page 11

6.9K 467 20
                                    

*Haske writer's Association* (home of expert and perfect writer's)

*SIRRIN MIJINA*

*Billy Galadanchi*

  Sadaukarwa ga qawata
*Nafeesatu sani kibiya....(Pheey)*

                                 11
D'aukacin mutanen dake zaune cikin court hall d'in tsit suke baka jiyo qarar komai se bugawar zuciyoyin wasu yayinda saukar numfashin wasu ke dira a hankali acikin hall, qarar fanka da kuma na'urar sanyaya d'aki ne kurin ne suka rinjayi qarar bugawar zuciyar Hisham tabbas ko Zuhra dake tsaye acikin dog cage s'in bata gaishi shiga firgici da tashin hankali ba.....ya kaiwa zuhrah ziyara ta gama sanar masa ita tayi kisan a tsorace yake kar shedun dazasu gabatar ya gagara ceto ran abar sonsa sam baya hango tasa rayuwar idan ba zuhrah yana roqon Allah ya aiko musu agajin gaggawa ya sani babu wani wanda ze iya kub'utar da zuhrah idan Allah ba.....tunda aka kawota cikin cage d'in kanta ke qasa qamshin turaren Hisham ne ya sanya ta d'ago kanta a hankali ta soma wara idanu domin nemanshi karaf idansu suka had'u dana juna murmushin qarfin hali ya sakar mata yayinda ita kuwa tana ganin shi tasoma zubar da qwallah tasani kashe ta zasuyi wataqil yau da angama zaman sharia arnan tata ta gama qarewa a hankaki hisham ya had'e hannayenshi guda biyu yana girgiza mata alamar dan Allah ta dena kuka, d'auke kanta tai daga dubanshi zuwa wani b'angaren taso ace ya fahimci zuciyarta ce ke zubar da wannan hawayen bada sanin idanta ba sam yaya tsayarda zuciyarta?... Ana haka aka soma shari'a Brr. Auwal ne ya nemi izinin shigowar mubarak inda ya shigo zuwa d'ayna dog cage d'in ya tsaya kallon sosai ya masa yace

"Malam Mubarak bayan kisan da akayiwa yayan ka kaine mutum na farko daka shiga cikin gidan kaga gawar yayan naka shin a tare da wa ka sameshi a wannan lokacin?" Kallon shi mubarak yayi yaji haushin tambayar kamar ya a tare dawa? Yanzu fa yagama fad'ar shine mutum na farko dayaga gawar ta mukhtar,gyaran tsayuwarsa yayi sannan yace "Shi kad'ai na sameshi" girgiza kanshi yayi yace

"Wace alama ce ta tabbatar maka cewar zuhra ce tayi kisan" Brr. Asma'u ce ta miqe tsaye "Objection my lord, Brr. Akowane lokaci yana karkata akalar tambayoyinsa ne inda yakeso aje, kacokam yake daurawa wacce ake zargi laifin kisan yafa kamata ya gane zargi akeyi bawai an tabbatar bane" karamar hama katako me shari'a ya buga asaman teburinsa ya "Akiyaye Brr." Zuwa Brr Auwal yayi ya zauna yayinda Asma'u ta taso ta tsaya wurin Mubark ta kalleshi sosai tace

"Mubarak a bayanan damukaji kaine mutum na farko dakaje kayi karo da gawar mukhtar har cikin gidanshi mezakace game da wannan, shin ya akayi kasan gawan na ktchn ka duba ko inane baka ganshi ba? Ko kasaba shiga ko inane a gidan?" Gyaran tsayuwarshi yayi

"Ban taba wuce parlor gidan ba tun bayan da aka akai masa matarsa sabida baya so, baya barin nake shiga hasalima ko parlor d'in seda izininsa idan yana gidan"

"In hakane meya kaika har ktchn ranar tunda kaga gawa bata magana bare muce wai itace tabaka izinin shiga gidan gashi kai kuma kace gawarsa ka tarar bashi d'inba" yasha jin labarin lauya Asma'u jega akwaita da ilmi ga kuma saurin gane me laifi ya soma tsorata da tambayoyinta dukda yake yasha ji ance bata bin bayan qarya ko kad'an

"Nafeesah matarsa ce ta sanar dani labarin yana gida dama yace na karb'o masa waankinsa ban samu kai masa se washekari yazo ya kawo su gidan amma bamu had'uba nasan halinshi da shegen fad'a ya sanya nayi qoqarin kiranshi domin naji in yana gidan be daga ba,haka matarshi ma ta karbi wayana akan ta kirashi amma sam bata samun shi sabida baya d'agawa itace ta tabbatar mun yana gida ya sanar mata bacci zeyi wannan ya sanya naje gidan azuwan idan nai knocking ze bud'e mun dad'e muna hira da wasanni da Habu me gadi kasancewar mun saba hakan dashi ni kuma naita kiranshi har alokacin be d'aga ba, munjiyo qara sosai nida habu ta mace da ihun ta  kafin mu jiyo ihun namiji me razanarwa wanda shine ma yaja hankali na nayi tattaki zuwa bakin qofar batare dana shiga ba dukkuwa dayake munyi zaton qarar badaga gidan bane anan na tsaya ina kwankwasa wa se zuhrah na gani da gudun fanfalaqi ta fito daga gidan bako zani ajikinta se under skirt na mata bakuma d'ankwali akan ta se rigarta dana kula ta yage gaba da baya sororo nayi ina kallonta naga motar gidan Dr. Hisham a cikin gidan amma nazata shine a gidan kuma ban tambayi me gadi ko waye ba kamar shima be sanar dani kowaye ba....ban samu damar cewa komai ba naga ta juya ciki se kuma can ta dawo ta dauro zaninta amma dankwalinta da mayafinta da jaka duk a hannu suke kana ganin kasan bata cikin nutsuwa sam, na kalleta sosai nace "Lapia dai Aunt zuhra?" Bata tsaya b'ata lokaci ba tace

SIRRIN MIJINAWhere stories live. Discover now