page 12

6.9K 445 17
                                    

*Haske writer's Association* (home of expert and perfect writer's)

*SIRRIN MIJINA*

*Billy Galadanchi*

  Sadaukarwa ga qawata
*Nafeesatu sani kibiya....(Pheey)*

                         12

Nafeesah zaune ta rafka uban tagumi yau saura mata watanni biyu da kwana hud'u ta gama wanka abin duniya dukya dameta ta barwa Allah zancen mutuwar mijinta har wannan lokacin babu wani abu daya sauya daga huld'arta dasu zuhrah  a gidan mijinta take zaman takabar ta.......Ta kula zuhra sosai takejin kunyar ta domin kuwa duk yanda taso ta saki jikinta su dawo kamar komai be faru ba amma abin yaci tura sam taqi ta sake da ita...yau zaune suke a parlor gidan pheey kowa yayi shiru da abinda zuciyar sa ke saqa masa  itadai zuhrah batason zuwa gidan sabida sam ta kasa sakewa da abinda ta aikata wa mijin pheey yayinda Nafeesah ke tunanin rayuwar dazata shiga agaba kasancewar ta bame farin jini ba tun asali tayaya zata samu wani mijin yanzu?? Zuhra ce ta katse shirun dacewa

"Nafeesah kinama cin abinci kuwa ninaga duk kin rame?" Murmushi ta sakar mata tace

Inaci mana dandai mun kwana biyu bamu had'u bane kece dai naga kinata ramewa har wani baqi kikayi, zuhrah dan Allah da manzan sa ki rufawa kanki asiri da tunanin abinda kika aikata hukuncin ki tun a wurin mahalicci shine ki zauna a duniyar nan kuma cikin nutsuwa,na kula sosai kika matsawa jin dad'in ki akan mutuwar mukhtar ni ban damu ba, tausayi d'aya yake bani daya kasancewa ya komawa mahalincinsa cikin mugun hali,ina masa fatan samun rahamar Allah wanda bazan gushe ba zanci gaba dayi masa har abadan....kema kuma wannan ne kurun abinda zakimun inji sanyi kinawa mijina adu'ar samun rahamar Allah mahalicci shine kawai" share qwalla zuhrah tai

"Nafeesah bakisan yanda nakejiba duk sanda na  kalleki nakuma tuna cewar wai ninan nice sanadin zuwan mijinki lahira, babu yanda za'ayi na sake kai tsaye koba da keba ni kaina banida aiki se istigfari sabida nasan cewar koba komai da laifi na, ina roqon Allah yamasa gafara nima kuma ya yafemun" shiru ne yabiyo baya na wani lokaci kan daga bisani sukayi haramar sallah

*Bayan pheey tagama wankan takaba*

     Tsaf ta shirya  cikin shiga irin na likitoci madubi fari ta d'auka ta sanya wa idanta sannan tayi amfani da motar da mukhrar ne yake amfani da ita kanya rasu tafita zuwa asibitin, kai tsaye wurin daya dace ta nufa gyenae ward dama tana b'angaren en Fame c ne wanda Hisham ne ogan team d'in, zuwa tayi har office d'insa ta shiga da sallamar ta

"Good morn sir" shine abinda ta furta tana me kawar  da kanta daga b'arin duban shi sabida kallo d'aya ta masa ta gano abubuwan datakeji game dashi sunma ninka nada can, gyara zaman madubin idanshi yayi sannan yace

"Good morn Nafeesah ya haquri kuma?"

"Angode Allah" shine abinda ta furta a wahalce kazancewar duk motsawar dabakin sa zeyi yana tafiyane da bugawar numfashin ta

"Zamuje ward round munma yi late so muje" ya fad'a yana miqewa batare daya kalle taba,Hisham wani irin takaicin Nafeesa yakeji dashi kanshi besan dalili ba, Gabanshi ta shiga yabi bayanta ta madubinshi yake qarewa surarta kallo gadai mace har mace amma sam batada kyau fuska kullum sekace b'arnan mota ya fad'a a zuciyar sa.....Kallon patient d'insu yayi yace da Nafeesah

"Ta samu treating abortion ne, student su duba sabida tasha magungunan ta idan har bakin mahaifar ya rufe kema kuma ki duba da kyau ki gani" bakinshi take kallo duk yayinda ya motsa bakin nisawa tayi sannan ta kalli matar tace
"Se munje labour room, so immediatly after the ward round zamuje da ita" had'a baki sukayi wurin cewa

"Yes ma" Haka suka gama ward round d'in wurin k'arfe d'aya ma ta gota sannan suka juya zuwa office d'in hisham ita dashi, bata jira ya mata tayin binshi ba haka kawai ta tsinci kanta dabin bayanshi, zama yayi itama ta zauna a kujerar baqi ta kishingid'a tana mayarda numfarfashi a hankali alamun gajiya, fridge ya bud'e ya d'akko mata lemun gwangwani na malt ya zo ya miqa mata, tashi tae da kyau tana yamutsa fuska tace

SIRRIN MIJINAWhere stories live. Discover now