ade mesa zakiyi kisa kuma?" Harara ta wurga mata

"Gado gadon hisham zesanya nayi kisa, shi d'inma yara biyu kurin zan haifa in kashe uwarsa sannan in kashesa muci gado" mamakin furucinta ya sanya zulaiha ta kalleta

"Dan Allah karki soma kisa plss zunubin ze miki yawa" duka ta d'aka mata "Ba ruwanki banza kawai" tsawa bokan ya  daka musu

"Ku tsaya akan aiki d'aya idan kuma shawara kukeyi ku tashi ku bani wuri" jiki na rawa tace

"Boka a taimaka akasheta kanna qarasa gida sakin kuma ko zuwa nanda kwana biyar ne kar ana zaman makoki ai  zargin wani abu" kwashew ayae da dariya ya dakko wani garin magani yace

"Ki bad'awa 'yar a abinci taci.....mijin kuma ranar dakikeso ayi sakin ki kalleshi kice dashi agabanta

" ka saki zuhrah!"  Zakiga ya saketa har saki uku" godiya ta dinga zabgawa suka miqe ita da zulaiha  suka wuce gari....kaintsaye zulaiha gun Shamsiyya ta wuce dama qawartace tare suka taso tun suna yara halin zulaiha ke damunta na mugun kwad'ayin abun duniya shisa sukayi baran baran da ita......riqe baki tayi alokacin tana part d'in pheey tana tayata girki kasancewar girkin tane saleem ya rako baquwar suka rungume junaa tace

"Zaliha kina duniyar nan, rabon dana ganki tunkan mubar tsohon gidan cen tukunna ma wai waya kwatantamiki nan gidan" janye jikinta tayi daga nata tace

"Kedai dabaki gayan zakubar cen gidanba seki isheni da uwar tambaya ba ruwanki da wannan tunda gashi nazo" zama sukai anan parlor din pheey ta kalleta

"Hajja shamsiyya saleem yace kina part d'in amaryar daddynsu nace tab kaji en aljanna" harararta tayi

"Kuma en aljanna ne inshaa Allah ya kwana biyu?"

"Qalau yau na tunaki ne kuma dai inada wata damuwa ne wlhy nayi wani abu ne babba kuma yaxo yamun tsaye a rai" mamakin furucinta tae

"Tabb zaliha yauda kanki kike maganar kin aikata abu ya miki tsaye arai to meye shi" kallon qofar da shamsiyyah ta fito tai

"Muje gidanki ba kishiyraki tana nan ba" hannunta taja suka miqe batare dasun nemi Nafeesah ba suka wuce part din shamsiyyah.... Basu jima da fitaba pheey ta fito tayi mamakin rashin ganin Shamsiyya wannan ya sanya tabi bayanta.....

"Ki bari kaiwa shamsy wata qawata na raka gun boka yau, sa'ade sunanta ai kin santa wacce kike cewa in rabu da ita tuni?" Gyada mata kai shamsy tae alamar ta gane tace

"Yauwa ita to, in gaya miki wai kishiyarta zuhra take so mijinsu ya saka,  kuma bama sakin ya furgitani ba wannan ai is normal abinda yafi bani mamaki da sa'ade shine wai tace da bokan ya kashe ersu qwaya d'aya tal!!! Ni tun acen naso in hanata taqi ta yarda se inaga kamar idan akayi kisan nima dani akayi tunda nice er rakiya Allah ya gani bazan iya qura ido a kashe er mutane ba wai da sunan zataci gado, har tana cewa idan ta kashe ershi seta sanya ya saki matar sa sannan ta kashe uwarsa shima ta kashe sa ta mallake dukiya" dafe qirji shamsiyya tayi jin wannan labarin ta wara ido

SIRRIN MIJINAWhere stories live. Discover now